kwace kudin sayo makamai: Dangantakar Najeriya da Afirka ta Kudu ta fara tsami
Najeriya ta fusata da kasar Afirk ta Kudu bayan da mahukunta Afirka ta Kudu suka kwace kashi na biyun na kudin sayo makamai don yaki da Boko Haram, inda mahukuntan Najeriya suka musanta cewa an bi hamatacciyar hanya a harka, kuma suka yi gargadin ramako kan jarin Afirka ta Kudu da ke Najeriya.Gargadi na Najeriya […]
Najeriya ta fusata da kasar Afirk ta Kudu bayan da mahukunta Afirka ta Kudu suka kwace kashi na biyun na kudin sayo makamai don yaki da Boko Haram, inda mahukuntan Najeriya suka musanta cewa an bi hamatacciyar hanya a harka, kuma suka yi gargadin ramako kan jarin Afirka ta Kudu da ke Najeriya.
Gargadi na Najeriya ya zo bayan da gwamnatin Afirka ta Kudu ta kwace Dalar Amurka miliyan biyar da dubu 700 9 (kimaninn Naira miliyan 950) na gwamnatin Najeriya da ta tura ta wani banki ga wani kamfanin dillancin makamai da ke Afirka ta Kudu.
Sashin kwace kadarori na Hukumar Gabatar da kararraki ta Afirka ta Kudu ya ce, kudin an shiga da su kasar nan ne do haramtaccen ciniki kamar yadda jaridar kasar City Press ta ruwaito.
kwace wannan kudi shi ne irin sa na biyu cikin mako uku, bayan da mahukuntan kasar suka kwace Dala miliyan 9 da dubu 300, sama da Naira biliyan daya da rabi na tsabar kudin da wasu ’yan Najeriya biyu da wani dan kaar Isra’ila suka dauka don sayo makamai. A lokacin Afirka ta Kudu ta ce lamarin ya keta dokar safarar kudi na kasar
Sai dai a kakkausar martanin da ke nuna dangantaka ta fara tsami a tsakanin kasshen biyu, gwamnatin Najeriya ta musanta cewa harkar ta keta doka, inda ta tunatar da kasar Afirka ta Kudu kan yadda Najeriya ta ba kamfanonin Afirka ta Kudu da suka hada da MTN Da DSTb da sauransu dama su rika gudanar da harkokinsu ba tare da wata matsala ba.
“Muna fata Afirka ta Kudu za ta tuna da wannan mutunci,” inji Mashawarcin Shugaban kasa, Sambo Dasuki a ranar Litinin, inda ya yi alkawarin ganin bayan Boko Haram komai dabarar “masu zagon kasa.”
Dasuki, wanda jaridar ta Afirka ta Kudu ta ruwaito cewa shi ya sanya hannu a badakalar farko, ya tabbatar da lamarin na baya a ranar Litinin da yamma, to amma ya musanta cewa ta haramtacciyar hanya aka kulla cinikin.
“Muna son fadi balo-balo cewa harkar kasuwancin ta gudana a tsakanin halattaccen kamfani da ke Najeriya da wani halattaccen kamfani a Afirka ta Kudu ta hanyar banki,” inji Dasuki wanda ya yi magana ta bakin kakakinsa, Karounwi Adekunle.
“Kuma ana cikin haka ne kamfanin na Afirka ta Kudu ya kasa sayo makaman, kuma ya nemi dawo da kudin. Mene ne rashin halacci a wannan harka da aka yi ta banki,” ya yi tambaya.
Bayanin cinikin na bayan nan ya zo ne bayan mako biyu da kama ’yan Najeriya biyu da dan Isra’ila a lokacin da suka yi kokarin fasa-kwaurin tsabar kudi Dalar Amurka miliyan 9.3 ta filin jirgin sama na Lanseria International Airport da ke Johannesburg a ranar 5 ga Satumba a jirgin shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) Fasto Ayo Oritsejafor wanda ya tashi daga Abuja.
