Kwaddibuwa za ta fara amfani da iskar gas din Najeriya
Hukumar Man Fetur ta Najeriya (NNPC) ta bayyana nan da wadansu watanni kasar Kwaddibuwa za ta fara amfani da iskar gas din kasar nan, wanda hakan wani yunkurin da Kwaddibuwa take yi wajen bunkasa wutar lantarkinta. Mai magana da yawun hukumar Ohi Alegbe ne ya bayyana hakan a Abuja a ranar Talata.Masu sharhi a kan […]
Hukumar Man Fetur ta Najeriya (NNPC) ta bayyana nan da wadansu watanni kasar Kwaddibuwa za ta fara amfani da iskar gas din kasar nan, wanda hakan wani yunkurin da Kwaddibuwa take yi wajen bunkasa wutar lantarkinta.
Mai magana da yawun hukumar Ohi Alegbe ne ya bayyana hakan a Abuja a ranar Talata.
Masu sharhi a kan lamurran tattalin arziki sun bayyana wannan mataki da Kwaddibuwa ta dauka zai ba Najeriya damar samun abokiyar hulda ta daban bayan wadda ta saba yi da kasashen Asiya, zai kuma bunkasa tattalin arzikin kasar nan.
Baya ga kasancewar Najeriya kasa ta daya da ke samar da mai a Afirka, kasa ce kuma da ke dimbin iskar gas, kuma daya daga cikin kasashe biyar a duniya da suke samar da iskar gas.