Kwalara ta yi ajalin mutum 4, an kwantar da 36 a Yola
Shugaban ya shawarci jama’ar yankunan da su mayar da hankali wajen tsaftace ruwansu da kayan abincinsu.
Shugaban ƙaramar hukumar Yola ta Arewa, Malam Jibrin Ibrahim, ya tabbatar da rasuwar mutum huɗu, tare da kwantar da wasu 36 a asibiti, sakamakon kamuwa da cutar kwalara a Yola.
Ya bayyana haka ne ga manema labarai yayin ziyararsa ga marasa lafiyar da suka kamu da cutar a Cibiyar Daƙile Cututtuka Masu Yaɗuwa (IDC), da ke Yola a ranar Lahadi.
Ibrahim, ya bayyana cewar cutar ɓarke ne a unguwannin Alkalawa, Ajiya, da Limawa da ke ƙaramar hukumar.
Ya ce a lokacin da ya isa ya tarar mutum 20 da suka kamu da cutar, amma adadin ya ƙaru zuwa 40, inda wasu huɗu suka rasu.
Ya ƙara da cewa, yawancin marasa lafiyar sun samu sauƙi kuma suna samun kulawa daga ma’aikatan kiwon lafiya.
Shugaban ya jinjina wa ƙoƙarin gaggawa da ma’aikatan lafiya na Red Cross, da abokan haɗin gwiwa na ƙasa da ƙasa suka yi wajen daƙile yaɗuwar cutar.
Ya danganta ɓarkewar cutar ta hanyar Amfani da ruwan sha mara kyau, wanda ambaliyar ruwa ta haddasa a wasu yankuna.
Ibrahim, ya shawarci jama’a da su ci gaba da tsaftace muhallansu, sannan su riƙa shan ruwa mai tsafta, kuma su ke wanke kayan lambu da ’ya’yan itatuwa yadda ya kamata don daƙile yaɗuwar cutar.