Kwalara da Kyanda sun kashe mutum 252 a Borno

Mutane 10,710 aka ruwaito sun kamu da cutar kyanda.

Kwalara da Kyanda sun kashe mutum 252 a Borno

Babagana Umara Zulum, Gwamnan Jihar Borno.

Rahotanni daga Jihar Borno na cewa kimanin mutane 252 cutar Kwalara da kuma Kyanda suka kashe a jihar daga watan Yuli kawo yanzu.

Jaridar HumAngle ta tattaro wasu bayanai daga Hukumar Lafiya a Matakin Farko ta Jihar Borno da suka nuna cewa kimanin mutane 178 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar kwalara mai haddasa amai da gudawa tun daga watan Yulin wannan shekara.

Hakazalika, an kuma tabbatar da mutuwar mutane 74 bayan kamuwa da cutar kyanda a jihar.

Wasu bayanai da HumAngle ta gani ya nuna cewa, daga cikin mutane 10,710 da aka ruwaito sun kamu da cutar kyanda, ya zuwa yanzu an tabbatar da 140 daga cikinsu kuma fiye da rabin wadanda aka tabbatar sun mutu.

A baya dai HumAngle ta wallafa wani rahoto a cikin watan Satumba inda gwamnatin jihar ta nemi taimakon kasashen waje domin dakile yaduwar cutar kwalara da a wancan lokacin ta yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 43.

Jaridar ta ce akasarin wadanda cututtukan biyu na kyanda da kwalara suka shafa galibi sun kasance a sansanonin ‘yan gudun hijara masu cunkoson jama’a da kuma al’ummomin da suka tsugunar da ‘yan gudun hijirar.

HumAngle ta ruwaito yadda fursunoni da dama a daya daga cikin sansanonin da ake tsare da masu alaka da Boko Haram a Maiduguri suka mutu sakamakon kamuwa da cutar kwalara.