Kwalara ta kashe ’yan gudun hijiran Burundi 27

barkewar cutar kwalara a tsibirin Kagunga da ke kasar Tanzaniya ya yi sanadiyyar mutuwar ’yan gudun hijiran kasar Burundi su 33, yayin da dubban jama’a ke ci gaba da tsere wa daga birnin Bujumbura, kamar yadda wani jami’in hukumar kula da yara ta majalisar dinkin Duniya wato UNICEF ya bayyana wa tashar talabijin na Aljazeera, […]

Kwalara ta kashe ’yan gudun hijiran Burundi 27
Kwalara ta kashe ’yan gudun hijiran Burundi 27

barkewar cutar kwalara a tsibirin Kagunga da ke kasar Tanzaniya ya yi sanadiyyar mutuwar ’yan gudun hijiran kasar Burundi su 33, yayin da dubban jama’a ke ci gaba da tsere wa daga birnin Bujumbura, kamar yadda wani jami’in hukumar kula da yara ta majalisar dinkin Duniya wato UNICEF ya bayyana wa tashar talabijin na Aljazeera, jiya Alhamis.

Akalla dai mutum 33 suka rasu. Kuma 27 daga cikinsu an tabbatar da cewa daga ciwon kwalara ne.
Fiye da mutum dubu 100 ne suka tsallaka kasar Tanzaniya mai makwabtaka da kasar ta Burundi tun bayan barkewar rikicin siyasar kasar a karshen watan jiya. Kuma akwai akalla ’yan gudun hijira dubu 70 da suke tsugune a tsibirin Kagunga, inda suke fatan isa sansanin ’yan gudun hijiran garin Nyarugusu.
Akwai dai iyalai da dama da aka raba da sauran ’yan uwansu, inda aka samu yara da dama wadanda suka isa Tanzaniya su kadai.
A shekaranjiya Laraba ne, Shugaban kasar Burundi, Pierre Nkurunziza ya sanar da jinkirta ranar zaben ‘yan majalisar dokoki zuwa nan da kwanaki 10 masu zuwa. Tun farko an dai shirya gudanar da zabukan ne a ranar Talata mai zuwa. Kuma ‘yan adawa da wasu shugabanni a shiyyar gabashin Afirka ne suka bukaci a jinkirta shi domin tabbatar da cewa kura ta lafa.
An dai shafe makonni ana gudanar da zanga-zangar adawa da yunkurin neman wa’adi na uku da Shugaba Nkurunziza ya sanya a gaba, wanda kuma ’yan adawa ke kallon ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar. Kuma fiye da masu zanga-zanga 20 ne suka rasa rayukansu sakamakon arangamar da suka yi da jami’an tsaro.