Kuskure daya Ke bata Sharhi – Farfesa Ibrahim Malumfashi (2)
To amma mai sharhin ya kuma ce littafin naku maimakon ya bi fasalin kamus da aka sani, sai ya buge da bayyana ma’anoni na karin magana 157, daga cikin sama da dubu 7 da aka tattara. Shi kuma wannan wane irin salo ne? Wato ka ga wannan ya kara tabbatar mana da cewa mai sharhin […]
To amma mai sharhin ya kuma ce littafin naku maimakon ya bi fasalin kamus da aka sani, sai ya buge da bayyana ma’anoni na karin magana 157, daga cikin sama da dubu 7 da aka tattara. Shi kuma wannan wane irin salo ne?
Wato ka ga wannan ya kara tabbatar mana da cewa mai sharhin yana kurme ne a cikin kogin jahilci. Mu tambayi kanmu, me kalmar kAMUSU ke nufi? Da Ingilishi ana kiran ta da DICTIONARY da Hausa kuma ana nufin MA’ANONI ko BAYANAI KAN BATUTUWA ko BIN DIDDIGI. Shi harshen adabi ba kowane dan ku-ci-ku-ba-nin dalibi ke gane shi ba. Abin da sunan littafin ke nunawa shi ne, ga kundi mai dauke da MA’ANONIN KARIN MAGANAR HAUSA, babi guda ne aka kebe da ya yi wa mai karatu gwari-gwarin karin magana, wato inda ya yi kama da abin da mai sharhin ya sani na kAMUSU, irin na yau da kullum. Kenan an batar da ‘masani’ a nan, domin an yi masa wuji-wuji ya kasa gano gabas, sai ya nuna sama!
A tuna, wannan aiki na bincike ne a kan Karin Maganar Hausa wanda ba a taba yin kamarsa ba (ba wai nuna sani ko isa ba ne muke yi, gaskiyar lamarin kenan). Tun da farko tunanin marubutan littafin shi ne a kandame Karin Maganar Hausa a waje daya a karo na farko ta fuskar bin diddigi tun daga samuwar ta a ka zuwa ga rubatawa da Ajami da Larabci da kuma Hausar Boko. Haka kuma an sake bin diddigin Karin Magana a kafafen watsa labarai na rediyo da talbijin da kuma yanar gizo, wannan ne ya bayar da damar da aka tattaro Karin Magana sama da dubu 7, aka ajiye a wuri daya. Ba wani aiki a duniyar nazarin karin maganar Hausa da ya yi wannan hobbasa, wanda ya kokarta yin haka shi ne ke dauke da guda dubu 2. Wannan aikin shi ne ashararanci?
Me ya sa wannan littafi naku ya sha bamban da saura da aka yi a baya?
Babban abin da ya sa wannan aiki ya sha bamban da saura shi ne, a karo na farko an hada tattarawa da ginuwar tarihi inda aka yi waiwaye kan nazarce-nazarcen karin magana da hujjojin da suka wajabta bincike da adana karin magana da makasudin tattara da adana karin magana. Baya ga wannan an yi tsokaci kan kasar Hausa da ginuwar adabin baka, wanda shi ne mazaunin karin magana tun da farko, an kuma kawo takaitaccen tarihin kasar Hausa da samuwa da ginuwar adabin bakan Hausawa, inda aka yi tsokaci kan waka da take da kirari da habaici da salon magana da bakar magana. An kuma kokarta kawo tarihin Samuwar Karin Maganar Hausa da asalin Karin Magana da rabe-raben Karin Magana, inda a karo na farko aka zo da guda 23 da kuma wuraren amfani da Karin Magana a kasar Hausa.
A wani sashe na wannan littafi kuma an bi diddigin karin Maganar Hausa a rubuce, wato bayan ta baro kai, ta yadda ta bi zangunan da ta bi a zamanin zaman gargajiya da bayan zuwan Larabci da Musulunci da kuma zuwan Turawa da Boko da bayan amsar mulkin kai, daga nan aka dubi matsayin karin maganar Hausa a yau. Dukkan wannan aiki ga mai sharhin kuskure ne!
Haka a wani bangare kuma an zo da bayanin sauye-sauyen da Karin Maganar Hausa ta samu ta fuskar tsarin sauti da ma’ana da kwayoyin sauti da karin sauti da naso da karin harshe da tsarin jimla da ilmin ma’ana da kuma irin kamancin da kuma bambanci da ake samu a cikin karin magana, tsakanin mabambantan kasashen Hausa. Bayan wannan an kuma bi sawun samuwar sababbin karin maganar Hausa ta yadda tsofaffi suke komawa na zamani da yadda na zamani suke a cikin wannan zamani, aka rufe da yadda karin magana take da alaka da shirin kauyantar da duniya, wato globalisation. Abin da ke cin karensa, babbake a wannan lokaci. Duk wannan domin a bata al’adun Hausawa aka yi in ji mai sharhi?
