kuri’un Buhari a Kudu sai sun ninka na Arewa-Chinyere Ikechukwu.

Wata ‘yar kasuwa mai suna Chinyere Ikechukwu da ke sayar da atamfa a garin Asaba, hedikwatar Jihar Delta, kuma ‘yar siyasa mai goyon bayan dan takarar Shugabancin kasa a karkashin Jam’iyyar APC mai girma Janaral Muhammadu Buhari, ta bayyana cewa lallai abin da ta gani ya tabbatar mata gwaninta zai samu gagarumin rinjayi na yawan […]

kuri’un Buhari a Kudu sai sun ninka na Arewa-Chinyere Ikechukwu.
kuri’un Buhari a Kudu sai sun ninka na Arewa-Chinyere Ikechukwu.

Wata ‘yar kasuwa mai suna Chinyere Ikechukwu da ke sayar da atamfa a garin Asaba, hedikwatar Jihar Delta, kuma ‘yar siyasa mai goyon bayan dan takarar Shugabancin kasa a karkashin Jam’iyyar APC mai girma Janaral Muhammadu Buhari, ta bayyana cewa lallai abin da ta gani ya tabbatar mata gwaninta zai samu gagarumin rinjayi na yawan kuri’u da ‘yan Kudancin kasar nan za su kada a zaben shugaban kasa mai zuwa.

Misis Chinye Ikechukwu ta yi furucin hakan ne a wata hira da wakilin Aminya ya yi da ita, inda take cewa: ‘’Ni na tabbatar a jihohinmu na Kudu ba ni da wani taraddudi akan Janar Muhammadu Buhari zai lashe zaben Shugaban kasa da ake shirin gudanarwa a kasar nan. Don haka jihohinmu na Kudu a nan ne zai fi samun kuri’a mafi rinjaye, wanda zai ninka na yankin Arewa gaba daya. Dalilina shi ne ina ganin alamar wasu daga cikin manyan Arewa har kawo yanzu ba sa goyon bayan Janar Muammadu Buhari a cikin zuciya, amma mu ‘yan Kudu da gaske muke yi, muna son shi, kuma muna ba shi goyon baya na gaskiya babu wata munakisa aciki.”
‘’Mu har kullum mai gyara mana kasarmu muke bukata, kuma wanda zai iya tabbatar mana da tsaro ya yaki cin hanci da rashawa; ya farfado da tattalin arzikin kasa. Irin wannan shugaba muke so, kuma muke bukata babu batun kabilanci ko maganar addini da yanki. Muna so ne kasarmu ta gyaru, ta zauna lafiya a kullum. Don haka mu al’ummar Kudu muna bakin ciki da abin da muke jin yake ci gaba da faruwa a wasu sassa na yankin Arewa na salwantar rayuka da dukiyoyin jama’a. Wannan abin takaicin ina ganin ya nuna gazawar gwamnati mai ci yanzu, wadda ta kasa shawo kan wannan rikici na ‘yan kungiyar yan Boko haram,” inji ta.
Ta yi kira ga ‘yan Arewa masu gudun suna komawa Arewa saboda wannan zabe, cewa mu mun yarda da Allah shi ke da ikon komai, don haka irin wadannan masu gudun ya kamata su gane al’ummar Kudu da Arewa uwa daya, uba daya suke. Saboda haka Najeriya ta kowane dan Najeriya ne. Don haka ina kira da su kwantar da hankalinsu, su natsu a wuri guda. Mu zabi Shugaba Mai kaunar talakawa, kuma zai Share mana hawaye da ikon Allah Mai girma a cewarta.