Kuskure ne a bude iyakoki don shigo da shinkafa – Sarkin Noman Kebbi
Alhaji Muhammdu Jiga Sarkin Noman Jihar Kebbi, ya ce babban kuskure a sake bude kan iyakokin kasar nan domin a shigo da shinkafa daga kasashen waje. Ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da Aminiya: Me za ka ce kan kiran a bude kan iyakokin kasar nan, domin shigo da shinkafa daga kasashen waje? Mu kara […]
Alhaji Muhammdu Jiga Sarkin Noman Jihar Kebbi, ya ce babban kuskure a sake bude kan iyakokin kasar nan domin a shigo da shinkafa daga kasashen waje. Ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da Aminiya:
Me za ka ce kan kiran a bude kan iyakokin kasar nan, domin shigo da shinkafa daga kasashen waje?
Mu kara bunkasa noman shinkafa da muke yi a Najeriya shi ne mafita. Idan muka yawaita shinkafar da muke nomawa a Najeriya za ta wadata, amma ci gaba da shigo da shinkafa daga kasashen waje ba shi ne mafita ba.
Ya kamata mutanen Najeriya su gane bambancin shinkafar da muke nomawa a Najeriya da shinkafar da ake shigowa da ita daga waje – dadi da gardi shinkafar da muke nomawa a Najeriya ba daidai take da shinkafar da ake shigowa da ita daga waje ba. Kuma shinkafar da manomanmu suka noma, a sabuwarta muke amfani da ita, ba tare da ta dade a ajiye ba. Amma shinkafar da ake shigowa da daga waje, wata ta kai shekara sama da 15 da nomawa.
A Najeriya za mu iya noma shinkafar da za mu ci har mu fitar zuwa kasashen waje. Yanzu a nan jihohin Kebbi da Sakkwato da Kano da Katsina da Neja za ka ga ana noman shinkafar nan rani da damina. Saboda haka ’yan kudaden ajiyarmu na waje mu tsaya mu rike su, don nairarmu ta yi daraja a kasuwar duniya. Idan ba mu yi ba, babu yadda za a yi darajar kudinmu ta farfado.
A da muna sayo shinkafa daga kasashen Thailand da China da yankin Kudancin Asiya. Idan ka sayi shinkafa kamar ta Naira miliyan dubu bakwai daga China ko Thailand ka kara wa manomansu karfin gwiwar bunkasa harkokin nomansu. Domin za su kara yawan filayen da za su yi noma, za su kara dibar leburorin da za su yi musu aiki a gonakinsu.
Idan ka sayo abinci daga waje ka tauye manomammu na Najeriya, domin yin haka zai sa su rage yawan filayen da suke nomawa da yawan leburorin da suke yi musu aiki. Kuma ciniki a kasuwanni zai ragu domin manoma ba su da kudi, ka ga a nan an samu hasara.
Saboda haka muna kira ga gwamnatin Buhari kan ta dage ta tsaya kan matsayin da ta dauka, na rufe kan iyakokin domin hana shigowa da kayayyakin amfanin gona da wasu haramtattun kayayyaki zuwa kasarmu. Mu yi kokari mu dogara da kayayyakin abincin da muke nomawa a Najeriya.
Bude kan iyaka don shigo da abinci babban kuskure ne. Idan kasa tana sayen abinci daga wata kasa a kullum tattalin arzikin kasar karyewa zai ci gaba da yi. Domin duk kudin da kasa ta samu za ta rika sayo abinci ne da shi. A kullum kudin kasar za su ci gaba da tafiya. ’Yan kudaden ajiyarmu ne ake kukkulewa a je a biya kudin wannan abinci da ake shigowa da su. Don haka ba daidai ba ne a sake bude kan iyakoki don a ci gaba da shigowa da shinkafa.
Me kake ganin ya sa mutanen kasar nan, musamman na Arewa suka rungumi aikin noma a shekara hudu da suka gabata?
Abin da ya sa mutane suka rungumi aikin noma a shekara hudu da suka gabata, shi ne sun gane cewa shugabancin da ake yi a yanzu, ya nuna musu cewa su dawo kan tafarkin gaskiya su kama noma. Domin haka, yanzu kowa ya fahimci cewa idan ya koma noma zai zauna lafiya a rayuwarsa. Saboda haka ka ga yanzu kowa ya koma noma a Najeriya. Domin shi ne tafiya ta gaskiya a Najeriya, mu yi noma mu noma abincin da za mu ciyar da kanmu, idan ya ragu mu fitar zuwa kasashen waje.
Idan al’ummar kasar nan suka ci gaba da rungumar aikin noma wane ci gaba ne kake ganin Najeriya za ta samu?
Idan kowa ya kama noma a Najeriya nan da ’yan shekaru kadan Najeriya za ta bunkasa. Domin za a samu wadataccen abinci, miliyoyin ’yan Najeriya za su samu ayyukan yi, kudade za su samu a hannun talakawa kuma darajar kudinmu za ta farfado. Abin da muke bukata shi ne gwamnati ta sanya matakan tsaro, idan aka yi noma da yawa ta fito da kudi, ta sayi kayayykin amfanin gonar da aka noma a farashin da manoma za su samu riba, ta saya ta ajiye a manyan runbunanta na adana abinci. Idan aka yi haka manoma za su ci gaba da yin noma domin sun san idan suka yi noma nan, za su sayar su biya wa ’ya’yansu kudin makaranta da sauran bukatun yau da kullum.
Wane kira kake da shi ga manoma?
Ina kira ga manoman kasar nan su dage su kara gonaki. Idan manomi yana noman masara ce to ya kara da noman dawa da gero ko wake. Manomi ya yi noman da zai samu abincin da zai ciyar da iyalansa kuma ya sayar ya biya bukatunsa na yau da kullum.