Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan

Ana nuna damuwa game da yiwuwar ɓarkewar zazzabin dengue a Sudan

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan

Adadin wadanda suka mutu a kasar Sudan sanadiyyar ɓarkewar cutar amai da gudawa da aka fi sani da Kwalara ya kai 348 a cewar ma’aikatar lafiya.

Barkewar cutar ta shafi jihohi tara, inda sama da mutane 11,000 suka kamu da cutar kamar yadda TRT ya ruwaito.

Bugu da ƙari, ana nuna damuwa game da yiwuwar ɓarkewar zazzabin dengue, bayan mutuwar wasu mutane biyu da ake zargin sun kamu da cutar.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da ambaliya sun ta’azzara yaduwar cutar kwalara tun watan Yuni.

Tsarin kiwon lafiya mara inganci a Sudan da yaƙi ya ɗaiɗaita, ya ƙara dagula ƙoƙarin da ake yi na daƙile cututtuka masu yaɗuwa.

A watan Agusta Ministan lafiya na Sudan ya ayyana bullar cutar kwalara bayan shafe makwanni ana ruwan sama kamar da bakin kwarya a kasar da yaki ya daidaita, kamar yadda aka nuna a wani faifan bidiyo da ma’aikatarsa ​​ta fitar.

Haitham Ibrahim ya ce an dauki matakin ne tare da hadin gwiwa da hukumomi a jihar Kassala da ke gabashin kasar, da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya, da kwararru bayan “dakin binciken na lafiyar jama’a ya gano kwayar cutar ta kwalara.”

Kwalara na haifar da gudawa mai tsanani da amai da ciwon jiki, kuma galibi tana faruwa ne ta hanyar ci ko shan abinci ko ruwan da ya gurbata da kwayoyin cutar, a cewar hukumar lafiya ta duniya.

Tana iya haifar da rashin ruwa a jiki mai tsanani, wanda zai iya kai wa ga mutuwa a wasu lokuta a cikin ‘yan sa’o’i.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos