Kwalliya a cikin mintuna kalilan

Gaskiya idan ana zancen kwalliya, kayan kwalliya mai tsada ne ya fi dacewa da kowace fuska. Yana da kyau a zabi launin jambaki da ya dace da baki. Ba a cika son maka kowane irin launin jambaki ba. Haka kuma hodar da ta dace da fata da kuma irin launin kwallin da za a gyara […]

Kwalliya a cikin mintuna kalilan

Gaskiya idan ana zancen kwalliya, kayan kwalliya mai tsada ne ya fi dacewa da kowace fuska. Yana da kyau a zabi launin jambaki da ya dace da baki. Ba a cika son maka kowane irin launin jambaki ba. Haka kuma hodar da ta dace da fata da kuma irin launin kwallin da za a gyara gira da shi da sauransu. A yau na kawo muku yadda za a yi kwalliya a cikin mintuna kalilan ba tare da bata lokaci ba.

 

• Jan launi ya fi dacewa da kowace irin baki don haka, idan za a zabi launin jambaki, a zabi mai launin ja. Sannan kuma ina son a san cewa, jan launin ma ya bambanta. Idan ke baka ce, sai ki zabi ja amma ba mai haske sosai ba. Domin fitar da kwalliyarki.

 

• Kada a manta irin ‘eye shadow’ da za a shafa a kan fatar ido. Ya kamata launin ya kasance ya dace da launi kayan da za a sanya bayan an gama kwalliya.

 

• Idan za a shafa hoda, ya kamata a san wani irin fatar da ake da ita. Idan ke mai gautsin fata ce, sai ki samu hoda mai maiko (fandesho) wadda ta dace da launin fatarki. In ba ki da gaustin fata, sai ki shafa hoda haka wadda ta dace da fatarki.

 

• Adon gira: Launi mai ruwan kasa ya fi dacewa da kowace irin fata. Amma idan ke baka sosai ce za ki iya amfani da gazal baki domin fitar da kyan girarki. Idan kuwa ke ruwan tarwada ce ko fara, za ki iya amfani da gazal mai launin ruwan kasa a gira.

 

• Kayan sawa: Yana da kyau a gane irin launin kayan da ya dace da kowace irin fata; idan ke baka ce sai ki yawaita amfani da kaya wadanda launinsu na da haske. Haka zalika idan ke fara ce sanya kaya wadanda launinsu na da duhu ya fi dacewa.