Kwale-kwale ya nutse da mutum 70 a Kwara
Mun dauke lamarin a matsayin mukaddari ne daga Allah.
Akalla mutum 15 sun riga mu gidan gaskiya yayin da wani kwale-kwale ya nutse da mutane 70 a kauyen Boti na Karamar Hukumar Patigi da ke Jihar Kwara.
Wani mazaunin yankin da lamari ya faru, Malam Muhammad Sani ya ce jirgin kwale-kwalen ya dauko wasu ‘yan biki ne daga kauyen na Boti.
Amma da suka je tsakiyar ruwan sai jirgin ya fashe. Malam Sani ya ce “ya zuwa yanzu an sami gawarwakin mutane 15 kuma ana ci gaba da neman sauran har yanzu’’
Muryar Amurka ta ruwaito babbar jami’ar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), mai kula da jihohin Kwara da Neja, Hajiya Zainab Sa’idu na cewa ba ta riga ta sami labarin ba amma za ta tuntubi jami’anta da ke jihar ta Kwara.
Shugaban Karamar Hukumar Patigi, Muhammad Ibrahim Liman ya tabbatar da aukuwar lamarin, amma ya ce suna gudanar da bincike domin gano dalilin fashewar kwale-kwalen.
Idris Kpata Muhammad, Sakataren Karamar Hukumar Patigi ya ce lamarin ya tayar da hankalinsu matuka, amma kuma sun dauke shi a matsayin mukaddari ne daga Allah.
A baya an sha samun hadurran jiragen ruwan kwale-kwale a cikin kogunan Kwara da Neja da su ka yi sanadiyyar asarar rayukan jama’a, al’amarin da masu fashin baki suka ce yana bukatar daukar matakin shawo kan wannan matsala.