Kwalara ta kashe mutum 23 a Sakkwato

An dora alhakin barkewar cutar kan rashin tsafta.

Kwalara ta kashe mutum 23 a Sakkwato

Hukumomin lafiya a Jihar Sakkwato sun tabbatar da barkewar cutar Kwalara a yankunan Kananan Hukumomi 13 daga cikin 23 na jihar.

A cewar Kwamishinan Lafiyar Jihar Ali Inname, mutane 23 uku ne suka rasa rayukansu daga cikin fiye da mutum 260 da suka kamu da ita kawo yanzu.

Inname ya dora alhakin barkewar cutar kan rashin tsafta, da bahaya a kan tittuna da rashin mayar da hankali wajen kula da muhalli musamman lokutan damuna.

A watan Maris ne Gwamnatin Jihar ta rufe wata makarantar Mata ta GGC Mabera, biyo bayan barkewar cutar amai da gaduwa da ake kira Kwalara.

Cutar Kwalara dai ta ci gaba da yaduwa a jihohi da dama na Najeriya da sanadin rayuka.