‘Kurkurar baki na dakika 30 na iya kashe kwayar COVID-19’
kuskure baki na tsawon dakika 30 na iya kare mutum daga kamuwa da cutar COVID-19.
Wani bincike ya gano cewa kurkurar baki na tsawon dakika 30 na iya kare mutum daga kamuwa da cutar COVID-19.
Masana kimiyya a Jami’ar Cardiff ta Birtaniya sun gano cewa kurkurar bakin na dauke da kusan kaso 0.07 cikin 100 na sinadarin cetylpyridinium chloride (CPC) wanda suka ce zai taka muhimmiyar rawa wajen dakile yaduwar cutar.
- Mata gajiyayyu 18,000 za su amfana da tallafin rage radadin COVID-19
- Masu yi wa kasa hidima sun kamu da COVID-19 a Kano
Binciken dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake kokarin gwaji a Asibitin Jami’ar Wales don gano ko wanke baki zai iya rage kwayoyin cutar a cikin yawun masu dauke da ita.
Ana sa ran wallafa sakamakon binciken ne zuwa farkon shekarar 2021.
Jagoran binciken a jami’ar, Farfesa David Thomas ya ce, “Ko da yake sakamakon wannan binciken abu ne mai karfafa gwiwa, hakan na nuna cewa akwai bukatar yin wasu domin tabbatarwa”.
Wani kwararre a fannin kula da lafiyar baki, Dakta Nick Claydon, ya ce ya yi amannar wanke baki, hadi da ragowar matakan kariya irinsu wanke hannu, sa takunkumi da ba da tazara, zai taimaka matuka wajen yaki da cutar.
Ya zuwa yanzu dai akwai akalla mutum miliyan 54 da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a fadin duniya, lamarin da ya tilasta sake kakaba dokar kulle don dakile yaduwarta.
Binciken ya kuma zo ne mako daya kacal bayan shahararren kamfanin harhada magunguna na kasar Amurka, Pfizer ya ce binciken da yake gudanarwa da hadin gwiwar kamfanin BioNTech na kasar Jamus ya gano maganin na da ke tasirin yakar cutar da kimanin kaso 90 cikin 100.