Kwale-kwale ya kife da matasa 20 a Jigawa

Wani Kwale-kwale ya kife da wadansu samari 20 a kauyan Darai da ke karamar Hukumar Jahun a Jihar Jigawa inda dukkansu suka mutu a hadarin.An ce jirgin ya samu tangarda ne a lokacin da direban jirgin ke kan hanyarsa ta zuwa kauyen dauke da matasan 20 wadanda suke dawowa daga kasuwa wasu kuma daga gona.Mutanen […]

Kwale-kwale ya kife da matasa 20 a Jigawa
Kwale-kwale ya kife da matasa 20 a Jigawa

Wani Kwale-kwale ya kife da wadansu samari 20 a kauyan Darai da ke karamar Hukumar Jahun a Jihar Jigawa inda dukkansu suka mutu a hadarin.
An ce jirgin ya samu tangarda ne a lokacin da direban jirgin ke kan hanyarsa ta zuwa kauyen dauke da matasan 20 wadanda suke dawowa daga kasuwa wasu kuma daga gona.
Mutanen yankin da suka kware wajan fito sun yi kokari sun gano gawarwakin matasan 20 kuma tuni aka yi musu jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Badaru Abubakar ya ziyarci yankin na Darai Doro da Gilima, inda ya jajanta musu kan wannan hadari.
Gwamna Badaru ya nuna matukar damuwa kan rasuwar matasan kuma ya shawarci matuka kwale- kwale a yankin su yi hattara tare da bin dokokin tuki domin kiyaye rayuwar jama’a.
Wata majiya a kauyen ta ce an ceto mutum uku da ransu, yayin da masunta suka ci gaba da laluben wasu mutanen a ruwa. Ya ce mutane da hadarin ya shafa sun kai 30, ciki har da manoman da suke dawowa daga cin barkono.
Kakakin Rundunar ’Yan sanda ta Jihar Jigawa DSP Audu Jinjiri ya ce mutum shida ne suka rasu kuma an ceto mutum shida. Ya ce mutum 12 ne a cikin kwale-kwalen ba mutun 20 ko 30 da wasu suke fada ba.
DSP Jinjiri ya ce matuka kwale-kwalen su biyu sun taimaka wajen ceton yaran da jirgin ya kife da su masu shekaru daga tara zuwa 15 da suka fito kauyen Darai za su je kauyen Gilima.