kusa a bango

Barkanmu da warhaka Manyan gobe, tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘kusa a bango’. Labarin ya kunshi yadda bakar Magana ke zamo rami a zuciya. A sha karatu lafiya. Audu yaro ne mai rashin kunya ga manya da kuma sa’o’insa. Ga shi ba shi da lafazi […]

kusa a bango
kusa a bango

Barkanmu da warhaka Manyan gobe, tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘kusa a bango’. Labarin ya kunshi yadda bakar Magana ke zamo rami a zuciya. A sha karatu lafiya.

Audu yaro ne mai rashin kunya ga manya da kuma sa’o’insa. Ga shi ba shi da lafazi mai dadi. Wannan irin halin nasa ya sa makwabta da abokansa suka tsane sa har ya janyo sanadin da mutane ba su son yi wa iyayensa magana.
Wannan halin Audu yana bata wa iyayensa rai. Sai rannan mahaifinsa ya kira sa ya ce da shi, idan ransa ya bace ya dauki kusa daya ya buga a bango.
A ranar farko Audu ya buga kusoshi talatin, a rana ta biyu sha biyar. Haka dai kusoshin suke ta raguwa har aka samu ranar da ta wuce bai buga kusa ko daya a bango ba.
Sai ya fada wa mahaifinsa akan bai buga kusa ko daya ba a wannnan ranar. Mahaifin ya ce ya je ya  cire kowace kusa daya bayan daya da ya buga a bango. a raminsa. Audu y a dage da cire kusoshi amma abin ya ba sa wahala har ya kasa cire wasu daga bangon.
Sai mahaifin ya ce da shi mai ya gani a bangon bayan ya cire kusar. Audu ya ce rami. Sai mahaifin ya ce haka bakar maganar da kake fadawa mutane take a zuciyarsu. Don haka ka zamo mai fadan alheri ko kuma ka yi shiru domin ba wanda zai taba mantawa da wannan bakar maganar.
Tun daga wannan ranar Audu sai ya zama dan kirki.