Kuskure ne jingina ta’addanci ga Musulunci – Fafaroma

Jagoran Cocin Katolika na Duniya Fafaroma Francis ya ce ba daidai ba ne a yi maganar Musulmi masu tada zaune tsaye, ba tare da yin maganar takwarorinsu Kiristoci mabiya darikar Katolika wadanda su ma suke aikata  hakan ba.Har ila yau, Fafaroman ya yi Allah-wadai da yadda ake jingina addinin Musulunci da ta’addanci, inda ya ce […]

Kuskure ne jingina ta’addanci ga Musulunci – Fafaroma

Jagoran Cocin Katolika na Duniya Fafaroma Francis ya ce ba daidai ba ne a yi maganar Musulmi masu tada zaune tsaye, ba tare da yin maganar takwarorinsu Kiristoci mabiya darikar Katolika wadanda su ma suke aikata  hakan ba.
Har ila yau, Fafaroman ya yi Allah-wadai da yadda ake jingina addinin Musulunci da ta’addanci, inda ya ce “kusan kowane addini yana da wasu gungun tsirarun mutane da suke da tsatsauran kishin addinin”.
Ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi lokacin da manema labarai suka tambaye shi game da yadda ba ya alakanta kalmar “Musuluci” da ta “ta’addanci”, yayin da yake cikin jirgin sama a kan hanyarsa ta koma wa birnin Rome, bayan wata ziyarar ibada da ya kai kasar Poland.
“Kuskure ne jingina addinin Musulunci da ta’addanci. Batun ba haka ba ne kuma ba gaskiya ba ne,” inji shi
Fafaroman ya ziyarci kasar Poland ne tsakanin ranakun 27 zuwa 31 ga watan jiya don bikin Ranar Matasa ta Duniya, wani biki da mutane fiye da miliyan guda suka halarta, kamar yadda kafar yada labarai na Aljazeera ya bayyana.
Kwana guda gabanin ya kammala ziyarsa ne kuma aka kashe wani dattijo limanin darikar Katolika a arewacin kasar Faransa, a wani hari da kungiyar da take ikirarin kafa kasar Musulunci wato IS ta dauki alhakin kai wa.
“Ba na kaunar yin magana a kan tashe-tashe hankula masu danganta da addinin Islama saboda a kullum, idan na duba jaridu, ina cin karo da labaran rikice-rikice a kasar Italiya, kasar da galibin jama’arta Kiristoci ne mabiya darikar Katolika,” inji shi.
Ya ci gaba da cewa: “To idan zan yi magana kan Musulmi masu tada zaune tsaye, kamata ya yi na fara masu tada zaune mabiya darikar Katolika.”
Ya ce kamar yadda ya sha ganawa da limaman addinin Kirista. “Na san yadda suke kaunar zaman lafiya,” inji shi.
Game da kungiyar IS kuma ya ce “kungiya ce ta ta’addanci, amma ba ta wakiltar daukacin mabiya addinin Musulunci.”