Kuskure ne a yi sulhu da masu aikata miyagun ayyuka – Ali kwara

Fitaccen mai yaki da ’yan fashin nan da masu aikata miyagun ayyuka, Alhaji Ali kwara a kwanan baya ya yi wani artabu da ’yan fashi a dajin Maladumba da ke Misau a Jihar Bauchi. Manema labarai sun yi masa tambayoyi kan abin da ya kai shi dajin da kuma dalilin da ya sa aikata miyagun […]

Kuskure ne a yi sulhu da masu aikata miyagun ayyuka – Ali kwara

Fitaccen mai yaki da ’yan fashin nan da masu aikata miyagun ayyuka, Alhaji Ali kwara a kwanan baya ya yi wani artabu da ’yan fashi a dajin Maladumba da ke Misau a Jihar Bauchi. Manema labarai sun yi masa tambayoyi kan abin da ya kai shi dajin da kuma dalilin da ya sa aikata miyagun laifuffuka da fashi da makami ke ci gaba da karuwa:

 

Kwanan baya an ce ka yi wani artabu da ’yan fashi a dajin Maladumba da ke karamar Hukumar Misau a Jihar Bauchi yaya al’amari ya kasance?

Alhamdu lillahi, artabun da muka yi a dajin Maladumba da taimakon ’yan sandan ofishin Sufeto Janar da suke tare da ni ne da kuma ’yan sandan Jihar Bauchi. barayin ba a dajin suke ba, zuwa suka yi, sun fito ne daga Jihar Zamfara, amma kafin nan mun riga mun yi ayyuka a kansu mun san su mun gane su mun san motocin da suke da su da makamansu mun sa musu ma’aikaci, wanda ke kula da abubuwan da suke yi yana ba mu labari. To sai ya ba mu labari cewa za su taso da mota ga lambar motar ga launin motar, sai muka sa ’yan sandanmu suka tsare hanyar suna bincike Allah Ya taimake mu an samu motar aka kama su aka daura musu ankwa a hannunsu, aka sa su a cikin motar kuma daga baya motar ta samu matsala. A wajen da motar ta tsaya sai daya daga cikinsu ya ce yana jin fitsari aka bude musu kofa, da ya sauko sai sauran ma suka diro daga cikin motar ashe duk ankwar da aka sa musu matacciya ce, sun bude ankwar a dan karamin lokaci suka shiga daji. Da suka nufi dajin Maladumba ne, sai ’yan sandanmu suka kira ni suka ce ’yan fashin nan sun kwace. Na ce to kada ku bar kafarsu inda suka taka ku saurara kuma a wajen da yake ko’ina ina da jama’a na yi ta tsshinsu da dare a waya, na buga waya Doguwa da Giyade, na buga cikin Misau na buga Maladumba, har Zindi duk mafaraucin da yake kewayen na kirashi na fada masa abin da ya faru kuma ga inda suka sa gabansu. Na ce a yi waya wa mafarautanmu gaba daya a je a gaya wa mutanen gari. Kafin gari ya waye zancen ya gama kasa, muka ba da shawarar cewa duk inda aka same su a kula da su don miyagu ne, an samu daya tsakanin Misau da Giyade a cikn dajin ya yi kokarin gudu suka buge shi, biyu kuwa a can wani dutse suka je suka kama a cikn dajin Maladumba. Su ma aka same su aka buge su sannan aka yi mini waya, shi ne na je na samu ’yan sandan da mafarautar da masu ba da gudunmawar sun yi nasarar buge su. 

barayin su nawa ne?

Su uku ne kuma duk su ukun suka kwace kuma duk aka samo su aka bugo su, kuma da bindigoginsu guda hudu akwai AK47 guda uku da babbar bindiga mai baki biyu guda daya suna da harsasai masu rai guda 210, akwai kuma harsasan babbar bindiga guda shida, akwai kayan yunifom din ’yan sanda da suka kwace a hannun ’yan sandan kwantar da tarzoma. Wadannan barayin sun fi yin tu’annatinsu a jihohin Katsina da Zamfara da kuma Sakkwato, ina zato a can suka samu wannan kaya na ’yan sanda. 

A baya ka yi hasashe kan bazuwar makamai da yawaitar aikata laifuffuka sai ga shi wannan abu ya tabbata me za ka ce?

Eh wajen shekarar 2007 na yi hasashen cewa wadannan barayi in aka yi sake za su fi karfin hukumar. Abin da ya sa na fadi haka, akwai sarakuna da muka samu suna cikin ayyukan masu fashin musamman a kasar Gabar din nan wadansu jami’an tsaro sun san su, kuma akwai shugabannin kungiyoyi. Babban abin da ya fi tsorata ni sai aka samu ’yan siyasa suna amfani da su, wajen siyasa ko amfani da su wajen cire kudin gwamnati, haka kawai sai ka samu dan siyasa ya ce maka ya tubar da barayi, in ba ka mance ba wata shekara an samu haka sun kama dama sun ce gwamnati dubu biyar-biyar take ba su bayan ta tubar da su sai suka zama daga gidan gwamnati suke zuwa su yi mana ta’adi. barawon ya ce dubu biyar-biyar ake biyansu kowane wata, wani mai bai wa Gwamna shawara ya fito ya ce sun kashe musu wajen Naira biliyan daya. Ka ga kasar nan ba ta mahaukata ba ce ba kuma kasar yara ne kanana ba, ba jahilai ba ne ba kuma mutanen da suke cikin duhu ba ne wadanda ba wando a jikinsu. kasa ce ta Musulmi da Kirista kowane da addininsa da shari’arsa, a ce kana shugaba ka dauki kudin al’umma Naira biliyan daya ka je ka bai wa dan ta’adda da yake kashe mutane, ka ga wannan abin tsoro ne, dole za a samu matsala. Cikin hasashen da na yi jami’an gwamnati suna amfani da barayi suna tara su a gindinsu suna kashe mutane bayan in sun kashe kuma su zo su cire kudin gwamnati suna ba su kashi biyar ko goma, don haka barawo ya gane gidan kara ce gwamnatin don haka raini ya shiga, wadansu in an kama su sai a yi waya a fitar da su wadansu kuma a yi fadan addini ko kabilanci, sai ka ga Gwamna ko Kwamishina ya nuna yana bayan kabilarsa. Duk irin wadannan sun taru sun yi yawa ga gwamnatin, in irin wannan yana faruwa dole mutum ya yi hasashen bacin lamarin ga shi kuma babu shari’a. 

Ko in ka gana da gwamnoni kana ba su irin wadannan bayanai?

Kamar gwamnatin PDP da suka shude a da ina fada musu tunda su ne suke jan mutane su saurare su, amma wannan lokaci ba Gwamnan da nake magana da shi in ba Gwamnana na Jihar Bauchi ba. 

Yaya kake ganin tasirin sulhun da ake yi da barayi a jihohin da suka addabi mutane kamar Zamfara da Katsina?

Ai ba ya da wani tasiri kamar yadda na fada a baya, saboda duk mutumin da Allah Ya ba shi mukamin Gwamna ya zama uba a jiha, amma ba zai yiwu kana shugaba kana da Kwamishinan ’Yan sanda da Kwamandan Soji da Daraktan Tsaro na farin kaya da sauran hukumomin tsaro a ce za a shekara biyu ana kashe jama’a a jiharka a karbe musu dukiyarsu ba ka je ka yi musu jaje ba, ba ka je ka yi musu ta’aziyya ba, ba ka mayar musu da kudinsu ba, baicin ka kashe kudin tsaro kana neman barayin nan sai a wayigari wai barayin nan an kawo maka su a gabanka. Ya kamata ka binciki wanda ya kawo maka su in ka san me kake yi a shugabanci. Amma wani ya ce maka ya sans u har wai za a tara mutum 100 zuwa 200 ku yi sulhu ko ka yi musu afuwa kai in zuciyarka da adalci na shugabanci ya kamata ka yi nazari mutumin nan da ya kawo su shi wane ne tukuna? In jami’in tsaro ne ta ina ya san su da bai nuna maka ba, kai kuma sai idonka ya rufe kake daukar kudin gwamnati talakanka da aka kashe wa ’yan uwa yana nan abin da zai ci ma ya rasa, kuma ka dauki makudan kudi ka ce ka bai wa barawo da sunan sulhu ko afuwa wanda wannan barawon ya kashe sojanka ya kashe maka ’yan sanda da talakawan da suka zabe ka ba iyaka. Ya sace mata da yawa wadansu ma ya yi lalata da su, ba ka sa an kamo su an yi musu hukunci ba, sai ka kuma dibar kudi ka ba su ba da ka bi hakkin al’ummarka ba? Ni duk wanda ya yi haka ina ganin ba mutumin kirki ba ne kawai!

In aka samu irin wadannan mutane me ya kamata a yi?

To duk abin da za ka yi ya kamata ka yi aiki da hankalinka da tunaninka domin duk kasar nan kowa na da da ko ’ya’ya. Ka san gidan kowa in ba Allah Ya shirya ba sai ya samu dan da ya fi karfin ubansa, yawanci gidajen akan samu fitnannun yara balle gidajen masu mulki ko masu dukiya. To ’ya’yanka ma sun fi karfinka bare dan wani, dan wanin ma mai kashe mutum, wanda ya fi karfin iyayensa ka ce kai za ka gyara shi.

Abin da ya kamata a fahimta ba wanda y afi Allah Ubangijin da Ya halicce mu muke bauta masa. Kowane mai laifi akwai hukuncin da Allah Ya ce a yi wa mai laifi kan duk abin da ya aikata, amma ka dauko mai aikata miyagun laifuffuka ka ce za ka yi wani zama da shi bayan ikon shari’a yana hannunka, don hakkin kare rayuka da dukiyoyin jama’a na wuyanka, yin sulhu da su ba zai biya hakkin wadanda suka kahe suka kwashe dukiyarsu ba. Kuma ’ya’yansu suna nan kuma jahilai ne kuma sun san wadanda suka kashe musu iyayensu suka kwace dukiyarsu, su ma sai su fada in ba sa’a aka yi ba kuma ko a yau in mutane suka gane mutum yana kashe mutane sai a zo a zauna daji wadansu za su shiga. Yanzu Neja-Delta me ya sa abin ya ki mutuwa da tun tasowarsu an murtsuke su da an yi an gama, yau kusan shekara 20 ana tubar da barayin nan a kasar nan ba nasarar da aka samu. 

Ko akwai wani yanayi da mutum zai iya amfani da barawon da ya tuba?

Bai wuce a yi amfani da mutum biyar ko goma cikinsu ba a kashe saura wadanda suke boye, amma ba zai yiwu a kashe gida a raya miyagu ba. Ya kamata in suka aikata laifufukka a kama duk a hukunta su don ya zamo darasi ga na baya ba a karfafe su ba, su ci gaba da aikata laifi.