An dauki kudin ne shake a akwatuna uku lamarin da ya jawo ma’aikatan tsaro a filin jirgin Afirka ta Kudu suka sha jinin jikinsu lokacin da na’ura ke auna kayan fasinjoji.
Babban Mai shigar da kara na Afirka ta Kudu ya ce akwai takardar sayen helikwaftoci da wasu makamai da ake shirin yin amfani da su a Najeriya. Kuma an shake wasu bakaken akwatu biyu da dauri 90 na Dalar Amurka bandir din Dala dubu dari-dari da wasu, inda akwa kwace su tare da wasu jakunkunan hannu biyu da suke dauke da dalolin Amurka kamar yadda jaridar City Press ta bayyana.
dan kasar Isra’ila, Eyal Mesika, ne zai iya bude akwatuna.
A karkashin dokokin Afirka ta Kudu, mutumin da zai shiga kasar ko fita daga cikinta an lamunce masa ya yi tafiya da Dala 2,300 ne kacal ko kwatankwacinsa na sauran kudaden kasashen waje.
Labarin badakalar farko ya fusata ’yan Najeriya, musamman da aka gano cewa ya hada da jirgin shiga na Shugaban CAN, Ayo Ortisejafor, wanda na hannun Shugaba Goodluck Jonathan ne, kuma ya yi da’awar an bayar da hayar jirgin ne ga kamfani na uku don haka bai kamata a zarge shi da hannu kan yadda yake tafiyar da ayyukansa ba.
Gwamnati ta ce tana da hannu a badakalar, inda ta ce ta yi haka ne saboda matsuwar da ta yi don sayo makaman saboda ta samu nasara kan yakin da take yi da Boko Haram.
Mahukuntan sojan Najeriya sun ce ko cinikin farko bai a keta ka’ida ba ganin da hannun ofishin Mashawarcin Shugaban kasa a lamarin, kuma ba kowace hark ace da ta shafi sayo makamai ta zamo jama’a sun sani ba.
Harkar ta bayan nan dai an kulla ta ce a tsakanain kamfanin Cerberus Risk Solutions, wanda dillalin makamai ne da ke birnin Cape Town da kamfanin Societe D’Ekuipments Internationaud da aka ce kamfani ne na ’yan Najeriya da ke Abuja.
Jaridar City Press ta ce cinikin ya wargaje ne bayan da kamfanin Cerberus, wanda da farko ya amshi Randi miliyan 60 (kimanin Naira biliyan daya da digo 02) ta asusunsa a bankin Standard Bank, ya yi kokarin bayar da kudin bayan da ya gaza warware matsalar rajistarsa da hukumomin kasar Afirka ta Kudu.
Kamfanin Cerberus a baya an yi masa rajista a matsayin dillali ne da hukumar kula da ma makamai (NCACC), amma rajistara ta kare a Mayun baya,” inji jaridar City Press. Wadda ta kara da cewa: “Takardar izinin kasuwanci da kulla yarjejeniyar harkar makamai na kamfanin sun kare aiki a daidai lokacin. Kamfanin ya nemi a sake yi masa rajista tun a lokacin amma aka bar takardar neman rajistar ba a yi komai kanta ba fiye da wata biyu.”
Majiyoyi sun shaida wa Rapprt cewa Cerberus ya yi kokarin mayar da kudin ga kamfanin na Najeriya, inda hakan ya sa bankin ya sha jinin jikinsa,” inji jaridar. Ta ce nan take ofishin mai shigar da kara ya garzaya Babbar Kotun South Gauteng yana yana neman kwace kudin, sai dai kakakin ofishin Nathi Mncube ya ce babu wata alama ta akwai dangantaka a tsakanin cinikiyyar biyu. Ya ce ana gudanar da bincike kan batutuwan biyu.
Ofishin Dasuki ya tabbatar da gazawar kamfanin na Afirka ta Kudu na samar da makaman tare da yunkurinsa na dawo da kudin.