kurungun Babban mutum mai rawani
Tsakanin makon da ya arce zuwa kwanakin da muke ciki, hukumar guidan waya ta kasar Haurobiya ta fara shirinta na tara Hauro tiren-taliya, inda a ke cire wa duk mai mu’amala da asusu-asusun ajiya Hauro babban lauje da zagaye, cikin kowace hada-hadar shige da ficen matsabban da aka yi a asusun ajiyar daidaikun mutane da […]
Tsakanin makon da ya arce zuwa kwanakin da muke ciki, hukumar guidan waya ta kasar Haurobiya ta fara shirinta na tara Hauro tiren-taliya, inda a ke cire wa duk mai mu’amala da asusu-asusun ajiya Hauro babban lauje da zagaye, cikin kowace hada-hadar shige da ficen matsabban da aka yi a asusun ajiyar daidaikun mutane da kamfanoni masu zaman kansu da ma ma’aikatun gwamnati. Wannan al’amari da aka ce kudin kurungun babban mutum mai rawani ne, hakika ya haifar da takaddama a tsakanin al’umma, kai har ma a teburin mai shayi.
Ni dai ba masanin tsimi da tanadi ba ne, amma ina iya fasko jirgin masu tsuwurwurta tsimi da ta’adi, ko munanan tsare-tsaren da hukumomi suka sha aiwatarwa a kasar Haurobiya, musamman tsarin nan na ga lukudi, ga lakume kudi. Ire-iren munanan tsare-tsaren tsikarin talakawa da kwashi kwaraf da dukiyar al’umma shi ya haifar wa kasar nan ‘ talalar tulin tufkar talauci a tsakanin Haurobiyawa,” ita kuwa gwamnatin kasa ta gaji FANKON LALITA. Fankon lalita da aka gadar wa Gwamnatin Baban-burin-huriyya da Usainin-Babajo, ya haifar wa kasar nan matsanancin ciwon kurungu. Hakika Mai-duka ya kawo mana dauki, tunda jam’iyya mai maganin zogi da radadin ciwon kurungu ta kama ragama, muke fatan za ta sanya tsintsiyarta mai kwakwa don share mana hawayen da ke kwarara daga namujiyar gama-garin al’ummar Haurobiya.
Sannan akwai bukatar bullo da hanyoyin cike gibin damin Hauron da za a zubo wajen awatar da aikace-aikacen raya kasa, kamar yadda yake kunshe a kundin baje-kolin Hauro na bana. Ko wata tantama babu, idan mutum na iya gano cewa, irin wadannan tsilli-tsillin matsaloli ne suka sanya Gwamnatin Haurobiya ta fara aiwatar da dokar biyan kudin kurungun babban mutum mai rawani. Ga dai manufofi da ma’anar wannan doka, bisa tsarin faskaren ma’anonin wannan katafariyar makaranta.
Dokar biyan kudin kurungun babban mutum mai rawani na Hauro babban lauje da zagaye ta shekarar dubu karamin lauje da tsayuwa bisa kafa daya, bisa doron kaidar daidaita lamuran hada-hada damin matsabbai ta shekarar dubu karamin lauje da manuniyar kasa. Kuma kotu ce ta tursasa Babban Asusun Haurobiya ya umarci asusu-asusun ajiya irin su asusu mai sunan korar kaza da giwa mai mangalar Hauro da Uba mai tarairayar dukiyar ’ya’yansa da sauran su, kan lallai su fara zare wa mutane zare daurin daman su, don kai wa hukumar gidan waya ta kasar Haurobiya.
A matsayina na Katafaren Direban Allin farfcajiyar Dodorido da ke Amintacciyar jaridar kasar Haurobiya, na fasko cewa, kamata ya yi a aiwatar da wannan doka a cibiyoyin kasuwanci da kasuwanni da tashohibn ababen hawa, ta yadda za a tantance shige da ficcen damin Hauro tun daga dubu sili zuwa malala gashin tunkiya,; ko ghashin balama; ko tiren-taliya. Yin hakan zai bai wa gwamnati samun damin ’yan tsabbai don tafiyar da harkokin hukumar gidan waya, har ma ta yi amfani da wani ba’ari na damin matsabban don cike gibin baje-kolin Hauro na bana.
Misali da za aje karamar Hukumar Munin-silifas, inda fadar Maimartaba Masanin Sisi-da-sisi take, sai a dauki hotunan bukukuwa da hawan ingarma da ake gudanarwa a kowace shekara; kai hatta fitowar mai martaba a bainar jama’a, don likawa a takardun hada-hadar Hauro.
Kuma ana iya aiwatar da irin wadannan tsare-tsare a kusan kowace jiha, matukar akwai jiga-jigsn jagorancin al’umma da muka gada iyaye da kakanni. Don haka akwai bukatar irin wannan salon zayyana ko hotuna Mai martaba Muminin Babban Mutum mai rawani na birnin Dikko; da Shehun Bararon-nono da Shehunnan masu rawunna da ke Jihar Yawon-Bebe. Uwa-uba mai alfarma Jagoran masu fuskantar alkibla don kadaita Mahalicci da ibada da ke birnin shehu Mujadaddi.
Salon zayyana da lika hotunan jiga-jigan jagorancin al’umma na iyaye da kakanni zai sanya attajirai da talakawa su amince da biyan kudin kurungun babban mutum mai rawani. Idan kuwa hukumar gidan waya ta jajirce kan lallai a asusu-asusubn ajiya za ta rika yi wa mutane suri-ka-ruga, tabbas za a wayi gari Asusun korar kaza (ass) ya koma Asusun assasa asarar Hauro; Giwa mai mangalar Hauro na iya zama mai tuntsurar da matsabbbai, Uba kuwa ya daina yi wa ’ya’yansa tari, illa kawai ya tattare komai sai shi kadai, inda ’ya’yansa za su asarar tarin su.
Batu na ingarman kwangiri, asusu-asusun ajiyar kasar nan na zarar ’yan matsabbai a duk sa’adda mutum ya zaro Hauro daga ramin ajiya; ko ya sanya cakin caccako kudi, ya cake dami; kuma idan aka cillo wa mutum bayanai ta cikin kurtun magana na halo-alalo, nan ma za a zare zare. Waki shin bisa la’akari da wadannan dimbin matsabbai da ake zarewa daga gurbin ajiya a asusun daidaikun mutane, shin ba a fasko cewa, wani ko wata na iya yanke hukuncin boye matsabbai ko damin Hauro a karkashin matashi. Abin da kawai za a iya samu shi ne, daga ladar kwadago neman kadago da ’yan kwadago ake biya wa al’umma ta asusun kasuwanci da ke fadin kasar nan.
Lallai akwai bukaytar Gwamnatin Baban-burin-huriyya da Usainin-Babajo da Hukumar Gidan-waya su aiwatar da dabarun da al’umma za su yi amanna da su. Kam,ar yadda na bijiro da wannan al’amari, kowace jiha a rika amfani da salon zayyanar hoton jiga-jigan jigon jagorancin al’umma da aka sani iyaye da kakanni. Sannan a wayar wa gama-garin al’umma fa’idar yin haka a kasar nan, musamman al’marin da ya shafi baje-kolin Hauro na bana da aka kuduri aniyyar aiwatar da ayyukan raya kasa. Idan kuwa aka ki duba wannan bukata ta al’umma, sai mu yanke cewa, ba ta sake zane ba, wato dai tsarin damo-da-kura-da-diyya irin na mai dan boto da sanda jirge ya sake bijirowa a dama-dama-da-kurda-kurdar wasan Samson-siya-siya da ke kai kawo a siyasar kasar Haurobiya.