Kusancina da Shata ta sa ana kamun kafata don ya yi waka – Musa danbirni
Alhaji Musa danbirni, daya ne daga wadanda marigayi Alhaji Mamman Shata ya yi wa waka. Ya bayyana haduwarsa da Shata kuma ya ce tsakaninsa da Shata da iyalin Shata abin ya wuce alaka ta waka, sai dai a ce mutunci da zumunci: Aminiya: Za mu so mu ji tarihin haduwarka da Shata da alakarka da […]

Alhaji Musa danbirni, daya ne daga wadanda marigayi Alhaji Mamman Shata ya yi wa waka. Ya bayyana haduwarsa da Shata kuma ya ce tsakaninsa da Shata da iyalin Shata abin ya wuce alaka ta waka, sai dai a ce mutunci da zumunci:
Aminiya: Za mu so mu ji tarihin haduwarka da Shata da alakarka da shi?
danbirni: Ni Alhaji Musa danbirni an haife ni a Unguwar Karofin Sudawa a cikin birnin Kano a gida mai lamba 48, a gidan kakana da ake kira da Umaru Makam. Yau ina da shekara 63 a duniya. Kuma tun ina da shekara bakwai zuwa takwas, nake jin wakokin mawakan Hausa na gargajiya, musamman mawakan kasar Sakkwato da Katsina da sauransu. Daga cikinsu akwai marigayi Alhaji Mamman Shata Katsina wanda Allah Ya saka mini son wakarsa. A koyaushe na ji wakarsa, sai na tsaya na ji har karshenta.
Haka kuma nake sauraron wakokin Shata da ake sakawa a shirin zabi sonka da kuma filin Shata a gidan Rediyon Tarayya na Kaduna. Akwai lokacin ma da NTA Kano suka yi ta gayyatar Shata ya je ya yi musu wakoki su nada don sakawa a cikin talabijin, amma sun dade suna bin sa, bai je ba, sai da aka sa suka neme ni. Ni kuma a lokacin yana Kwanar dangora, na je na fada masa, na hada shi da ma’aikatan NTA, ya fada musu duk bukatunsa, na kudi da inda zai zauna da duk irin abin da yake so a yi masa duk suka yi masa, sannan ya dauki mako uku a masaukin Bagauda yana waka suna dauka, har ma ya kara da wadanda ba su tambaye shi ba. Ana nan ran nan sai Shata ya zo Kano ya sauka a kofar Mata a gidan wani maroki da ba zan iya tuna sunanasa ba. A lokacin ne na yi kokari na gana da shi ya fara sanina. Daga duk lokacin da ya zo Kano yakan sauka a layin Ibedi na Sabon-Gari ko ya sauka a otel din Neja a Sabon-Gari, sai nakan je na gaishe shi kuma mu gana, daga nan har muka fara shakuwa, kuma har ya fahimci cewa ni masoyinsa ne. Duk kuwa da cewa ya girme ni sosai a shekaru, domin a lokacin ina da kamar shekara 30, duk da haka yana ba ni muhimmanci sosai. Shata ya fahimci ina kaunarsa duk da kankantata kuma yana sanin masoyinsa. Da ya lura ma ba na son zuwa otel saboda ni yaro ne a lokacin kuma ba ni da wata bukata ko harka a nan, sai yakan bar masaukinsa na otel, ya je titin Ibedi, na hadu da shi a can. Sanin masoyinsa da ya yi duk lokacin da na je wajensa yakan ba ni cikakken sauraro kuma Allah ne Ya hada jinina da shi.
Wannan ta sa na samu daukaka a wajensa don ko me yake yi idan na je zai saurare ni kuma yakan tuntube ni ko ya yi shawara da ni har mukan ci abinci tare da shi. Hatta zuwa unguwa ko wani gari ko wajen sana’arsa ta waka yakan ja ni mu je tare, kuma a gabana ya yi wakoki ba iyaka, ina zaune kusa da shi da ’yan amshinsa da makadansa. Wannan ya sa koyaushe ya zo nan Kano zai neme ni, kai har ma ya zamo duk wanda yake son ganin Shata ko Shata ya zo ya yi wasa a wajen bikinsa, sai ya neme ni, saboda alakarmu ta kai duk inda yake yana fada min. Ni kuma sai na je na kirawo shi ko a fada masa bukatar da mutane suke da ita a wajensa ta gayyata ko makamancin haka, kuma a cikin yardar Allah da na fada masa, zai amsa ya zo. Idan Shata yana son za a sayo masa wani abu ko zai je wani waje, sai ya neme ni. A wannan lokacin duka-duka ban wuce dan shekara 30 da ’yan kai ba, amma dai na samu daukaka a wajen Shata da yaransa. Kuma a lokacin ni ina tireda ne da harkar kasuwanci, a wannan kasuwanci na samu na yi aure kuma sai da Shata ya zo wajen bikin aurena. Domin an yi biki a Wapa a 1973 ko 1974 na yi auren.
