Kusufin rana zai baibaye nahiyoyin Afirka da Turai da Amurka

  Akwai yiwuwar wani irin kusufin rana ya baibaye nahiyoyin Afirka da Turai da Amurka, a ranar Lahadi mai zuwa, musamman ganin cewa wata ya tare wani sashe na gurbin tafiyar rana. Fasalin kwai da duniya ke da shi, shi ya bayyana dalilin da ya sanya daukacin fadin Afirka ta Yamma za tag a kusufin […]

Kusufin rana zai baibaye nahiyoyin Afirka da Turai da Amurka

 

Akwai yiwuwar wani irin kusufin rana ya baibaye nahiyoyin Afirka da Turai da Amurka, a ranar Lahadi mai zuwa, musamman ganin cewa wata ya tare wani sashe na gurbin tafiyar rana. Fasalin kwai da duniya ke da shi, shi ya bayyana dalilin da ya sanya daukacin fadin Afirka ta Yamma za tag a kusufin rana, a yayin da Amurka da Turai za su ga wani sashe na kusufin.
Masana sun bayyana cewa, mutane su guji kallon rana kai tsaye, a lokacin kusufin, sai dai in suna da gilashin ’yan walda, wanda ke da siririyar mahangar ‘pinhole.’
Wannan kusufi, ana sa ran zai fara da karfe 1237 agogon GMT a kan tekun Atilantik, wato da nisan kilomita 330 a Kudu maso Yammacin Laberiya, kamar yadda Cibiyar binciken Sararin Samaniyar Amurka na NASA ya bayyana a shafin yanar sadarwarsa.