Kuskure daya Ke bata Sharhi – Farfesa Ibrahim Malumfashi (3)
Auren bincike kamar yadda ka nuna halal ne ba haram ba, ba kamar yadda shi mai sharhin ya nuna ba kenan ko? Auren bincike da samar da littafi daga ciki ai ba matsala ba ce, ci gaban ilimi ne. Idan har wannan ‘sabon’ fasalin ciyar da adabi gaba ya yi wa mai sarhin turnuku ko […]
Auren bincike kamar yadda ka nuna halal ne ba haram ba, ba kamar yadda shi mai sharhin ya nuna ba kenan ko?
Auren bincike da samar da littafi daga ciki ai ba matsala ba ce, ci gaban ilimi ne. Idan har wannan ‘sabon’ fasalin ciyar da adabi gaba ya yi wa mai sarhin turnuku ko shi da masu koya masa karatun sun ga abin da ba sa so, to da alama sun fada cikin kogin wahala, domin yanzu ma aka fara irin wannan tada ta aure a ginuwa da ci gaban adabin Hausa.
Yanzun nan muna kan wasu irin su da suka hada da littafin Labarin Hausa A Rubuce wanda na rubuta da hadin gwiwar dalibaina (da suka kammala ko na biyu ko na uku); da suka hada da Dokta Adamu Rabi’u Bakura da Dokta Umar Aliyu Bunza da Dokta Balbasatu Ibrahim Yabo da Dokta Aliyah Adamu Ahmed da Dokta Shu’aibu Hassan da Bashir Abusabe da Ramatu Lawal Usman. Litttafi ne mai kusan shafi 600 da zai kandame rayuwar rubutaccen labarin Hausa a tsawon shekara 80 da samuwa.
Haka akwai littafin Dare Dubu Da daya da muke aiki kansa ni da danladi Haruna da Bukar Mada, aikin hadin gwiwa ne tsakanin malami da dalibai, abin alfahari ne a ga aure irin wannan ya samar da littafi, shafi sama da 3,000. Ba don komi ba sai don raya da ci gaban adabin Hausa.
Akwai kuma littafin Mata Marubuta A kasar Hausa, shi ma ni na jagoranci rubuta shi tare da hadin gwiwar Dokta Balbasatu Ibrahim Yabo da Ikilima Abba Abdulkadir. Littafi ne da ya karade rayuwar mata marubuta a tsawon shekara sama da 300 da suka wuce a cikin kasar Hausa, dauke da tarihin fitattun mata marubu na kowane karni.
Wannan irin auren shi zai samar da littafin Adabin Kasuwar Kano, na Ibrahim Malumfashi da Bashir Abusabe. Wannan kila ba sai na fadada zance ba, kokari ne na dangance rayuwar rubutaccen labarin Hausa, tsakanin 1980 zuwa yau.
Akwai littafin Adabin AMINU ALA a bisa hanya shi ma, na Ibrahim Malumfashi da Abdurrahaman Faruk, wanda ke dauke da rayuwar mashahurin marubucin labaran Hausa da wakoki a wannan zamani. Shi ma an kammala, sai ’yan gyare-gyare da ake kai.
Akwai kuma littafin Adabin A Daidaita Sahu na Ibrahim Malumfashi da Sakeena Adamu Ahmad yana bisa hanya shi ma. A nan an kwakulo irin gudunmuwar da shirin A Daidaita Sahu na Gwamnatin Jihar Kano a karkashin jagorancin tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau ya bayar wajen gina da raya wani bangare na adabin Hausa.
Wannan fa duk baya ga hadakar malami da daliban Makarantar Malam Bambadiya da ta samar da littafin gajerun labarai na Jamhuriyyar Mabarata da ’Yan Yau. Saboda haka in har irin wannan auren bincike da nazari da samar da littatafai ya kasance jafa’i ga wasu manazarta ko masharhanta, to ba za mu fasa ba, ba kuma za mu ja da baya. Zagi ko cin mutunci ba yau aka fara ba, ba kuma kanmu za a kare ba. Bincike da nazari sana’armu ce, ita muka sani, ita muka iya, ba kuma wani Farfesan boye ko wata masarauta da ta isa ta hana mu gudanar da irin wannan aiki.