Aminiya: To ko a wajen bikin naka ne ya yi maka waka, kuma ka taba nuna kana son ya yi maka waka ko kuwa shi da kansa ya yi maka?
danbirni: To ni dai ban taba fada masa cewa ya yi min waka ba, amma da yaransa suka fahimci cewa wani mutum yana yawan yi wa Shata alheri, kuma su yaran suna so a yi wa wannan mutumin waka, kuma sun fahimci wakar yake so, to sukan hada kai da ni su gaya min, ko na san mutumin ko ban san shi ba. Haka idan za a je gidan rediyo ni ake fadawa na kawo shi. Ni na kai shi gidan talabijin na CTb da gidan Rediyon Kano da NTA Kano duk ta kaina aka bi na kai shi. Don duk inda za a yi wata gayyata ni ake fadawa na kawo shi, haka ta ba ni damar ma idan za a je wani wajen wasa, yaransa kan fada min cewa na fada masa cewa wane yana ta yi musu hidima, ya kamata a yi masa waka. Ga su fa tare muke da su da shi Shata, amma ni za su gayawa saboda idan na gaya masa, to, kuwa zai dubi wannan maganar, don yana sauraron maganata.To, ni ban taba cewa ya yi min waka ba amma duk wacce ya yi a gabana idan ta yi dadi, zan fada masa cewa amma fa wakar wane ta yi dadi. Har ta kama idan zai je wasu garuruwan irin su Azare, irin su Bauchi, irin su Gombe, irin su Nijar, irin su Neja su Abuja babu inda bai sa na raka shi ba. Misali idan an gayyace shi nadin sarauta ko wani kasaitaccen biki ko daurin aure, idan dai zai ratso ta Kano, to zai sa ni a gaba sai mun tafi tare. Ni ba na waka ko amshi, duk ban iya ba, amma wannan alaka ta kauna da soyayya ta sa har a wajen kidan zan zauna ga kujerarsa, ga tawa tare da makadansa da ’yan amshi kuma koda hotonsa ake dauka a talabijin idan ka duba za ka gan ni a ciki. Kuma idan ma ya tsaya da waka zan yi zance ko hira da shi ko wani abu daban, idan an huta kuma a ci gaba da yin wakar. Idan Shata ne yake wasa, sai gari ya waye, domin yakan kwana yana yin waka iri daban-daban. Yawanci akan tanadi ranarsa ne ta musamman kuma koda mawaka nawa ne suka zo wajen wasa, akan kyale su, su yi ta wake-wakensu, sai sun gama, shi ne zai zo a karshe kuma idan ya fara aka zauna, sai gari ya waye.
Masu ba shi dukiya ma irin ta da, su daban suke domin masu bikin duk kyautar da za su baiwa wani maroki ko makadi, to shi nasa daurin ko kyautar daban take, sai ta ninka ta sauran, kamar yadda tasa wakar take daban. Domin a nan wajen ne mai shirin ya ba da mota, sai ya ji Shata ya fara, sannan ya ce “Na ba ka mota.” Mai ba da gida ya ba da gida, wanda zai ba da kujerar Makka sun bayar babu iyaka a gabana. Wadansu kuma sukan dauko kudi bandir-bandir daurin banki su rika mika masa. Wannan kyutar da ake yi wa Shata ta soyayya a tsakaninsa da iyayen gidansa, a gabana an yi ta babu iyaka.
