Kwalejin Kimiyya ta Jihar Nasarawa za ta kafa gidan rediyo

Kwalejin Kimiyya da kere-kere ta Jihar Nasarawa da ke Lafiya za ta kafa gidan rediyonta nan ba da jimawa ba. Shugaban Kwalejin Farfesa Silas Gyar ne ya sanar da haka a lokacin da yake jawabi a wajen bikin rantsar da sababbin daliban kwalejin na shekarar 2015 da 2016 da ya gudana a filin taron makarantar. […]

Kwalejin Kimiyya ta Jihar Nasarawa za ta kafa gidan rediyo
Kwalejin Kimiyya ta Jihar Nasarawa za ta kafa gidan rediyo

Kwalejin Kimiyya da kere-kere ta Jihar Nasarawa da ke Lafiya za ta kafa gidan rediyonta nan ba da jimawa ba.
Shugaban Kwalejin Farfesa Silas Gyar ne ya sanar da haka a lokacin da yake jawabi a wajen bikin rantsar da sababbin daliban kwalejin na shekarar 2015 da 2016 da ya gudana a filin taron makarantar.
Shugaban ya ce a kokarin hukumar gudanarwar kwalejin na ganin ta bunkasa tare da daukaka harkokin karatu ne ya sa suka dauki matakin kafa gidan rediyo na makarantar, inda ya ce tuni aka samu filin gina gidan rediyon.
Ya ce da zarar gidan rediyon ya kama aiki za a samu ci gaba sosai a harkokin karatu kuma makarantar za ta yi suna a ciki da wajen jihar.
Ya taya sababbin daliban murnar nasara da damar da suka samu na soma karatu a kwalejin, inda ya bukaci su kasance dalibai nagari ta hanyar kiyaye dokokin makarantar da guje wa shiga kungiyoyin asiri. Har ila yau ya yi kira ga malaman makarantar su ci gaba da gudanar da aikinsu cikin mutunci da sadaukarwa kamar yadda suka saba don dorewar kyakkyawan suna da makaranta take da shi.
Farfesa Gyar ya jinjina wa Gwamnan Jihar Umaru Tanko Al-Makura kan gagarumar gudunmawar da yake bayar wajen ci gaban makarantar musamman sababbin dakunan kwanan dalibai da sauransu.
 Sababbin dalibai 2,107 ne suka samu gurbin karatun karama da babbar diploma a kwalejin a bana.