Kwalejin aikin gona ta Gombe ta koyar da mata 250 dabarun sarrafa kayan gona
Kwalejin aikin gona da tsirrai ta gwamnatin tarayya dake Gombe “Federal Collage of Horticulture” Dadin-Kowa ta koyar da mata 250 daga sassa daban-daban a fadin kasar nan yadda za a sarrafa kayan gona da adana shi. Da take jawabi a wajen bude shirin, shugabar kwalejin, Farfesa Fatima BJ Sawa, ta ce shirin na gwamnatin tarayya […]
Kwalejin aikin gona da tsirrai ta gwamnatin tarayya dake Gombe “Federal Collage of Horticulture” Dadin-Kowa ta koyar da mata 250 daga sassa daban-daban a fadin kasar nan yadda za a sarrafa kayan gona da adana shi.
Da take jawabi a wajen bude shirin, shugabar kwalejin, Farfesa Fatima BJ Sawa, ta ce shirin na gwamnatin tarayya ne tare da hadin gwiwar ma’aikatar aikin gona ta tarayya. Ta ce wannan shirin Sanatoci da ‘yan majalisun tarayya ne suka turo jama’arsu da za a koyawa yadda ake sarrafa kayan gonar dan samun hanyar dogaro da kai.
Ta kara da cewar sakamakon tabarbarewar tattalin arzikin kasa yasa ake son samar wa matasa aikin yi na sarrafa kayayyakin albakatun gona da adana su musamman kayan lambu ta hanyar da ba za su lalace ba. Kana kuma ta godewa gwamnatin tarayya da ma’aikatar aikin gona ta tarayya bisa bullo da wannan shiri. “Kwalejin na bada horo a bangarori daban-daban kama daga koyar da kula da fulawowi da kiwon dabbobi da yadda ake noma da sauran su. A baya kwalejin cikin wadanda suka koyawa shirin har da wata ‘Yar Jihar Bayelsa wacce ta koyi yadda ake yin Ketchup da tumaturin gwangwami da Juice din kankana da yanzu take samun kudi da sana’ar” in ji ta.
Sannan ta bukaci wadanda suka koyi sana’ar da cewa kar su rike ta a tsakaninsu su kadai, su koyar da wasu ma su amfana.
Shi ma babban jami’in ‘yan sanda na garin Dadin Kowa, DSP Sani Yaro, shawartar matan ya yi da cewa su tsaya su koyi abinda aka turo su dan amfanin kansu. Haka zalika shi ma Sarkin Yamaltu, DSP Hassan Usman Jonga, kira ya yi ga gwamnatin tarayya da cewa a samar wa da wannan kwalejin injuna na musamman da za su taimaka wajen sarrafa kayayyakin.
Wasu daga mahalarta taron da wakilinmu ya zanta da su, Adeeze Chisom daga Jihar Abia da Aisha Umar da Martha S Musa daga Gombe, sun bayyana jin dadinsu bisa kasancewarsu cikin wadanda za su ci moriyar wannan shiri. Sai kuma suka godewa shugabaninsu da da dukkan wadanda suka shirya taron.