Kuros Riba ta Arewa: ’Yan takarar APC sun janye wa Sanata Jarigbe
Rahotanni sun nuna cewa matakin ya biyo bayan tuntuɓa da neman goyon bayan al’ummar mazaɓarsa da Sanata Jarigbe ya gudanar, lamarin da ya sa sauran masu neman kujerar suka amince da mara masa baya.
Dukkanin masu neman tikitin takarar kujerar Sanatan Kuros Riba ta Arewa a ƙarƙashin Jam’iyyar APC sun janye tare da mara wa Sanata Jarigbe Agom Jarigbe baya shi domin ya ci gaba da neman kujerar da yake kai a yanzu a Majalisar Dattawa.
Rahotanni sun nuna cewa matakin ya biyo bayan tuntuɓa da neman goyon bayan al’ummar mazaɓarsa da Sanata Jarigbe ya gudanar, lamarin da ya sa sauran masu neman kujerar suka amince da mara masa baya.
Taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da aka gudanar a ƙaramar hukumar Bekwara, ƙarƙashin jagorancin babban basaraken yankin, Ada Bekwarra II, Honorabul Signor Omang Idiege, ya kasance ɗaya daga cikin muhimman tarukan da aka tattauna batun.
Daga cikin waɗanda suka nuna sha’awar neman kujerar Sanatan akwai Farfesa Ochugudu Ipuele, John Onyi, da Barista Cecilia Adams.
Sai dai Barista Cecilia Adams ta janye tun kafin gudanar da taron, inda ta bayyana goyon bayanta ga Sanata Jarigbe Agom.
A wani ɓangaren kuma, ɗaya daga cikin ’yan takarar da suka fafata a zaɓen fid-da-gwani na kujerar wakilcin Ogoja/Yala a Majalisar Wakilai, Honorabul Godwin Offiono, ya soki yadda aka gudanar da zaɓen fidda gwanin na APC.
Offiono ya bayyana zaɓen a matsayin “soki-burutsu”, yana zargin jam’iyyar da yin abin da ta ga dama maimakon bai wa wakilan jam’iyyar damar zaɓar wanda suke so ya wakilce su.
Ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da magoya bayansa a makarantar firamare ta St. Joseph da ke Okuku, inda ya nuna rashin gamsuwarsa da yadda aka gudanar da zaɓen fidda gwani a yankunan Ogoja da Yala.
Duk da haka, Honorabul Offiono ya buƙaci magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da nuna haƙuri da biyayya ga jam’iyyar.