Kuskuren taya shugabanni murnar nadinsu
Tsohuwar al’ada ce idan an zabi mutum ko an nada shi a wani mukami mutane su rika fitowa suna taya shi murna ta hanyoyi da daban-daban. Sau da yawa idan wani ya samu mukami za ka ga na kusa da shi suna murna ‘namu ya samu,’ a yi ta shagulgula, wadansu su rika ganganci da […]
Tsohuwar al’ada ce idan an zabi mutum ko an nada shi a wani mukami mutane su rika fitowa suna taya shi murna ta hanyoyi da daban-daban.
Sau da yawa idan wani ya samu mukami za ka ga na kusa da shi suna murna ‘namu ya samu,’ a yi ta shagulgula, wadansu su rika ganganci da ababen hawa, wadansu su shirya liyafa domin taya shi murna, wadansu su tafi gidansa a yi ta bukukuwa, wadansu kuma su rika binsa ofis da sunan sun je taya shi murna.
Akwai shekarar da aka nada kansiloli na riko a wata karamar hukuma a Jihar Kaduna, sai wadansu suka ji an ambaci wani suna a cikin wadanda aka nada din da suke zaton na dan uwansu ne, maimakon su bincika sai kawai suka kama murna, suka nufi gidan wannan bawan Allah suna ta murna, aka yi ta shagali, aka yi dafe-dafen abinci iri-iri, ga abin sha iri-iri, wadannan mutane su shiga, wadansu su shigo. Haka aka yi ta murna da shagulgula, sai daga baya aka fahimci cewa ashe ba wannan mutum ne aka nada ba, wani ne daban.
Wannan yana faruwa ne saboda mutane sun dauki mukami a matsayin ganima, duk wanda aka ba shi mukami maimakon a tausaya masa a taya shi addu’a saboda an dora masa nauyi, sai a rika taya shi murna saboda ana ganin kakarsa ta yanke saka zai samu ‘alheri,’ ba a tunanin ko wannan matsayin da aka ba shi zai zamar masa alheri ko fitina, domin kaya ne mai nauyi aka dora masa, yana iya dankare shi ya zama masa fitina, ko ya kare a gidan yari, ko yana ji yana gani zaman kasar ya gagare shi ya tsallake zuwa wata kasar a matsayin dan gudun hijira, ko kuma mukamin ya kai shi ga rasa ransa baki daya.
Saboda haka kamata ya yi duk lokacin da aka bai wa wani mutum mukami a rika taimaka masa da addu’ar Allah Ya taimaka masa, Ya taya shi riko, Ya sa ya gama lafiya. Idan ya kammala aikinsa ya sauka lafiya to a lokacin ne za a taya shi murna, a yi shagulgula, har da ba shi kyaututtuka domin ya gama aiki ya dawo gida cikin jama’arsa lafiya ba tare da ko kwarzane ba. Wato bai bata wa kansa da zuriyarsa da sauran jama’arsa suna ba, domin ya yi aiki tukuru tsakaninsa da Allah.
Amma a rika taya shugaba murnar samun mukami ba daidai ba ne, a wannan lokacin addu’a yake bukata ba murna ba. Irin wannan taya murnar ya faru kwanan nan lokacin da Shugaba Buhari ya nada ministocin da zai yi aiki da su a wa’adin mulkinsa na biyu, inda shahararren malamin addinin Musuluncin nan Dokta Isa Ali Pantami ya zama Ministan Sadarwa, saboda haka aka rika turuwa ana zuwa taya shi murna, har da malamai, har ma liyafa aka shirya domin taya shi murna. Amma shi da yake ya san cewa babban nauyi ne aka dora masa kuma Allah Zai tambaye shi game da wannan matsayi da Ya ba shi, maimakon ya yi murna lokacin da aka shirya masa liyafar kuka ya kama yi, yana cewa ‘addu’a ya kamata ku taya ni domin in sauke wannan nauyin da aka dora mini.’
Ya kamata shugabanni su sani cewa ba kaunarsu ake yi ba idan an shirya musu liyafa ko aka yi ta gudanar da shagulgula saboda wani mukami da suka samu, addu’a suke bukata domin su kammala aikinsu lafiya. Saboda da zarar sun samu matsala, wadannan mutanen da suke murna su ne kuma za su koma suna yi musu dariya, ba za su ko rika zuwa kusa da su ba.
Su kuma talakawa ya kamata su fahimci cewa ba tsalle da murna da shagulgula za su yi ba idan an nada musu shugaba, addu’a za su rika yi masa da su kansu domin ya gama lafiya kuma ya zama shugaban da zai amfane su, ba wanda zai cutar da su ba. Domin sau da yawa akan samu talakawa su yi murna sosai, har ma wadansu sukan rasa rayukansu saboda samun mukamin wani mutum, amma daga bisani su koma suna kuka saboda mulkin wannan mutum ya zame musu fitina.
Domin haka kuskure ne babba a rika daukar cewa duk wanda aka nada a wani mukami ya samu ganima ne, ba amana ce aka ba shi ba. Saboda a yau an mayar da amana ta zama ganima, mutane sun mayar da mai cin amana abin sha’awa, maimakon su rika kyamar duk wanda aka ba shi mukami ya yi amfani da wannan matsayi nasa ya wawure dukiyar jama’a, sai a mayar da shi wani gwarzo abin sha’awa. Kowa yana kokarin samun kusanci da shi, babu mai fada masa gaskiya.
Babu laifi mutane su yi murna idan an nada musu wani mutum da suke ganin mutumin kirki ne da zai rike musu amana kuma ya fitar da su daga mawuyacin halin da suke ciki, amma kamata ya yi addu’a ta fi yawa fiye da komai.
Allah Ya ba mu ikon gyarawa, Ya kuma ba mu ikon iya bambancewa a tsakanin amana da ganima!