Kurarin ’yan Neja-Dalta bai razana ’yan Arewa ba – Shugabannin al’umma
Barazana da kurarrin da ’yan yankin Neja-Dalta suka yi, cewar matukar Shugaban kasa Goodluck Jonathan bai ci zabe ba za su tayar da rikici, kuma ma har sun umarci ’yan asalin Kudancin Najeriya mazauna Arewa da su tattara komatsen su, su dawo gida lamarin da ya haifar da tsoro da kuma wasuwasi makomar kowace kabila […]
Barazana da kurarrin da ’yan yankin Neja-Dalta suka yi, cewar matukar Shugaban kasa Goodluck Jonathan bai ci zabe ba za su tayar da rikici, kuma ma har sun umarci ’yan asalin Kudancin Najeriya mazauna Arewa da su tattara komatsen su, su dawo gida lamarin da ya haifar da tsoro da kuma wasuwasi makomar kowace kabila da ke zaune a Kudu dama ’yan kudu mazauna arewa raotanni daga jihohin Akwa Ibom da Bayelsa da kuma ribas harma da kuros riba kowace rana ana samun ,yan arewa mazauna jihohin na koma wa jihohin su an asali.wakilinmu a kalaba musa kutama ya tattauna mana da wasu da suke tafiya arewa da kuma wadanda suka yanke shawarar tsayaw ahar sai abunda hali yayi .
Aminu Lawal Wanzan ya shaida wa Aminiya dalilansa na kin barin Kalaba ya koma gida sakamakon tsoro da zullumin yadda za ta kasance cewa, “ Eh! To gaskiya mutane na ta kacaniyar tafiya sosai, amma ni ba zan tafi ba, saboda lokacin tafiyata bai yi ba, wata barazana ko rigimar zabe ba za ta sanya ni in tsorata in tafi ba. Sai Allah yayi.”
Ya ce barazanar da ’yan yankin Neja-Dalta suka yi na tayar da wata kayar baya idan nasu bai ci zabe ba, wannan ai an dade ana ruwa kasa na tsotsewa, babu wani tasiri da maganar su za ta yi, wadanda suka tafi Allah ya sauke su lafiya. Mu kuma da muka rage Allah ya kare mu. “Barazanar ba za ta kamayar masa da gaba ba. Saboda a cewarsa, “Allah ne mai yin komai.”
Alhaji Muammad Rani. Shi ma da yake tofa albarkacin bakinsa, cewa, ya yi shi kam bai ma fara tunanin zuwa ko’ina ba, ba inda za shi.
“Tawakalli ga Allah na yi yasa ba za ni ko’ina ba, amma nasan ko na bar Kalaba na tafi gida ai nan ma duk dai Najeriya ce, na bar Najeriya na sake koma wa Najeriya, ai irin wannan ta sha faruwa. Wadanda suka yi gudun hira, suna dawowa su iske mu. Allah ya kare mu, babu wani abu da ya faru garemu. Tafiyar ba wani amfani take da shi ba; babu wani abu da zai faru sai alheri in Allah ya yarda. In ma dai na tafi nasan gidan mu, amma dai ai duk Najeriya ce,” inji shi.
Maganar cewa ’yan Kudu su dawo gida idan shugaban kasa ya fadi zabe za su yi fada duk farfaganda ce irin ta su.
“Wane irin furuci ne ba su yi ba, karshe su dawo su raina kan su, kamar yadda ta kasance a shekarar2011. Mene ne ba su fada ba, bai yi tasiri ba. Wannan ma haka zai kare insha Allahu. Babu wata rigima da za a yi ’yan Najeriya sun gane gaskiya, sun daina bari ’yan siyasa na rudin su a yi fadan siyasa. In Allah ya yarda za a yi zabe lafiya, a gama shi lafiya. Wanda ya ci zabe za a ba shi,” inji8 shi.
Shi kuwa malam Abubakar, wani mazaunin Akamkpa, wani gari da ke Jihar Kuros riba da wakilin mu ya isake shi a tashar mota da ke layin Bagobiri, unguwar Hausawa, ya shaida wa wannnan jarida cewa shi “kowace shekara ina zuwa watan Janairu ina shiga mota a nan in tafi gida ba gudun zabe zan yi ba.”
Akasarin wadanda aka tattauna da su sun rika nokewa, suna nuna ba gudun zabe suke yi ba, a’a rajistar su ta katin zabe da suka yi a Arewa suka yi ta, shi ya sanya. Sai dai Malam Abubakar ya bayyana fargabar da wasu suke da ita ce take sanyawa suke tafiya gida.
“Fargabar da wasu ke da ita ce, suke ganin kamar za a kawo yamutsin zabe, wanda suke tsoro hakan ba ya haifar da alheri. Shi yasa gara mutum ya koma gida kusa da iyali, ya fi yi masa kamar yadda ni ma zan matsa kusa da nawa iyalin,” a cewarsa.
A wata sabuwar, al’ummar jamhuriyar Nijar mazauna Kudanci, musamman mazauna Jihar Kuros riba wasu daga cikinsu sun fara kaurace wa yankin, domin tsoron duk wata larura ta rikicin zabe idan ta taso, kar a zarge su, ko kuma huce haushi a kansu, ba tare da an bambance tsakanin bako da dan ketare ba.
Alhaji Nasiru Ishaka, shi ne shugaban kungiyar al’ummar jamhuriyar Nijar mazauna Kuros riba, ya bayyana wa Aminiya matsayin su dangane da haka, inda ya ce su ma kan su ’yan Nijar mazauna Kuros riba, wasu sun dauki matakin tafiya gida, kamar yadda suka ga ’yan uwansu ’yan Najeriya ’yan Arewa suna yi, amma ni na sha fada musu, cewa, idan mutum ya dangana insha Allahu babu wani abin da zai faru, tunda zaben nan bai shafe mu ba; ba mu da damar yinsa, ko kallo ma mu je ba namu ba ne, amma na fada musu wanda yake son tafiya ya tafi, wanda kuma zai hakura ya yi zamansa babu wani abin da zai faru, kamar yadda muke samu labara daga hukuma a Najeriya, cewa wannan zabe ba za a yi tashin hankali ba, tunda ’yan takarar mukaman shugaban kasa suka ratttaba hannu.”.
“Yadda muka ji kowane daya daga cikin manyan ’yan takara suka sanya hannu za su ja wa magoya bayan su kunne, babu tashin hankali ya sanya mana kwarin gwiwa ba za a yi tashin hankali ba, wanda Allah duk ya zaba shi ke nan,” inji shi.
Can kuwa a Jihar Bayelsa, shugaban kungiyar ’yan Arewa mazauna jihar, Alhaji Dahiru Ya’u KT, ya shaida wa Aminiya cewa “hakika ’yan Arewa suna tafiya gida, amma fa masu rajistar katin zabe na dindindin ne ke tafiya, domin kashi biyu cikin goma na ’yan Arewa ne suka tafi, saura kashi takwas kuma na nan ba su je ko ina ba.
Ya ce babu wani wuri da duk wani dan Arewa da zai yi tinkaho da shi face Najeriya.
”Ai mu ba mutanen kasar waje ba ne, duk inda muke ai Najeriya ce don haka babu wata hujja da za a ce mun bar Kudu don mu gudu,” inji shi.
Da yake yin tsokaci game da furucin tsagerun yankin na idan Shugaba Jonathan ya fadi zabe za su tayar da rikici ana shugaban ’yan Arewa ya ce zargi ne, marar tushe kuma ai ba su isa ba in Allah ya yarda babu wani abu da zai faru face alheri.