Kuskure daya Ke bata Sharhi – Farfesa Ibrahim Malumfashi (4)
Wannan sai na ga lallai tamkar batsa ce da sabo, me ya sa za a sake dawo da su tun da sun bace kuma Hausawa yanzu yawanci Musulmi ne, suna kyamar irin wadannan kalamai? Eh, batsa ce ko ashararanci ga Musulmin Bahaushen yanzu amma tana nan a karin maganar ta, karin magana ce, mai dadadden […]
Wannan sai na ga lallai tamkar batsa ce da sabo, me ya sa za a sake dawo da su tun da sun bace kuma Hausawa yanzu yawanci Musulmi ne, suna kyamar irin wadannan kalamai?
Eh, batsa ce ko ashararanci ga Musulmin Bahaushen yanzu amma tana nan a karin maganar ta, karin magana ce, mai dadadden tarihi, sai a canza tarihi don a faranta wa wani? Ba a haka a fagen nazarin adabi. Kuma ma abin tambaya, wa ya san da irin wadannan karin magana a halin yanzu? Sai a fagen nazari, kenan ba wani ashararanci sai gaskiya.
Ni sai na ga ba ma asharari in ba wanda ya yi wannan sharhi ba, wanda batu na cikin littafin nazari, da ake sayarwa domin mai sha’awa ya saya ya karanta, ba kuma wanda ya je yana yayata wani bangare don watsa batsa, amma ka tsamo wani bangare da bai taka kara ya karya ba, kana yayatawa, a cikin kafafen da kowa da kowa zai iya ji da gani, irin jarida da Intanet! Wane ne ashararin a nan?
To ba a iya tsabtace adabi ko tsarkake shi kenan, duk irin daudar da ya zo da ita, sai a amsa?
Haka dai wannan mai sharhi ko wadanda suka ingizo shi suke so dinga yi wa adabin Hausa. Amma haka ba ya yiwuwa. Yanzu ne za mu tsarkake wanda muke yi don amfanin gaba. Na jiya suna nan yadda suke!
Idan mai sharhi bai sani ba to ya sani, aikin adabi hoto ne! In an dauko taswirar yadda rayuwa take a zamanin da, kai ko ma yanzu, hoton ba ya karya. Aikin adabi madubi ne, in ka leka ciki ka hango abin da ba ka so, ba zai hana abin wanzuwa da gudanuwa ba. Yaga hoton ko fasa madubin ba zai magance matsalar ba. Adabin na nan har abada a zukatan al’umma, aikinmu shi ne tattara shi da nazari! Abin da kurum muka yi kenan ba ashararanci ko gina batsa ba!
To amma mai sharhin cewa ya yi ko a tattara karin magana na wannan zamanin kun nuna son kai ko bangaranci, kamar ku ’yan APC ne ba ’yan PDP ba! Me za ka ce?
Wato mai aikin tattara da nakaltar adabi a kowane zangon rayuwa ba ruwan sa da wani ko wata ko wasu, hoton yake ajiyewa ko ya tsira wa madubin idanu. Abin da ya gani shi yake fada. Bisa irin wannan fasali za a dubi karin magana na wannan zamani ko wadanda tsarin mulkin soja ko na siyasa ya samar. Ga wasu da muka tattaro a matsayin misali:
Ganganci, marin soja a kusa da bariki.
Samun dama, sayen tikiti zuwa London sayen ruwan sha.
Rabo, makwabci ya biya wa matar makwabci kujerar Makka.
Rainin wayo, an ce da barayo wuce ka tafi, ya ce har da kayan!
Da wasu mazan, gara Indomie da miyar kuka.
Mace mai kwazo, za ta haihu ko ba miji.
Ka ji wata sabuwa, talaka a cikin jam’iyyar PDP.
Ba a banza ba, talaka a PDP.
karfin hali, Bakano da jar hula.
Kowa ya tuna bara, bai ji dadin bana ba, dan Acaba ya kalli babur dinsa a Kano.
Kwankwasiyya, maganin ’yan duniya.
Banza a banza, talaka a Takai.