Daga bayananka, kana nuna cewa tamkar ku ba kwa yin kuskure a aikin adabi, alhali ga kura-kurai nan jibge kamar yadda mai sharhin ya nuna?
A kula, ba mu ce ba mu yin kuskure ba, a matsayinmu na ’yan Adam, ajizai muke, a kullum fatarmu ita ce Allah ya gafarta mana bisa ga inda muka yi tuntube, domin ba za mu yi shi da gangan ko domin bata tarbiya ba. Duk inda mai sharhin nan ya nuna kuskure na gaskiya, ba na karya da neman cin mutunci ba, za mu gyara In Sha Allahu a bugu na gaba, wannan ba matsala. Amma abin da ba mu yarda da shi ba shi ne a yi amfani da sojan gona domin a bata aikin da aka yi shekaru ana fama ba da wata hujja kwakkwara ba!
Wannan ne zai kai mu ga zance na gaba!A duk cikin sharhin da mai sharhin ya gudanar game da kAMUSUN KARIN MAGANAR HAUSA, ba abin da ya fi mayar da hankali kai irin wai kun yi hadin gambizar basirar rubuta takardun ‘batsa’ da ashararanci a cikin aikin naku. Me za ka ce kan haka?
Abin da nake ta kokarin taushe dalibai kai ke nan cikin tsawon wata guda da fitar wannan kaharu da muzanci. dalibai da dama sun so su mayar da martani da kakkausan harshe, na hana. A bi abin a ilmance.
A sharhin nasa ga abin da ya ce, “ga kadan daga cikin Karin Magana masu dauke da ashararanci kamar haka: “Gaba mai dadi amma sai gaban yarinya” a shafi na 167. “Don jini ba a kin gato.” a shafi na 151. Da kuma “Babban gato abin zuwa buki” a shafi na 136. Da kuma “Ina amfanin girman bura ba tashi” a shafi na 182. Su ke nan ya kawo guda hudu daga cikin karin magana dubu 7, wannan shi ne mun cika batsa da ashararanci a cikin littafin. Wannan ba adalci ba ne daga mai nazari.
Ni abin da ya fi daure man kai shi ne, saboda mun taskato karin maganar da Hausawa suka yi a da, a lokacin suna masu bautar rana ko wata ko suna a matsayin Maguzawa ko Musulmi ko kuma Kiristoci ko wadanda ba su yarda da Allah ba baki daya sai a ce an yi laifi? Ko kuma kawo karin magana da kalamai da aka gina karin maganar da su tun asali, wadanda ba su yi wa mutum dadi ba sai abin ya zama laifi a fagen nazari? Shin Hausawa suna da karin maganar da aka kawo ko kuwa ba su da ita? Shin kaga karin maganar muka yi domin cin mutuncin al’adun Hausawa ko kuwa haka muka tsince su? Shin ya dace a fagen nazari a dinga suturta aikin adabi da shekara da shekaru haka abin yake don kawai Hausawa sun samu kansu a cikin wani sabon yanayi? Shin batsa ce ko ashararanci tattara karin maganar Hausa da kalmomin sassan jiki ko bauta ko kasuwanci ko mulki ko sara ko bakar magana ko zancen banza na Hausawa? Shin muna da ikon da za mu dage cewa karin magana irin wadannan da aka lissafo a cikin wannan littafi bai kamata a bayyana ko adana su ba?
Nan ina matsalar take? Me ake nufi da batsa da ashararanci a wannan hauji? A lura fa wadannan karin maganar Hausawa ne da aka tattaro a tsakanin al’ummmar Hausawa, a tsakanin shekarun 1900 zuwa 1921 a cikin kauyuka da gararuwa da biranen tsohuwar Lardin Sakkwato. Ba a da su ne a tsakanin Hausawan? Ko kuwa ana nufin sai mai nazarin tarihin adabi ya canza fasalin abu don kawai wani mai sharhi bai son jin haka? Shi wanda ya gina karin maganar, shi ne asharari kenan ko kuwa (Hausawa) masu karin maganar ne ashararu? A fagen tarihin adabi, ba a sauya wa abu riga don faranta wa wasu. Abin da kawai zai maganin haka, shi ne kada a fara tsarawa ko ginawa ko kattabawa! Da an gama ginawa to ya shiga tarihi, bai kankaruwa!
