kuri’arka ’Yancinka: Muhimmancin kuri’a ga ’yan kasa
Yau saura mako biyu kacal a gudanar da zabubbukan Shugaban kasa da na ’yan majalisun tarayya. Ganin irin yadda kuri’a ke da muhimmanci wajen kawo canji ga al’umma, MALAMA A’ISHA USMAN LIMAN (09093467171) ta dauki alkamainta, inda ta zayyano wasu daga cikin muhimmancin da ke tattare da kuri’a. Ga abin da take cewa: kuri’a takan […]
Yau saura mako biyu kacal a gudanar da zabubbukan Shugaban kasa da na ’yan majalisun tarayya. Ganin irin yadda kuri’a ke da muhimmanci wajen kawo canji ga al’umma, MALAMA A’ISHA USMAN LIMAN (09093467171) ta dauki alkamainta, inda ta zayyano wasu daga cikin muhimmancin da ke tattare da kuri’a. Ga abin da take cewa:
kuri’a takan zama ’yanci ga dan kasa me hankali da natsuwa da nura da sanin ya kamata.
An kirkiro kuri’ar zabe ne don bai wa ’yan kasa damar amfani da ita a wurin zaben shuwagabanni na siyasa, wadanda mutane suke ganin su suka cancanta su shugabance su a kasa. Ba ka da wata dama ko karfi na dauko wani ka nada shi a shugabanci ga kanka koma jama’arka, sai dai ta hanyar amfani da kuri’arka a zabe.
kuri’arka ita ce ra’ayinka, tunaninka, karfinka, makaminka, da za ka iya amfani ita don ganin ka samu shugaban da kake fatan ganin ya jagorance ka a lokacin zabe. Dukkan amfani da wani abun da ba kuri’a ba to karya dokar kasa ce.
Sai dai wani abun mamaki, duk da sanin mahimmancin katin zabe da muka yi, a lokutan kakar zabe sai ka samu wasu daga cikin ’yan kasa suna cefanar da katin zabensu ga masu neman su saya, don su yi magudin zabe da shi. Abin haushin ma shi ne, da ’yan kudi kalilan ake sayen kuri’ar ta su, kai koma da kudi masu yawa ne aka sayi katin zabenka, an cuce ka, an maida kai baya, ka zama wulakantacce abin tausayi. Kaicon wanda bai san mutunci da kima da kishi da ’yancin kansa ba. Tir da dan kasar da ba ya tunani da makomarsa da makomar kananansa da ba su da madogara sai daga wurinsa.
Shin ina tunaninka da kake da shi na zaben sugaban da kake tunanin zai kawo maka rayuwa mai inganci? Ina tunaninka na ganin sai ka yi amfani da kuri’arka ka canza shuwagabannin da ke cin amanar kasarka? To yanzu ke nan ka yarda da cewar karfi da ’yancin da kake da shi a cikin kati zabenka, ka sayar da shi ga banza? Ga banza mana, tunda an saye shi ne don a yi amfani da shi a sake maida kai cikin kangin bauta. An saye shi ne don a hana ka zaman lafiya a rayuwarka. An saye shi ne don a kashe makomarka da makomar zuri’arka.
Na san wani daga cikin mu zai ce kai a da ne ake yin haka, yanzu kam kan mage ya waye, an riga an karu, an sha mu mun warke, ba zai yiwu wani ya sayar da katin zabensa ba a bana, tunda kowa ya dandana kudarsa, kuma ya ga illar yin hakan. To ku sani a yanzu haka ana ta samun labarai masu tushe, cewar akwai jam’iyar da ta fitar da kudade masu dimbin yawa don a zagaya a saye mata katunan zaben jama’a, don ta samu damar dangwale su a takardun bogi da ta buga, don dai kawai ta samu damar yin magudin zabe.
Amma ko ka sani, wannan kudin da ka sayar da kuri’arka aka ba ka su ba za su iya yi maka maganin bakin talaucin da aka riga aka kakaba maka ba? Kuma ka sani, wannan kudin rance ne aka ba ka, domin suna kafa gwamnati za su kwashe kudinku na kasa da ya kamata su inganta rayuwarku, su boye a kasashen waje, daga su sai ’ya’yansu. Ranar za mu gane illar sayar da katin zabenmu, domin za mu ankara ba mu da tsuntsu ba mu da tarko, ba mu da katin zabenmu, ba mu da shuwagabannin kirki. Daga ranar za mu gane illar rashin jajircewarmu wurin ganin an yi sahihin zabe mai inganci.