Abin tambaya a nan, shin laifi ne tarkato irin wadannan karin magana? Ba a yi su ba ne? Ko kuwa don sun shafi wani bangare na rayuwa, misali sojoji ko jam’iyyun siyasa sai a noke a ki kawo su cikin kundin kamusun Karin Maganar Hausa? Me ruwan masu gina karin magana da siyasa ko bambancin akida ko addini? Abin da ya faru ne ke agazawa wajen samar da karin maganar. Kenan mai sharhin nan ya dage cewa kawo karin magana mai dauke da PDP ko APC ko wata siyasa can daban, kuskure ne, ina ga bai yi wa adabi adalci ba! Batun JAR HULA da TAKAI da dAN ACAbA da KWANKWASIYA a Jihar Kano, idan ba su tayar da karin magana a tsakanin Hausawa to ban san abin da zai agaza ba! Rashin sani aka ce ya fi dare duhu!
karin haske a nan shi ne tun daga farkon wannan shekara, musamman bayan da wannan littafi ya fita kasuwa, an ci gaba da ganin sababbin karin magana da suka wanzu, kuma za su ci gaba wanzuwa har abadan, abadan! Ba mai ikon hanawa. Mun ga ta ’Yan Boko Haram da Ebola da Ebele da wasu irin su da dama, muna nan muna ta tattarawa da adanawa, domin ’yan gobe, wadanda ba ashararu ba!
An ga a wasu kafafe kana cewa akwai wata boyayya dangane da wannan sharhi, inda kake inkarin akwai sa hannun masarautar Daura a ciki, me ya jawo wannan tunani ganin cewa masarautar ba za ta sa a yi wannan mummunan sharhi ba tun da ba huruminta ba ne?
Wannan wani zance ne daban, yana kuma bukatar dogon sharhi don a fito da batun fili. Abu na farko da ya daure kai shi ne mene ne matsalar littafin da ake ta cece-ku-ce a kan sa? Shin wace irin barna ce da ake ganin zai yi wa al’ummar Hausawa da wasu da suka fi shi ‘batanci’ ba su yi ba? Idan aka lura da harshen mai sharhin sai a ga cewa tamkar ba littafin ne matsala ba, kila matsalar ta wadanda suka rubuta shi ce. To sai mutum ya sake tambayar kansa, me wadanda suka yi wannan aikin tayar da littafi suka yi wa mai sharhin ko wadanda suka turo shi? Me zai hana in za a zagi ko cin mutuncin Ibrahim Malumfashi ne a ci mutuncinsa shi kadai ba tare da an jefo Hausawa da aikin adabinsu ba?
Wannan shi ne ya fi daure kai, amma daga baya da na tambayi wasu daga cikin dalibai da ke Sakkwato, me ya jawo haka; sun nuna mani cewa wai sun ji mai sharhin na cewa, “Farfesa taba mu ya yi, shi ne muka rama.” Ma’ana wani rubutu da na yi a cikin jaridar Aminiya watannin baya na HAUSA DA HAUSAWA da kuma WANE NE KUMA BAYAJIDDA? Bai yi wa masautar Daura dadi ba, shi kuma mai sharhin wai ya yi wa masarautar aikin rubutu kan wannan batu an buga a jaridar Leadership Hausa. An ce wai na karyata tarihin asalin Daura da Bayajidda daga nawa nazari da bincike, shi ya sa aka nemi a bata ni da aikin da na dade ina yi wa adabin Hausa.
Wannan in har gaskiya ne, to ina ga masarautar Daura ba ta yi mani adalci ba, domin a matsayina na mai bincike da nazari game da tarihin adabi, wanda tarihihin Bayajidda na cikin fagen irin wannan nazari, kamata yi ta neme ni ta ga hujjojina da na zuba daga cikin littafin da na rubuta na ASALIN HAUSA DA HAUSAWA mai dauke da shafi sama da 400. Tsakure ne daga cikin bincike na tsawon shekara bakwai na buga a cikin Aminiya. In sun nemi in yi bayani ba zan ki baje hajar hujjojina a gabansu ba, in har akwai kuskure ko wasu kwararan hujjoji da suka fi nawa, a kullum shirye nake na karbi gyara don ci gaban ilimi.
Amma a koma ta bayan fage a biya yaro kudi, a aje shi a cikin otel na kwanaki tare da sojojin haya domin a rubuta sharhin batunci da cin mutunci da muzanta Hausawa da adabinsu, ina jin ba daidai ba ne.
Daga karshe wane kira za ka yi wa wadanda suka karanta wannan sharhi ba tare da karanta ainihin aikin kamusun ba, suka kuma amince cewa an ci mutunci Hausawa?
Kiran da zan yi shi ne, a rika auna dukkan abin da mai sharhi ya yi a cikin kowane irin fage, ba komi ne da ke cikin takarda yakan kasance gaskiya ba. A sani cewa aikin koyarwa da nazari ce rayuwar irin mu da ke jami’a, bai kuma yiwuwa mu fara tun muna dalibai mu shiga matsayin malamai da masana, mataki bisa mataki tsawon shekara 25 ba mu lalace ba, sai yanzu da muke shirin barin fage. Koyarwa da nazari da bincike game da adabin Hausa da Hausawa, amana ce, ban kuma taba cin wannan amana a baya ba, balle yanzu, ba mu kuma fatar yin haka nan gaba.
Mun kammala