Kwale-kwale ya kife da mata da yara 40 a Jigawa
An na ci gaba da tattara sahihan bayanai domin tantance adadin mutanen da suka mutu da kuma waɗanda aka ceto.
An tabbatar da mutuwar mutum guda, yayin da ake ci gaba da neman wasu fasinjoji bayan wani kwale-kwale da ke ɗauke da mata da yara kimanin 40 ya kife a yankin Malamawa ta ’Yan Dutse da ke Ƙaramar Hukumar Ringim a Jihar Jigawa.
Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, inda ya jefa al’ummar yankin cikin alhini da fargaba, yayin da jami’an tsaro, masu aikin ceto da kuma mazauna yankin suka bazama domin ceto waɗanda hatsarin ya rutsa da su.
- Gidaje da gonaki sun lalace sakamakon mamakon ruwan sama a Filato
- Sifaniya ta lashe Kofin Duniya na 2026
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa, SP Shi’isu Lawan Adam, ya tabbatar da aukuwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Lahadi.
Ya ce rahotannin farko sun nuna cewa kwale-kwalen na ɗauke ne da mata da yara kusan 40 lokacin da ya kife.
A cewarsa, an riga an gano gawa guda, yayin da ake ci gaba da aikin ceto da kuma neman sauran fasinjojin da har yanzu ba a gano inda suke ba.
“Jami’anmu tare da masu aikin ceto suna ci gaba da gudanar da bincike da neman waɗanda suka ɓace domin tabbatar da an gano kowa,” in ji kakakin ’yan sandan.
Haka kuma, Masarautar Ringim ta tabbatar da faruwar hatsarin cikin wata sanarwa, inda ta bayyana cewa lamarin ya yi sanadin asarar rayuka.
Sai dai ta ce ana ci gaba da tattara sahihan bayanai domin tantance adadin mutanen da suka mutu da kuma waɗanda aka ceto.
Majiyoyi daga yankin sun ce da zarar kwale-kwalen ya kife, matasa da mazauna garuruwan da ke kusa sukan yi gaggawar shiga aikin ceto tare da jami’an tsaro, yayin da iyalan fasinjojin suka cika bakin ruwan cikin jimami suna jiran samun labarin ’yan uwansu.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomi ba su fitar da haƙiƙanin adadin waɗanda suka tsira ko kuma waɗanda suka rasa rayukansu ba, domin ana ci gaba da aikin ceto da kuma bincike kan musabbabin hatsarin.
A halin yanzu, jami’an tsaro sun tabbatar da cewa za su ci gaba da aikin neman waɗanda suka ɓace, tare da gudanar da bincike domin gano ainihin musabbabin kifewar kwale-kwalen.
Hatsarin kwale-kwale na ci gaba da zama ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da ake fuskanta a yankunan da ke amfani da hanyoyin ruwa, musamman a lokacin damina.
Masana da masu ruwa da tsaki sun sha yin kira ga masu kwale-kwale da fasinjoji da su riƙa amfani da rigunan kariya (life jackets), sannan a daina ɗaukan fasinjoji fiye da ƙarfin kwale-kwale, tare da bin ƙa’idojin sufuri ta ruwa domin rage yawaitar irin waɗannan munanan haɗura.

