Kuskure daya Ke bata Sharhi – Farfesa Ibrahim Malumfashi
A bana ne shahararren malamin adabin Hausa, Farfesa Ibrahim Malumfashi, wanda masana ke wa kirari da ‘Magajin Abubakar Imam’ tare da Malam Nahuce Marafa Ibrahim suka fitar da wani kasurgumin littafi mai taken kamusun Karin Maganar Hausa. Fitar littafin ke da wuya sai kura ta fara tashi a kansa, inda wasu suka yi ta yabawa […]
A bana ne shahararren malamin adabin Hausa, Farfesa Ibrahim Malumfashi, wanda masana ke wa kirari da ‘Magajin Abubakar Imam’ tare da Malam Nahuce Marafa Ibrahim suka fitar da wani kasurgumin littafi mai taken kamusun Karin Maganar Hausa. Fitar littafin ke da wuya sai kura ta fara tashi a kansa, inda wasu suka yi ta yabawa tare da sanya albarka; a yayin da wasu kuma suka rika kushewa. Shi kuwa Sharfadeen Umar, daukar littafin ya yi ya yi masa dogon sharhi, inda ya ga beken marubutansa. Dalili ke nan Aminiya ta nemi malamin, ta yi doguwar tattaunawa da shi dangane da littafin nasu da kuma sauran bayanai da suka biyo bayan fitowarsa kasuwa. Ga yadda ganawar ta kasance:
Yau kusan makwanni hadu ke nan da ake ta buga wani sharhi da wani Sharfadeen ke yi a cikin jaridar Leadership Hausa game da sabon littafinku na kamusun Karin Maganar Hausa. Mai sharhin na cewa ai ba komi kuka yi ba sai baje kolin ashararanci da batsa, ga shi kuma kun yi shiru ba ku mayar da martani ba, me za ka ce kan wannan batu?
Mayar da martani kan kowane batu a cikin harkar nazari da sharhi da kalailaicewa a fage irin na adabi ba sabon abu ba ne, ba kuma abin kyama ba ne, domin gishiri ne na kara gyara miyar harkar karatu. Haka kuma yin nazarin ko sharhi a irin wannan fage na adabi ta amfani da shaci-fadi ko harari-garken bincike ko gutsiri-tsoma, shi ma abin da aka gada ne tun da dadewa. Ma’ana, masani ko manazarci ko mai yin sharhi ya daga guduma kan aikin adabin da bai da masaniya kai ko yadda aka yi ya samu matsuguni ko kuma saboda bisa wata manufa ta daban, ba ta ilimi ba, bai zama wata sabuwar kwalliya ba, shi ma ga wadanda suka san yadda ake kasawa da kwashewa a harkar.
Saboda haka ban yi mamaki da ganin wannan bahagon sharhi da Sharfadeen Umar ya yi, ko yake cikin yi ba na tsawon mako hudu zuwa yau, musamman sanin sa a matsayin ‘dalibin’ Ibrahim Malumfashi na tsawon shekaru. Ita dalibta a kula, tana zuwa bisa matakai daban-daban, ko dai an sha daga nonon masani ko malami ko wani ya guntso daga nonon, ya fursa wa wani ko kuma an tsinto daga karikitan bincike na masani ko malami ko kuma a sami rara-gefen dalibi, mai jin amon ilmi, amma ya tasirantu da shi daga nesa.
Idan na ce ba wan ba kanen daga cikin wadannan matakai da mai sharhin ya bi ko ya samu nutso a ciki, ban yi kuskure ba, ganin cewa sojan gona, a cikin duhun gonar yake bacewa, har shi sojan na ainihi, ya yi masa sakiyar da ba ruwa.
Sharfadeen bai san adabi ba, bai karance shi ba, bai kusanci wanda ya lizimce shi ba, bai kuma taba zama dalibi da ya sha a mama ba. Kenan da wa za a yi rawar baje kolin? Wannan shi ne dalilin kin mayar masa da martani.
To amma wadanda suka karanta sharhin za su ga cewa kamar ya fi ku gaskiya ke nan, shi ya sa kuka yi shiru har zuwa yau, ko ya ka ga wannan shi kuma?
Haka ne, amma ita gaskiya daya ce, wanda ya gan ta kuma zai gane ta. Ni da so na yi mai sharhin ya gama sai a bar shi da dalibai su karantar da shi. Domin abin da na saba fada wa dalibai shi ne, wanda bai san gari ba, to ya saurari daka, ma’ana, idan mutum bai sani ba to ya nemi sani, idan kuwa ba haka ba, barnar da sharhi ko nazarin da ya yi ko zai yi tana iya sukurkuce harkar ilimi.
Na fadi haka ne ganin cewa an bude wancan sharhi na Sharfadeen da tabbatar da rashin sanin makama dangane da abubuwan da suke bayyane a fagen nazarin adabi, wanda ya kara tabbatar da cewa lauje ne cikin nadi.
Kamar yaya lauje a cikin nadi? Ko shi ne ake cewa akwai hannun Masarautar Daura a cikin yin sharhin littafin?
Zan zo kan wannan batu domin shi ne ya fi sosa rai ta yadda wai za a yi amfani da Masarauta domin a bata wani ko wasu ko kuma aikin adabi. Amma bari mu soma da ruhin sharhin tukuna, ga abin da mai sharhin ya bude nazarinsa da shi. Ya ce, “kirkirarren adabi da adabin baka sun fara bayyana ne bayan al’ada ta kyankyashe ’ya’ya da jikoki,” ya kuma kara da cewa “zancen cewar Karin Magana, Salon Magana ko Hausa a Dunkule wani kursali ne mai cin gashin kansa a farfajiyar adabi a iya cewa almara ce ko ra’ayi riga.” Ya kuma jaddada cewa a “zahirance gaskiyar zance, karin magana tana matsayin kwalliyar harshe domin a cikin kowane irin harshe da irin nasa salon karin magana domin kuwa wata hanya ce ta isar da sakon nuni ya ishi mai hankali.” Ya kuma tabbatar da cewa wai “karin magana ta samo asali ne daga daga tsofaffin fadawan Sarakunan Maguzawa, a wasu wuraren kuwa daga bakunan ’yan bori har zuwa karnonin da suka biyo baya da ’yan daudu da mata suka bayyana a farfajiyar amfani da karin magana a matsayin dibilwar fidda wando ga kai.”
