Kuza ya bace mana wata biyar da fara aikinsa – Leburori

Daya daga cikin matsalolin da masu hakar ma’adinai dangin kwaranda da kuza kan fuskanta shi ne bacewar ma’adinin bayan wani lokaci da fara aikinsa. Aminiya ta shiga dajin ’Yar Kurciya da ke hanyar Gidan Waya zuwa Godogodo a Karamar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna, wata biyar bayan kawo rahoto kan yadda ake hakar ma’adinan, inda […]

Kuza ya bace mana wata biyar da fara aikinsa – Leburori

Daya daga cikin matsalolin da masu hakar ma’adinai dangin kwaranda da kuza kan fuskanta shi ne bacewar ma’adinin bayan wani lokaci da fara aikinsa.

Aminiya ta shiga dajin ’Yar Kurciya da ke hanyar Gidan Waya zuwa Godogodo a Karamar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna, wata biyar bayan kawo rahoto kan yadda ake hakar ma’adinan, inda ta zanta da shugabannin leburori da dillalai da masu sayar da abinci kan yadda suke murna da bayyanar kuza a dajin da aka yi amanna Turawa sun zauna a wajen fiye da shekara arba’in da suka wuce. Sai dai ta gano yanzu lamarin ya ja baya bayan bacewar ma’adinin daga wurin.

Aminiya ta tarar da dajin babu kowa a cikinsa, maimakon hada-hadar jama’a a wancan karon, sai dai a wani gefe ta ga wadansu ’yan tsirarun mutane a wani karamin daji suna ta faman haka da tone-tone.

Daya daga cikinsu mai suna Zakariyya Saleh wanda ya ce shi ne Ma’ajin Kungiyar Masu Sayen Kuza a Masarautar Godogodo ya bayyana wa Aminiya cewa, “A wancan karon da ka zo muna cikin hada-hada inda hatta mai sayar da abinci ta fada maka bambancin cinikin da take yi kafin da bayan fara wannan aiki, amma yanzu ka ga yadda wurin ya bushe.”

Zakariyya ya ce dama dajin an taba amfani da shi shekaru aru-aru don haka abin da suka samu kamar kala ce, kuma suna fatar sake samun wani wurin da ya fi nan domin kusan yankin gaba daya Allah Ya albarkace shi da ma’adinai iri-iri da suka hada da kuza da tantalaye da kwaranda da sauransu.

Sai ya nuna wa Aminiya wani karamin daji kusa da inda aka yi wancan aikin da aka ce nan ne Turawa ke zubar da kasar da ake tono kuza, inda a wajen ne Aminiya ta ga yadda wadansu mutane ke ta tono kasar don neman duwatsu masu daraja.

Yohanna Danladi mai aikin hakar kuza a dajin ya shaida wa Aminiya cewa sun dawo gefen dajin ne don ci gaba da roro da kala a cikin kasa da duwatsun da ake zubarwa a shekarun da Turawa suka yi aikin kuza don neman dan abin da za su rufa wa kansu asiri.

“Nan kamar bola ce inda Turawa ke zubar da kasar da suka tono bayan sun debi abin da za su diba. Shi ne muke tono da wankewa inda muke samun kadan daga kuza da tantalaye da sauransu muna sayarwa,” inji shi

Ya ce a rana sukan samu kamar buhu guda na dutsen inda suke sayar da shi a kan Naira dubu tara.

Wani matashi mai suna Danjuma Douglas ya ce shi dalibi ne wanda yanzu yana shirin shiga jami’a kuma ya dauki dawainiyar karatunsa ne ta hanyar aikin leburanci a dajin.

“Wadansu kan dauka ko rashin aiki ke sanya mu gudanar da wannan sana’a. Ni ina aiki a nan ne saboda in rufa wa kaina da ’yan uwana asiri maimakon in jawo wa kaina da na dangina abin kunya. Na yi imani da wannan aiki zan ci gaba da daukar nauyin karatuna da yanzu haka na samu gurbin shiga jami’a,” inji shi.

“Idan kana da lafiya kuma kana da karfi, bai kamata ka tozarta rayuwarka ka zauna kana jiran a kawo a ba ka ba, ko ka rika jiran gwamnati ta sama maka aikin yi ba, ko ka jefa kanka cikin munanan ayyuka ba,” inji shi.

Ya yi kira ga gwamnati ta dubi yadda za ta sanya hannu a cikin lamarin don kada a bar matasan yankin cikin zaman banza don wanzuwar zaman lafiya da ci gaban kasa.