Aminiya: daukakarsa ce ta sa idan an zo wasa, sai ya bari sai sauran mawaka sun gama tukuna ya fara tasa?
danbirni: Ai duk makadan mafiya yawa ma tarewa suke a wajensa, kuma a masaukinsa suke zuwa su zauna. Za su zo su tube takalmansu, su zo su zuba su yi gaisuwa, kowa ya samu waje ya zauna, a yi hira da su. Idan za su tafi ma ya dauko wani abu ya ba su. Kuma a yi ta labarin wasu abubuwa da mu da su, idan an gama sai ya dauko wani abu ya ba su. Idan kuwa suka gama wakokinsu, sai su ma su zauna su zama ’yan kallo, sannan Shata sai ya fara wasa, sai gari ya waye. Na ga wannan ya faru a gabana ba sau daya ba, ba sau biyu ba.
Aminiya: To a ranar bikin naka ya yi maka wakar?
danbirni: Ai da na zo da kaset din ma da na saka maka ka ji, inda yake cewa “Yau ne ake bikin danbirni,” a cikin wakar “Sarki Bakwai na Sabon Birni,” wadda ni na yi silar aka yi ta, saboda alakata da shi Bagobiri. Tana nan ana yin ta kuma za ka ji yana cewa: “Ga danbirni mai mota, ga tamu rundana nan ta zo.”
Aminiya: Amma wacce aka fi sani ita ce wacce yake cewa “Musa na gode danbirni.”
danbirni: To wannan kafin ita ma ya yi min wata, a lokacin ba na nan da ya je wajen bikin ba da sanda ga Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris. Mun je tare da ni da shi amma bayan na tashi daga wajen ne sai ya yi min wakar, da na dawo na tarar yana yi min waka. Ita amshinta shi ne “Musa yaro dan Kano; Musa yaro dan Kano.” Na mance dai amma yaransa sun ba ni ita na ji a cikin kaset. Kuma na ji dadi sosai har na yi masa raha na ce masa na ji an fara sa min dan ba, sai muka yi dariya. Daga nan an yi kimanin shekar biyar ban sake yi masa maganar waka ba, shi bai waiwaye ni ba, kuma ba mu fasa cudanya ta zuwa ko’ina ba. Mukan fita yawo garuruwa yana ta wakoki, har wata ran yakan ce min wa za a yi wa waka? Ko yaransa su tuna masa cewa ya kamata a yi wa wane waka kuma ya yi nan take. Amma ni dai ya yi min waka kimanin iri hudu.
Aminiya: A nan take yake waka ko wata rana yakan kwatanta wakar a gida da yaransa kafin ya fita wajen wasa?
danbirni: Wata ran mukan fahimci Shata yana son wakar kuma shi kansa so yake ya yi wakar. Sai mu fada masa wadanda muke so ya yi wa waka, kuma ya yi musu nan take. Ni ban taba ganin Shata ya gwada waka a wani waje ba, kafin ya yi ta. A koyaushe a nan take yake yin kowace waka. Wannan duk wanda ya san Shata ya san shi da wannan, domin baiwa ce wacce Ubangiji Ya ba shi.
Aminiya: A sanin da ka yi masa, wakokinsa za su kai nawa?
danbirni: Duk wanda ya ce maka ya san yawan wakokin Shata, ya yi karya, domin shi ma ya taba cewa bai san yawan wakokinsa ba, sannan ya ce wakokin da ya yi wadanda ba su shiga kaset ko rediyo ba, sun ninka wadanda suka shiga rediyo yawa. Ko a yanzu ina da kaset na wakokin Shata da suka kai dubu biyu.
Aminiya: Me za ka ce a karshe?
danbirni: To ni dai zan iya cewa alakata da Shata ta fi karfin ta waka. Soyayya ce da kauna daga Ubangiji kuma kaunar har ta kai ga zumunci. Domin har yanzu shekaru da dama da rasuwar Shata, muna zumunci da ’ya’yansa da iyalansa. Suna fada min matsalolinsu da duk abin da ya shafi rayuwarsu kuma ina zuwa na ji bukatunsu, na ba su shawara. Yanzu haka ma akwai daya daga ’ya’yansa mata da take babbar lauya ce a Hukumar EFCC da kuma wata jami’ar hukumar hana fasa-kwauri ce da wata jami’ar hukumar shige da fice ce. Wasu ’ya’yansa mata da yawa suna gidajen aure kuma babban dansa Magaji yana gidansu na Funtuwa yana zaune da iyalinsa, kuma ina zuwa har can na gansu. Ina kira ga masoya Shata su ci gaba da kulawa da iyalansa duk da cewa ya rasu. Allah Ya jikanSa, Ya kyauta namu zuwan, amin.