Duk wadannan bayanai, shaci-fadi ne, ba abin da zan mayar da hankali kai ba ne, domin ya nuna a sarari cewa mai sharhin bai san matsayin karin magana a Hausa ba. Zan so na bar dalibai su barje gumi, wajen mayar masa da martani, kila ta haka a bambance tsakanin duma da kabewa.
To me za ka ce kan zargin da ya yi na cewa a Hausa ba a san wani abu ‘kAMUSU’ ba sai ‘kAMUS,’ wai wannan ya nuna cewa kun tafka kuskure tun daga taken sunan littafin naku, wato kamusun Karin Maganar Hausa?
Haka dai ya ce, amma tun da ba masani ba ne, ba wanda ya yi kurme ne a cikin fagen adabi ba, haye ya yi, da wuya ya kama kan zaren. Shi fa ke cewa “dukkanin Shehunan Malaman tarihi har ma da wadanda ake da su a raye da su kan su daliban tarihi wadanda wasu daga cikinsu a yau su ne Shehunan Malamai ba su da kowace irin masaniya a kan kalmar kamusu domin kuwa kamus suka aminta da a kira kalmar.” Wannan shi ne wanda ya san abin da yake yi a fagen adabin Hausa? Shi fa ne a cikin sharhin yake cewa “idan kuwa har akwai malaman da suke da masaniya a kai, to jira ba ya buwaya kan fashin bakinsu musamman idan akwai wani taron masana Hausa da aka yi wanda ya nuna cewar maimakon kalmar kamus kalmar ta koma kamusun to sai a fito a yi bayanin mahalarta da muhalli da ma ranar da ka yi taron.”
Wanda ke da wannan tabbaci ai ya fi karfin a tsaya a yi cece-ku-ce da shi, ni kuma wannan gurguwar fahimtar da mai sharhin ya yi wa aikin kamusun Karin Maganar Hausa, ita ce kuskure na farko da ya bata sharhin.
Amma da alama akwai kanshin gaskiya a nan, domin yawancin dalibai kamus suka sani, ku ga shi kun zo da wani abu wai kamusu? Yaya al’amarin yake to?
Kalmar kAMUSU da bai sani ba ko wanda ya yi masa sharhin shi ma bai sani ba, ko bai taba ji ko gani ba, haka shi ma wanda ya rubuta masa sharhin, bai taba ji ko gani ba, ba abin mamaki ba ne, domin ba karatun ake yi ba. kamusu kalma ce da ta dade da shiga cikin Hausa da kuma karbuwa a tsakanin masana.
’Yan shekarun baya, bayan nan, wato a shekarar 2006 Jami’ar Bayero ta fitar da littafin kAMUSUN HAUSA cikin Hausa na farko a duniya. MALAMAN Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya da ke a Jami’ar Bayero, Kano suka tsara kAMUSUN ‘tare da taimakon wasu daidaikun masana’ da suka hada da Farfesa dandatti Abdulkadir da Farfesa (marigayi) Ibrahim Yaro Yahaya da Farfesa Abba Rufa’i da Farfesa Abdu Yahaya Bichi da Farfesa Ibrahim Ahmad Mukoshy da Farfesa dalhatu Muhammad da Farfesa Muhammad Dauda Bagari da Farfesa Maikudi karaye da Farfesa Bello Sa’id da Farfesa Lawan danladi Yalwa da Farfesa Bello Salim da Farfesa Mu’azu Sani Zaria da wasu da dama, karkashin shugabancin marigayi Sarkin Daura, Muhammad Bashar. Aikin wannan kAMUSUN HAUSA an yi kusan shekara 30 ana fama, har Allah ya kawo a buga shi a shekarar 2006. Ban san wani gamsasshen bayanin da zai tabbatar da cewa kalmar kAMUSU akwai ta a Hausa wanda ya fi wannan ba, wanda kuma ya samo asali daga cibiyar kula da lamurran Hausa. Dukkan wadannan manyan Furofesoshi da na ambata da suka samar da kamusun Hausa, wanda shi muka kwaikwaya muka samar da kamusun Karin Maganar Hausa, su ne kakanninmu a wannan fage na nazari da sharhi a adabi da harshe da al’adun Hausawa.
Haka kuma ita wannan CIBIYA ita ce mazaunar HAUSA LANGUAGE BOARD a tsawon shekaru. Ita wannan Hukuma da Cibiyar ta gada aikinta ne ta tabbatar da gudanuwar al’amurran Hausa da Hausawa a doron kasa. Idan wannan Cibiya da muke hankoro da ita, ta san da kamusu, ta kuma amince da shi. Idan kuma kakanninmu, Farfesoshin farko a wannan harka, sun daddagi, sun daddale, sun aminta da kamusu, mu a su wa za mu ce ba mu amince da ita ba? Harka ce ta ilimi ba ta shaci-fadi ba!
Idan kuma mai sharhin na bukatar sanin yadda kamusun Hausa ko kamusun Karin Maganar Hausa ya sami gindin zama ta fuskar nazarin ilmin harshe da nahawu, sai a koma aji, nan ne kadai mafita, ba hauragiya ba!
Za mu ci gaba