Daga karshen aikin ne aka baje kamusu na karin maganar irin wanda aka saba ji da gani. Ko kafin nan sai da aka yi bayanin me ya sa ake bukatar kamusu irin wannan da irin dangantakar da ke tattare da labari a karin magana da yadda lafuzzan Larabci da Ingilishi da falsafar rayuwa ke wa mutane tarnakin gane karin magana a zahiri. Bayan nan an zo da misalin wasu karin magana da aka yi wa fida don a ga amfanin bin tafarki irin na wanan bincike da ya samar da littafin. Duk wadannan suna kunshe a cikin shafi 122 daga cikin shafi 297 na littafin. Kenan shafi 175 na littafin RATAYE ne na karin maganar Hausa kusan dubu 7 da aka tattaro. Wadanda su ne abin bakin ciki ga mai sharhin, me ya sa za a yi abin da wani bai taba yi ba?
To amma mai sharhin ya ce shi ya bi littafin daga farko har karshe sai da ya zakulo kura-kurai dubu da daya, in kuwa haka ne da alama akwai gyara a aikin?
Abin lura a nan shi ne dukkan ‘kura-kuran’ dubu daya da mai sharhin ke ta kururutawa, daga bangaren RATAYE suka fito, wato tsarin ABACADA… da aka yi wannan bangare na littafin, wanda an yi haka ne domin kokarta adana tsofaffi da sababbin karin maganganun Hausa a rubuce. Maimai da aka samu da rashin daidaituwa na wadansu kalmomi da ya tsakuro sun faru ne bisa abubuwa uku, ko dai bambancin karin harshe ko canjin kalmomi ko kuma juya zance bisa mabambantan ma’anoni. Kada mu manta cewa yawancin karin maganar a lardin Sakkwato aka tattaro su, kuma an san cewa yanki ne da ke da arzikin kalmomi, mabambanta. Kenan ba abin mamaki ba ne a ga karin magana mai dauke da kalmomi mabambanta, ta yadda za a sami guda biyar ko shida masu gini da ma’ana guda. Irin wadannan su ne ya kira kura-kurai.
To me za ka ce kan batun da mai sharhin ke neman nunawa na cewa aikin na binciken digiri na biyu ne da dalibi Nahuce Marafa Ibrahim ya yi, shi ne kai kuma ka bi ka kanannade a matsayin naku, ku biyu, alhali kai ba komi ka rubuta a ciki ba?
Wannan ma abin dariya ne ga wanda ya san harkar koyarwa da nazari a wannan fage. Bari in yi wa batun fashin bakin da za a gane da kyau.
Na farko, fagen da ake cewa Ibrahim Malumfashi ya gwanance a kai shi ne TARIHIN ADABI ba TARIHI ba, kamar yadda mai sharhin ya nemi ya nuna. A tsarin karatun digiri a Jami’a, ana hada dalibi da malami ne bisa fagen da ya fi kwarewa a kai. Tarihin samuwar karin maganar Hausa, fagen tarihin adabi ne, fagen Ibrahim Malumfashi ne. Saboda haka ko da dalibi Nahuce Ibrahim Mafara ya shigo ajin Ibrahim Malumfashi don karatun digiri na biyu, fagen da malamin ya gwanance ne aka turo shi.
Na biyu, hatta bigiren da dalibi Nahuce Ibrahim Mafara ya dauka don bincike, malaminsa ya sa shi bisa hanya. Shi ya hada shi da tulin sama da karin magana dubu 6 da ke jibge a National Archibes da ke Kaduna, wanda su suka kasance tsittsigen aikinsa na tsawon shekara 4.
Na uku, ko da dalibi Nahuce Ibrahim Mafara yake aikinsa na neman digiri ya iske malaminsa tsundum a wannan fage. Tun kafin ya shigo cikin fagen tuni wannan tsari da ya hau, wasu irinsa sun sami digiri na daya da na biyu, wasu zuwa yanzu har digiri na uku.
Na hudu ko da dalibin ya kammala digirinsa ya kama gabansa, malaminsa ya ci gaba da nazari da bincike, domin ko kafin ya shigo Jami’a domin kara karatu tuni Malam ya gabatar da takardu da kasidu kan Hausar Da Ta Gagari Bahaushe da kuma samar da dan karamin littafin da ya kira kAMUSUN KARIN MAGANAR HAUSA, wanda bai kai ga bugawa ba. Wannan shi ne ya jawo auren bincike tsakanin dalibi da malami daga baya. Shi ya haifar da samar da wannan littafi mai babi 6, dauke da binciken dalibi da na malaminsa da kuma taskatattun karin magana sama da dubu 7 da Malam ne ya kasance bankin da ke ajiye da su ko ya dora dalibi bisa godaben kalar ilimi.
Wani karin haske shi ne, wannan al’ada ta aure tsakanin dalibi da malami a fagen rayar da ilimi, ba mu saba da ita a fagen nazarin Hausa ba ne, shi ya sa ta zama wabai ga mai sharhi ko kuma ‘malaminsa’ na boye. Wannan shi ne karo na farko da aka soma ganin yiwuwar haka, alhali a wasu bangarorin nazari, musamman a fagen kimiyya da sauransu an dade ana cin moriyar haka. Kila ganin cewa an fito da wani sabon salon ci gaba shi ya jawo wannan badakalar sharhi.
Za mu ci gaba