Kurona: Kasashen G-7 sun yi taron gaggawa

Kasashe bakwai masu karfin tattalin arziki sun yi wani taron gaggawa sakamakon barazanar da tattalin arzikin duniya ke fuskanta daga annobar cutar Kurona  (Cobid19) ke ci gaba da bazuwa a sassan duniya. Hakan na zuwa yayin da aka samu bullar cutar a kasar Ukraine da ke Gabashin Turai, sannan gwamnatin Faransa ta bayar da umarnin […]

Kurona: Kasashen G-7 sun yi taron gaggawa

Masu feshin maganin yaqi da cutar Kurona (Covid-19)

Kasashe bakwai masu karfin tattalin arziki sun yi wani taron gaggawa sakamakon barazanar da tattalin arzikin duniya ke fuskanta daga annobar cutar Kurona  (Cobid19) ke ci gaba da bazuwa a sassan duniya.

Hakan na zuwa yayin da aka samu bullar cutar a kasar Ukraine da ke Gabashin Turai, sannan gwamnatin Faransa ta bayar da umarnin rufe makarantu 220 bisa fargabar da ake ciki, na ci gaba da yaduwar cutar.

A kasar Iran, wani babban jami’i a Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ne ya kamu da cutar mai kama numfashi, inda ya zama babban jami’i na uku da cutar ta kama a kasar baya ga Mataimakin Ministan Lafiya da Mataimkiyar Shugaban Kasar.

Jagoran addini, Ayatollah Ali Khamenei ya nemi taimakon Rundunar Sojin Kasar, don yakar cutar da ta riga ta hallaka mutum 29 a Iran.

A ranar Talata, ministocin kasashen duniya bakwai masu karfin tattalin arziki sun yi wani zama na musamman inda suka tattauna batun Cutar Kurona,  kan yadda take barazana ga tattalin arzikin duniya.

Ta rubanya sau tara a duniya –WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ta ce yanayin da kwayar cutar Kurona ke yaduwa a duniya ya rubanya sau tara cikin sa’o’i 24, duk da cewa an samu karancin yaduwarta a kasar China, inda ta samo asali. Zuwa ranar Talata an samu karin kasashe uku a Nahiyar Afirka da cutar ta bulla.

Sababbin kasashen da aka tabbatar da bullar cutar a Afirka su ne Senegal da Tunisiya da Moroko, hakan na nuna cewa a yanzu kasashe shida ne ke fama da cutar a nahiyar.

Ministan Lafiya na Senegal Diouf Sarr ya ce, wanda aka samu dauke da kwayar cutar wani Bafaranshe ne da ya dawo daga hutu a tsakiyar watan Fabrairun da ya gabata kuma tuni aka killace shi a wani asibiti da ke birnin Dakar.

A Moroko kuwa, wanda ya kamu da cutar dan asalin kasar ne da bai jima da dawowa daga kasar Italiya ba, yayin da a Tunisiya Ministan Lafiya, Abdellatif Mekki, ya ce tabbas wanda ke dauke da kwayar cutar dan kasar ne da bai dade da dawowa daga Italiya ba.

Wasu daga cikin sababbin kasashen da cutar ta bulla a tsakanin Litinin zuwa Talata sun hada da Jamhuriyar Czech da Indonesiya da Jordan da Latbia da Portugal da kuma Saudiyya.Saudiyya ta tabbatar da bullar cutar ce a karon farko a kasarta a ranar Litinin.

Kamfanin Dillancin Labaran kasar ya ambato Ma’aikatar Lafiya ta Saudiyya tana tabbatar da bullar cutar a jikin wani dan kasar da ya dawo daga Iran.

Ma’aikatar Lafiyar ta ce mutumin bai bayyana cewa daga Iran ya dawo ba, inda ya shiga kasar ta tashar jirgin ruwa. Ma’aikatar ta tabbatar da cewa wanda yake dauke da cutar an killace shi a asibiti.

A makon jiya ne Saudiyya ta dakatar da mutanen kasashen waje shiga kasar domin gudanar da aikin Umara a biranen Makka da Madina.

Wadansu da suka riga suka biya kudadensu don zuwa ibadar Umara daga Najeriya sun fada wa BBC cewa al’amarin bai yi musu dadi ba ko kadan.

Sai dai sun ce sun rungumi kaddara bisa la’akari da cewa dole ce ta sa hukumomin Saudiyya daukar wannan mataki. Miliyoyin Musulmi ne ke zuwa aikin Hajji da Umara duk shekara.

Saudiyya ta sanar da hana maniyyata aikin Umara shiga biranen Makkah da Madina, a wani matakin hana yaduwar cutar Cobid-19 mai shafar numfashi.

Za a mayar wa maniyyata aikin Umara kudadensu

Ma’aikatar Kula da Aikin Hajji da Umara ta kasar Saudiyya ta ce za ta mayar wa maniyyata aikin Umara ko ziyarar Annabi Muhammad (SAW) kudadensu.

Matakin mayar da kudaden ya zo ne bayan dakatar da aikin Umarar da hukumomin kasar suka yi na wucin-gadi.

Ma’aikatar Harkokin Wajen  Saudiyya ta kuma ce za ta hana ’yan kasashen da aka tabbatar akwai cutar ko tana barazana ga kiwon lafiyar al’umma zuwa kasarta.

Mutum sama da dubu uku cutar ta kashe bayan bullarta a Disamban bara, akasarinsu a kasar China.