Kwalejin Koyon Jinya ta Jihar Kaduna ta yi bikin yaye dalibai

Kwalejin Koyon Aikin Jinya da Unguwar Zoma ta Jihar Kaduna da ke Kafanchan ta yi bikin karrama fitattun daliban da suka nuna kwazo, cikin wadanda ta yaye tun daga 2010 zuwa 2017, tare da karrama wasu fitattun mutane da suka ba da gudunmowarsu wajen ci gaban makarantar. A lokacin da yake jawabi a wajen taron, […]

Kwalejin Koyon Jinya ta Jihar Kaduna ta yi bikin yaye dalibai

Kwalejin Koyon Aikin Jinya da Unguwar Zoma ta Jihar Kaduna da ke Kafanchan ta yi bikin karrama fitattun daliban da suka nuna kwazo, cikin wadanda ta yaye tun daga 2010 zuwa 2017, tare da karrama wasu fitattun mutane da suka ba da gudunmowarsu wajen ci gaban makarantar.

A lokacin da yake jawabi a wajen taron, Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmed El-Rufa’i, wanda Babban-Sakatare a Ma’aikatar Lafiya, Alhaji Muhammad Mahmud Shu’aibu ya wakilta; ya bayyana cewa sha’anin inganta kiwon lafiyar jama’a na daya daga cikin batutuwan da gwamnatinsa ta fi bai wa fifiko a jihar, ta yadda zuwa yanzu gwamnatinsa ta kaddamar da manyan ayyuka da su kunshi gyara da kuma gina kananan asibitoci da ke kananan hukumomin jihar.

Ya jinjina wa malaman makarantar da suka sadaukar da lokacinsu wajen karantar da daliban, sannan a karshe ya yi alkawarin ci gaba da tallafa wa makarantar da dukkanin abin da ya kamata.

Tunda farko, a lokacin da take gabatar da jawabinta, Shugabar makarantar, Misis Serah Adamu Baba ta bayyana cewa wannan biki na hadin gwiwa shi ne irinsa na hudu da ake yaye dalibai 988 tun bayan wanda aka gudanar a watan Afrilun 2009.

Ta kuma gabatar wa gwamnati korafinta da ya kunshi karancin malamai a makarantar, inda ta bayyana cewa makarantar na bukatar karin malamai da ma’aikata guda 31.

A lokacin da yake gabatar da nasa jawabin a matsayinsa na shugaban taro, dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Kudancin Kaduna, Sanata danjuma Tella Laah, ya mika godiyarsa ga duk wadanda suka halarci taron sannan ya yi kira ga gwamnati da sauran hukumomin da abin ya shafa da su taimaka wajen daukaka darajar makarantar ta yadda za ta rika bayar da takardar digiri a fannin kiwon lafiya da unguwar zoma.

Daga cikin wadanda aka karrama akwai Malam Mustafa Jumare Zariya da Madam Cecilia Musa sai kuma Gwamna El-Rufa’i.