Kurkukun Masar kamar otal-otal ne – Janar Osman

Janar Abdel Fattah Osman, Shugaban Sashin Hulda da kafafen yada labarai na Ma’aikatar Harkokin cikin gida ta Masar, ya karyata cewa kasarsa na azabtar da ’yan kurkuku, har ma ya yi ikrarin cewa, gidajn yarin kasarsa, tamkar otal-otal suke.Osman ya bayyana cewa hukumomi a Masar suna bai wa ’yan kurkuku “kyakkyawan masauki.” Gidajen yari a […]

Kurkukun Masar kamar otal-otal ne – Janar Osman
Kurkukun Masar kamar otal-otal ne – Janar Osman

Janar Abdel Fattah Osman, Shugaban Sashin Hulda da kafafen yada labarai na Ma’aikatar Harkokin cikin gida ta Masar, ya karyata cewa kasarsa na azabtar da ’yan kurkuku, har ma ya yi ikrarin cewa, gidajn yarin kasarsa, tamkar otal-otal suke.
Osman ya bayyana cewa hukumomi a Masar suna bai wa ’yan kurkuku “kyakkyawan masauki.” Gidajen yari a Masar sun zama tamkar otal-otal,” inji shi.
Gwamnatin Masar wadda ta samu goyon bayan sojojin kasar, ta karyata keta haddin fusunoni. Wannan dai makirci ne da karya, a kwatanta giajen yarin Masar da otal-otal, a cewar kungiyoyin fafutikar hakkin dan Adam.
Alkaluma sun nuna cewa akwai kimanin mutum dubu 16 da ake tsare da su, tun bayan da aka kawar da gwamantin Shugaba Muhammad Morsi. Kuma magoya bayan Mursi ake ta kamawa, ana daurewa.