Kwalejin Kimiyyar Lafiya ta Musulmi da ke Funtuwa cikin shekara 20
A ranar Laraba 26 ga watan Disamban bara ne, Kwalejin Kimiya da Fasahar Lafiya ta Musulmi da ke garin Funtuwa a Jihar Katsina a karon farko cikin kusan shekara 20 da kafuwarta, ta yi bikin yaye dalibanta kusan 3,000, a harabar makarantar ta dindindin a garin na Funtuwa tare da kaddamar da asusun neman taimakon […]
A ranar Laraba 26 ga watan Disamban bara ne, Kwalejin Kimiya da Fasahar Lafiya ta Musulmi da ke garin Funtuwa a Jihar Katsina a karon farko cikin kusan shekara 20 da kafuwarta, ta yi bikin yaye dalibanta kusan 3,000, a harabar makarantar ta dindindin a garin na Funtuwa tare da kaddamar da asusun neman taimakon Naira miliyan 350, don gina makarantun koyon aikin jinya da na ungozoma. Mai girma Gwaman Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari na cikin manyan kasar nan da suka halarci taron. Yayin da Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya jagoranci sarkunan Kano Malam Muhammadu Sanusi II da na Birnin Gwari Malam Zubairu Jibril Maigwari da Sarkin Lere Alhaji Garba Muhammad da Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal wanda ya samu wakilcin Kwamishinan Ilimi na jihar suka halarta. A bangaren manyan ’yan kasuwa akwai Alhaji Sadik Aminu Dantata wanda ya wakilci mahaifinsu Alhaji Aminu Alhassan Dantata da Alhaji Umaru Mutallab, wanda dan asalin garin na Funtuwa ne.
Makasudin taron kamar yadda na fadi shi ne yaye daliban da suka yi karatu a kwalejin da kuma kaddamar da asusun neman taimako don gina makarantun aikin jinya da ungozoma. An tara sama da Naira miliyan 60, inda Alhaji Lawal Garba ya ba da Naira miliyan 50, yayin da gwamnatin Jihar Sakkwato ta sha alwashin ba da Naira miliyan 10. Gwamnatin Jihar Katsina ta yi alkawarin yin wasu gine-gine bayan tattaunawa da shugabannin kwalejin, shi ma dan Majaisar Dattawa mai wakiltar Katsina ta Kudu Sanata Abu Ibrahim irin alkawarin da gwamnatin ta yi shi ma ya yi ta zai yi gine-gine bayan tattaunawa da shugabannin kwalejin. Dan Majalisar Wakilai na Mazabar Funtuwa da Dandume Alhaji Muntari Dandutse alkawari ya yi wa kwalejen cewa su ’yan Majalisar Wakilai daga jihohin Arewa maso Yamma za su sanya ayyukan mazabu na Naira miliyan 100, da za a yi wa kwalejin a kasafin kudin bana (alkawain na sa ya sa shakku a zukatan jama’ar da su ke wajen taron, bisa ga yanayin zabubbukan da za a yi bana). Tun a farkon bara Alhaji Aminu Dantata a tashi daya ya ba kwalejin gudunmawar Naira miliyan 20, wadanda da su aka fara ginin kwalejin ta ungozoma. Rashin ganin babban mai kaddamarwa Alhaji Auwalu Abdullahi Rano ko wakilinsa, duk an ce ya amince zai halarta har ya ba da hotonsa aka buga a cikin littafin shirye-shiryen bikin an ce bai yi wa jama’a da dama dadi ba.
An kuma nada Mai alfarma Sarkin Musulmi Babban Uban Kwalejin, sannan aka ba shi kyautatar gimamawa shi da wadansu fitattun mutane shida bisa gudunmawar da suke ba kwalejin wadanda suka hada da masu martaba sarakunan Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman da na Daura Alhaji Faruk Umar Faruk da Alhaji Aminu Dantata da tsohon Gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau da marigayi Alhaji Bala Abdullahi Funtuwa da marigayi Alhaji Ma’azu Isah Funtuwa. Kazalika an ba da kyaututuka ga malamai da daliban da suka yi fice a karatu da koyarwa.
