Kurunkus! Zidane ya bar Real Madrid

Zinadine Zinade ya ajiye aiki a matsayin mai horas da Real Madrid.

Kurunkus! Zidane ya bar Real Madrid

Zinadine Zidane. (Hoto: goal.com).

Mai horas da ’yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinadine Zidane, ya ajiye aikinsa nan take.

Real Madrid da ke kasar Spain ta sanar da hakan ne a ranar Alhamis, kwanaki kadan bayan kungiyar Atletico Madrid ta lallasa ta a gasar La Liga.

“Lokaci ya yi na a mutunta shawarar da ya yanke a kuma yaba masa bisa kwarewar gami da sadaukar da kai da kishi da ya nuna a tsawon shekaru,” inji sanarwar da ta wallafa a shafinta.

Ta ce “Zidane daya ne daga cikin wadanda suka kafa wa Real Madrid tarihi a matsayin dan wasa da kuma koci.”

Zidane dan kasar Faransa ya bar kungiyar wadda ta lashe gasannin kasashen Turai sau 13 ne a karshen kakar da ba ta kai ga nasara ba.