Kwadayin nama
Wasu Hadejawa ne suka je bikin suna gidan wara Bagwariya, sai ta kawo musu nama, ta ce: “Ga shi dan kadan, amma kan kare ne.” Su a zatonsu, matar tana nufin ‘kadan kankane.’ Ita kuwa tana nufin naman na kan kare ne. Hadejawan nan sai suka ce: “Ba damuwa, ai ba za mu raina ba.” […]
Wasu Hadejawa ne suka je bikin suna gidan wara Bagwariya, sai ta kawo musu nama, ta ce: “Ga shi dan kadan, amma kan kare ne.” Su a zatonsu, matar tana nufin ‘kadan kankane.’ Ita kuwa tana nufin naman na kan kare ne. Hadejawan nan sai suka ce: “Ba damuwa, ai ba za mu raina ba.” Nan suka cinye nama tas, har da sude kwano. Bayan sun gama shi ne take cewa: “Ashe kuna cin kare, ga shi ma karami ne.” Nan take suka gane ashe kare take nufi. Nan suka fara kakari, wai suna son haraswa.”
Daga Maryam Idris Metu, 07038412210