Mai karatu bari in dawo da kai kan abin da ya sa na ba makalar ta yau kanun da ke sama, bai wuce irin yadda na ga gagarumar nasarorin da kwalejin ta samu a cikin wadannan shekaru kusan 20 da kafuwarta ba. Tarihi ya tabbatar da cewa wadansu matasa na Kungiyar Dalibai Musulmi na kananan hukumomin Malumfashi da Funtuwa ne suka taru suka yi nazari a kan rashin irin wannan kwaleji a Arewa da Jihar Katsina duk da irin tsananin bukatar da ake da ita na samunta, don haka suka yanke shawarar kafa kwalejin a1999. Da farko ta fara da dalibai 20 da kuma kwas din Lafiyar Al’umma a matsayin satifiket. In takaice maka labari maganar da ake kwalejin na da tsangayar karatu har guda biyar kamar haka: Lafiyar Al’umma da ta Fasaha da Lafiyar Hakori da ta Tafiyar da Harkokin Bayanai kan Kiwon Lafiya da ta Gyaran Na’urorin Kiwon Lafiya da ta Tsabtar Muhalli, inda suke gudanar da kwasa-kwasai tara, don samun shaidar satifiket da karama da babbar diploma, baya ga kwararrun malamai da na’urori da kayayyakin gwaje-gwaje na zamani da ingantaccen yanayi na koyo da koyarwa da take da su.
Shugaban Kwalejin Alhaji Umar Aminu Imam, a jawabinsa ya ce shekara biyar a jeri daliban kwalejin a Tsangayar Lafiyar Al’umma su suke zuwa na daya (100 cikin 100), a jarrabawar kasa. Haka daliban Tsangayar Lafiyar hakora su suka samu irin wannan nasara ta kasa shekara biyu a jere, wato 2017 da 2018.
Shi kansa Mai alfarma Sarkin Musulmi da yake jawabi, cewa ya yi ci gaban da kwalejin ta samu a cikin ’yan shekarun nan sun kayatar da shi, kasancewar shekarun baya da ya ziyarci kwalejin da bana da ya sake dawowa, ya ga nasarori da dama da suka zama abin a yaba. A kan asusun neman taimakon ginin makarantun biyu da aka kaddamar, Mai alfarma Sarkin Musulmi da kansa ya rika kirawo masu kaddamarwa daya-bayan-daya a gaban taron, kowa na fadin abin da ya yi alkawarin bayarwa. Bayan kiran da ya yi ga dukan gwamnonin jihohin Arewa 19, su hanzarta kawo gudunmawarsu ga kwalejin, ya kuma sha alwashin yin dukan mai yiwuwa wajen ganin kwalejin ta cimma dukan burin da ta sa a gaba.
Domin tabbatar da abubuwan da ya yi niyya, Mai alfarma Sarkin Musulmi ya kara wadansu sarakunan Arewa cikin kwamitinsa na iyayen kwalejin, da suka hada da masu martaba Sarkin Gwandu da na Kano da na Katsina daga shiyyar Arewa maso Yamma, daga shiyyar Arewa maso Gabas kuwa ya kawo sunayen Shehun Borno da Sarkin Bauchi, daga shiyyar Arewa ta Tsakiya kuwa masu martaba Etsun Nupe da Sarkin Keffi, Mai alfarma Sarkin Musulmi ya sa cikin kwamitin nasa.
Gaskiyar magana nasarorin da kwalejin ta samu a zamanta na kwaleji irinta mallakar al’ummar Musulmi sai wanda ya gani kuma wani abin a yaba ne tare da yaba wa ’yan Kwamitin Amintattun Kwalejin da ke karkashin jagorancin Sarkin Maska Hakimin Funtuwa Alhaji Sambo Idris Sambo da kuma malaman kwalejin karkashin jagorancin shugaban Kwalejin Alhaji Umar Aminu Imam da ma ’ya’yan Kungiyar Dalibai Musulmi ta Kasa reshen kanannan hukumomin Malumfashi da Funtuwa da suka fara assasa wannan aikin alheri, yau shekaru kusan 20. Ba abin da kuma ya kawo wannan nasara sai kamanta gaskiya da rikon amana, kuma hakan na nuni da cewa muddin jama’a suka sa niyyar alheri a cikin zukatansu, to, kuwa Allah Zai kama musu ta inda ba su tsammani.