kusoshin jam’iyun adawa sun canza sheka zuwa APC a Oyo
Jagoran jam’iyar APC na kasa, Sanata Bola Ahmed Tinubu ya ce mutuwar jam’iyyun adawa musamman PDP a Jihar Oyo ta zo kusa. Ya fadi haka ne a ranar Asabar da ta gabata a Ibadan, lokacin da yake mika tutar jam’iyyar APC ga wasu jiga-jigan jam’iyyun adawa na PDP da Labour da Accord da suka canza […]
Jagoran jam’iyar APC na kasa, Sanata Bola Ahmed Tinubu ya ce mutuwar jam’iyyun adawa musamman PDP a Jihar Oyo ta zo kusa. Ya fadi haka ne a ranar Asabar da ta gabata a Ibadan, lokacin da yake mika tutar jam’iyyar APC ga wasu jiga-jigan jam’iyyun adawa na PDP da Labour da Accord da suka canza sheka zuwa APC a Jihar Oyo.
Tsohon Gwamnan Jihar Oyo, Otumba Christopher Adebayo Alao Akala shi ne ya karbi tutar APC a madadin tsohon jagora a Majalisar Dattijai, Sanata Teslim Folarin da tsohon Mataimakin Gwamna, Ambasada Taofeek Arapaja da dan Majalisar Wakilai Mista Dokun Odebunmi da tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Oyo Mista Ayodele Adigun da tsohon shugaban Majalisar Dokoki ta Jihar Oyo Asimiyu Alarape da wasu kusoshin jam’iyun adawa da suka yi adabo da jam’iyyun nasu.
An gudanar da gagarumin taron karbar sababbin manbobin na APC ne a babban zauren taro na Mapo da ke tsakiyar birnin Ibadan. An yi taron ne a karkashin shugabancin Sanata Bola Ahmed Tinubu da mai masaukin baki, Gwamnan Jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi da shugaban jam’iyyar APC na Jihar Oyo, Cif Akin Oke. Taron ya samu halartar Gwamnonin jihohin Osun da Ondo da wakilan gwamnonin Legas da Ogun.
Da yake mika tutar APC ga sababbin mambobin, Sanata Bola Tinubu ya nuna farin cikinsa da wadannan kusoshin jam’iyyun adawa da suka gane gaskiya, suka shigo cikin jirgin APC wacce ita ce kadai jam’iyya mai fafutukar tabbatar da dimukradiyya a Najeriya da Afrika. Ya ce, jam’iyyar APC ta zama gandun daji da take karbar kowa a cikinta, inda ya kara da cewa APC ba za ta taba bari wannan dama ta subuce daga hannunta ba, musamman wajen lalubo hanyar hada kawunan jama’a a Jihar Oyo da kasa baki daya. Ya jinjina wa Gwamna Abiola Ajimobi saboda namijin kokarin da ya ce ya yi wajen janyo wadannan fitattun ’yan siyasa zuwa cikin APC. Ya ce canza shekar da wadannan ’yan siyasa suka yi alama ce ta nasarar APC a zabuka masu gabatowa a Jihar Oyo.
Bayan karbar tutar APC, a madadin sauran wadanda suka canza sheka, tsohon Gwamnan Jihar Oyo, Otumba Christopher Adebayo Alao Akala ya ce yanke shawarar komawa APC ne saboda ya hango cewa PDP da sauran jam’iyyun adawa ba su da wata madogara a Jihar Oyo, domin jama’a sun gaji da irin tafiyar da suke yi. dimbin magoya bayan wadannan ’yan siyasa ne suka rufa masu baya zuwa wajen taron na Ibadan.
Birnin Ibadan ya cika makil da ’yan siyasa maza da mata da suka sanya riguna iri daya da tsintsiya a hannayensu, inda suka yi ta kade-kade da raye-raye da wake-wake, domin nuna goyon bayansu ga jam’iyyar APC.