Kwale-kwale ya kife da mutum 300 a tsakiyar kogin Kwango
18 daga fasinjojin cikin jirgin sun mutu
Wani kwale-kwale da ke dauke da fasinjoji 300 ya karye a tsakiyar ruwa sannan ya kife da su a yammacin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango.
Mutum 18 daga cikin fasinjojin ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon hatsarin babban kwale-kwalen.
Kwale-kwalen dai ya karye gida biyu ne bayan da isa tsakiyar kogin Lukenie.
- Sojoji sun kama jirgin ruwa makare da lita 350,000 na man dizel din sata
- A shirye Rasha take ta taimaka wa abokan gabar kasashen Yamma – Putin
Jami’an ’yan sandan kasar sun ce mafi yawan mutanen da ke cikin jirgin kananan ma’aikatan gwamnati ne.
Shugaban ’yan sandan yankin Oshwe da ke lardin Mai-Ndombe inda lamarin ya faru wato Martin Nakweti ya ce, a yanzu jami’an bayar da agajin gaggawa da masunta na gargajiya na ci gaba da aikin ceto ragowar mutanen da suka nutse a ruwa.
Sai dai ya ce har yanzu gawarwaki 18 kawai aka iya tsamowa.
Kwale-kwale dai babbar hanyar sufuri ce ta jama’ar yankin mafi sauki, kuma hakan ne ya sa ake yawan samun asarar rayuka sanadin hatsari ko kuma karyewar kanana da manyan kwale-kwalen ke yi lokaci zuwa lokaci.
Shugaban wata kungiyar fafutukar kare hakkin jama’a na yankin, Bovic Ngampenga ya ce jirgin ya karye ne saboda dama ya tsufa, kuma an yi masa lodin mutane da kayan da suka wuce kima.
Bovic ya kuma ce a ka’ida, bai ma kamata a ce har yanzu wannan kwale-kwale na aiki ba. (RFI)