Kwalara ta kashe ƙarin mutum 21 a Legas

An yi hasashen samun ƙaruwar adadin sakamakon bukukuwan Sallar layya da aka yi.

Kwalara ta kashe ƙarin mutum 21 a Legas

Cutar Kwalara da ake fama da annobarta ta kashe ƙarin wasu mutum 21 a Jihar Legas kamar yadda mahukunta suka tabbatar.

Bayanai sun ce adadin waɗanda suka kamu da kwalara a fadin jihar ya ƙaru zuwa mutum 401, inda cutar tafi ƙamari a yankunan Lagos Island da Kosofe da kuma Eti-Osa.

Mai bai wa gwamnan shawara ta musamman kan harkokin kiwon lafiya, Dokta Kemi Ogunyemi ce ta tabbatar da hakan.

Ta bayyana cewar adadin waɗanda suka mutu sakamakon barkewar cutar kwalara ya ƙaru zuwa mutum 21, bayan rahotannin da aka samu a baya da ke cewa mutum 350 ne suka kamu kuma 15 ne suka mutu.

A yau Alhamis, Dokta Ogunyemi ta bayyana hakan lokacin da take ƙarin haske game da annobar, bayan da ta gana da mambobin cibiyar ba da agajin gaggawa a fannin kiwon lafiyar al’ummar Jihar Legas.

Ta ƙara da cewar adadin waɗanda cutar ta hallaka ya ƙaru zuwa mutum 21, karin mutane 6 a kan adadin da aka ba da rahoto a baya.

A cewarta, an yi hasashen samun ƙaruwar adadin sakamakon bukukuwan Sallar layya da aka yi, lamarin da ke janyo cunkoson jama’a a wuri guda.

Sai dai ta ce, ana samun raguwar waɗanda ke kamuwa da cutar a ilahirin kananan hukumomin jihar, musamman ma waɗanda a da aka samu ɓullarta saboda ɗaukar matakai da sanya idanu daga gwamnatin jihar.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos