Kwale-kwale ya kife da fasinjoji 200 a Kogi

Ana fargabar cewa wani kwale-kwale ɗauke da fasinjoji fiye da 200 ya yi hatsari a tekun Neja da ya ratsa tsakanin ƙauyukan Dambo zuwa Ebuchi a Jihar Kogi. Kifewar kwale-kwalen wadda ta auku a wannan Juma’ar ta yi ajalin fasinjoji da dama wanda galibinsu mata ne. An kuɓutar da ’yar shekara 4 daga hannun mai […]

Kwale-kwale ya kife da fasinjoji 200 a Kogi

Ana fargabar cewa wani kwale-kwale ɗauke da fasinjoji fiye da 200 ya yi hatsari a tekun Neja da ya ratsa tsakanin ƙauyukan Dambo zuwa Ebuchi a Jihar Kogi.

Kifewar kwale-kwalen wadda ta auku a wannan Juma’ar ta yi ajalin fasinjoji da dama wanda galibinsu mata ne.

A cewar shaidun gani da ido, kwale-kwalen mallakin wani mai suna Musa Dangana na ɗauke da fiye da fasinjoji 200, ciki har da mata ‘yan kasuwa da leburorin d ake aiki a gonaki, a kan hanyar ta zuwa kasuwar Kdake ci mako-mako a Jihar Neja.

Sun bayyana cewa an samu wannan mummunan akasi ne bayan da kwale-kwalen wanda bai daɗe da soma jigilar ba ya lalace a tsakiyar ruwa.

Wakilinmu ya ruwaito cewa kawo yanzu an tsamo gawawwaki takwas, yayin da ake ci gaba da aikin lalube da ceto domin gano ragowar fasinjojin.

Wata majiya daga Hukumar Kula da Hanyoyin Ruwa (NIWA) ta tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ba ta yi ƙarin haske ba tana mai cewa za su fitar da sanarwa a hukumance da zarar sun kammala bincike.

Aminiya ta yi ƙoƙarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Kogi, SP Williams Aya, amma ba ta yi nasara ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

A farkon watan Oktoban da ya gabata ne aka samu kwatankwacin hatsarin nan a kwale-kwale a rafin Muwo Gbajibo da Ƙaramar Hukumar Mokwa a jihar ta Neja, inda mutane da dama suka rasu.