Wai ma to ina hankali da tunaninmu yakan je ne da ba mu iya gane cewar dukkan wanda ya ce zai sayi katin zabenmu to azzalumi ne? E, azzalumi mana, tunda in dai mai adalci ne da niyyar yi mana gaskiya da rike mana amanar arzikin kasarmu, ai da kawai tallata mana kansa ko jam’iyarsa zai yi da kyawawan manufofinsa a kanmu, har sai mun ji mun aminta da shi mun zabe shi, amma dubarar sayen katunan zabenmu ai kamar wata hanya ce cikin wayau ta tilasta mana mu zabi wanda ya sayi katin namu, alhalin manufarsa a kanmu yaudara, tunaninsa a kanmu ha’inci.
Shin wai me ke sa wasunmu ke sayar da katin zabensu? Tambayar da idan ka yi wa wasu da suka sayar da kuri’arsu ke nan, sai ka ji sun ce ina amfanin katin tunda ko an yi zaben ba za a ba mu wanda muka zaba ba, ai gara kawai idan sun zo nema da kudi mu karbi kudin mu ba su katin; ko ba komi ai dai mun karu da kudin nasu. To ku sani, wannan tunanin naku tunani ne na wanda bai san me ye ’yancin kansa ba. Kana da ’yancin ka kada kuri’aka ga wanda kake so, ka zabe shi koda za a yi maka magudin zabe, ya fi maka kwanciyar hakali. Ka san komi aka yi wa zalunci ne ba hakkinka ba ne, a kan ka sayar da katinka ka dawo kana da na sani, domin kullum aka ha’ince ka sai ka yi tunanin akwai hannuka a cikin hakan. Shi ko mai sayen kur’arka kullum tunaninsa shi ne, ba ka da hakki a kansa, tunda kudinsa ya sa ya sayi ’yancinka kuma da yardar ka ka sayar masa.
Wasu ko idan an tanbaye su, sai ka ji sun ce wa zai iya wannan wahalar layin jefa kuri’a? To mu kuma tambayarmu a nan ita ce, da wahalar yini daya, da wahalar shekaru hudu wacce kuka zaba? Ba gara ka jajirce a cikin yini daya ba don ka ji dadi na shekaru hudu ba? Tunda idan ka jefa kuri’arka, ka kasa, ka tsare, ka raka, ka jira duk a cikin yini daya, zai iya sama maka ingantacciyar rayuwa mai alfanu ta shekaru hudu.
Wasu ko idan ka tambaye su, sai ka ji sun ce ni ba ruwana da jefa kuri’a, Allah Ya ba mai rabo sa’a. Ka manta Allah ma Ya ce tashi in taimake ka? Ai cikin niyyarka da jajircewarka ne Allah zai taimake ka, Ya taya ka zaben shugaba nakwarai mai adalci. To idan ba ka yi zabe ba fa, da wa za ka yi kuka idan ka ga rashin cancanta? Sai dai ka yi kuka da abin da matattar zuciyarka ta janyo maka.
Haka dai za ka yi ta cin karo da hujjojin wasu ’yan kasa wadanda ba su dauki zabe da wani muhimmanci ba amma ni dai ina ganin kamar laifin hukuma ne, shuwagabanni da sauran al’ummar kasa, a ce shekara 15 da kafuwar dawwamammar demokuradiyya a kasar nan, banda ma wadanda aka yi ta gwadawa can baya suna rushewa, amma a ce da yawan al’ummar kasa ba su yi wayewar da suka san muhinmancin zabe da katin zabensu ba, musamma ma yankin Arewacin kasar nan? Gaskiya ya kamata shuwagabanni da malamai da wayayyun cikin al’umma, mu tashi tsaye haikan mu fadakar, mu wayar, mu ankarar da al’ummarmu muhimmancin zabe da katin zabe. Mu fitar da ’yan uwanmu daga cikin duhun jahilcin rashin sanin alfanun zabe da katin zabe da suke cikinsa, kodayake wasu ’yan siyasar sukan amfana da jahilcin, amma mu kam talakawa da sauran ’yan kasa cutar da mu yake yi, musamman shi wanda ya sayar da nasa katin. Mu yi kokari mu taimaki kasarmu, mu ceto ta da katunan zabenmu. Ya Allah Ka taimake mu, Ka ba mu sa’a, amin.