Kwalara ta yi ajalin mutum 12 a Adamawa
Kwamishinan ya gargaɗi mutane kan kula da tsaftar ruwan da suke sha.
Gwamnatin Jihar Adamawa, ta tabbatar da mutuwar mutum 12, sakamakon kamuwa da cutar amai da gudawa a jihar.
Kwamishinan Lafiya na Jihar, Cif Felix Tangwami ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
- Tsadar Rayuwa: Matar Tinubu ta raba wa ɗalibai littafan rubutu a Nasawara
- An kama matan da suka yi yunƙurin sayar da tagwayen jarirai a Legas
Ya bayyana cewar aƙalla mutum 50 ne ake zargin sun kamu da cutar, yayin da aka tabbatar da mutum 30 na ɗauke da cutar.
Tangwami, ya bayyana cewa, mutum shida sun mutu a asibiti, yayin da wasu shida suka mutu a gida.
Ya zuwa yanzu, mutum 308 ne aka kwantar a asibiti sakamakon kamuwa da cutar Kwalara, inda aka sallami 244 bayan sun samu lafiya.
“A madadin Gwamnan Jiha, ina sanar da ku cewa mun samu sakamakon gwaje-gwajen da muka tura zuwa cibiyar NCDC. Mun tabbatar cewa ana fama da amai da gudawa mai tsanani wato, Kwalara.
“Daga cikin gwaje-gwaje 50 da muka tura zuwa ɗakin gwaji na ƙasa da ke Abuja, 30 sun nuna suna ɗauke da cutar Kwalara.
“Sakamakon ya nuna mutum shida na ɗauke da cutar, sakamakon mutum biyu kuma bai fito ba, sannan an killace mutum 12 kafin fitowar sakamakonsu.
“Saboda haka ina tabbatar wa jama’a cewa cutar Kwalara ta ɓulla a Jihar Adamawa.
“Akwai buƙatar mutane su kula da inda suke zuwa, tsaftar jiki, da kuma ingancin ruwan da suke sha.
“Gwamnati tana aiki tuƙuru tare da ma’aikatan lafiya domin magance wannan cuta, kamar yadda muka yi a baya.
“Muna roƙon jama’a da addu’a da kuma haɗin kan ma’aikatan lafiya wajen ƙara wayar da kan al’umma da shawarwari,” a cewarsa.