Kana nufin cewa Hausawa suna gina karin magana da lafuzzan batsa, me zai hana to abar amfani da irin wadannan karin magana dungurungum?
In muka yi haka ba mu yi wa Hausawa ko adabin Hausa adalci ba. Kamar ka ce ne Hausawa ba su taba zama Maguzawa ko Yahudawa ko Habashawa ko Kibdawa ba, ko ba su taba yin tsafi ko bautar rana ko wani abu makamancin haka ba. Hausawan yanzu ne wasu suke Musulmi, wasu har yanzu Maguzawan ne, wasu Kiristoci ne, yaya za ka yi da wannan hadakar? Sai ka ‘tsabtace’ adabi don yanzu yawancin Hausawa Musulmi ne? An gurbata adabi kenan.
Irin wannan shi ke faruwa tsakanin wasu sassan al’ummar yankin kasar Hausa tun da dadewa, saboda bambancin karin harshe ko wurin zama. In Bahaushen Katsina ya ce GINDIN BISHIYA, na Sakkwato ihu zai yi ya ce ai batsa ce, domin ba a fadin gindi haka gatsar a yankin Sakkwato, sai dai a ce GUTSUN BISHIYA. Nan kuma wata sabuwar matsala ce, gutsu kuma ga Bakatsine, batsa ce! Duk kalmomin da karin magana ta zo da su, na Hausa ne, ko da kuwa na batsar ne, kuma har abada ba ka iya hana Hausawa gina karin magana da su.
Bisa irin wannan tunani ke sa wasu yanzu ke kokarin canza karin maganar Hausa zuwa ta son ransu ko biye wa wasu kananan tunani na ba gaira ba dalili. Misali, idan yau ka yi karin magana da cewa duk bori daya ake yi wa tsafi, sai Musulmin Bahaushe ya ce ka yi sabo. Ga karin misali domin mu fahimci batun sosai.
Allah nawa, Annabi na uwata.
Duk dadinka da Allah sai ya kashe ka.
Allah ubana, in ji shegiya.
Gafara Allah, Bamaguje ya taka Masallaci.
Shakiyyi, Allah na tsoronka.
Allah na dawo, in ji matar dan ci-rani.
Ban ga alama ba, an ce da kuturu Allah ya sawwake.
Allah gyara, makaho ya ce a yaushe.
Abin tambaya shi ne, shin Hausawa ba su yi wadannan karin magana ba ne? Hausawa ba su gina tunanin samar da karin magana ta amfani da kalmomi irin wadannan ko makamantansu ba ne? Me za a sakaya? Me za a suturta? Me za a sa wa kunya a ciki? Haka kuma Hausawa ba su yi bori da bautar tsafi ba? Idan da ba su yi ba, to ba za su gina karin magana kan haka ba! Duk yadda muke ji a yanzu game da irin wadannan karin magana, ba abin da za mu iya yi kan su. ‘Shegiya ba ta da uba in ba Allah ba, in ji Bahaushe,’ wannan gaskiya ne. Tunanin Bahaushe ne! Haka kuma akwai wanda zai rayu har abada, bai mutu ba? Babu, saboda haka komin dadinka, Allah sai ya dauki ranka, ina matsala a nan? Shi kuwa masallaci ai dakin Allah ne, duk wanda ya taka shi, ya taka dakin Allah, (ko ma Allah), ina ruwan Bamaguje, in ya ce gafara Allah, kada in taka ka? Shin ba Bahaushe ba ne ya ce an tambayi Gwari ka san Allah, ya ce, ‘ga jida, ga jida?’ Ma’ana, shi da yake makwabtaka da Allah a ce bai san shi ba! Domin ga gidan dan Gwari ga Masallaci! Ina batsa ko sabo ko ashararanci a nan?
Za mu ci gaba