Kwalliya da Tuffa
Shan Tuffa daya a rana na korar da cututtuka da dama, kuma yawan shanta na rage tsufa da shekaru. Idan ana son sayen man rage shekaru ko tsufa, ba sai an kashe kudi masu yawa ba. Sai a rinka shan tuffa. Yin hakan na rage tsufan jiki da na fuska. Tuffa na dauke da sinadaren […]
Shan Tuffa daya a rana na korar da cututtuka da dama, kuma yawan shanta na rage tsufa da shekaru. Idan ana son sayen man rage shekaru ko tsufa, ba sai an kashe kudi masu yawa ba. Sai a rinka shan tuffa. Yin hakan na rage tsufan jiki da na fuska. Tuffa na dauke da sinadaren bitamin C da A. A yau na kawo muku yadda za a yi amfani da tuffa a fuska domin rage tsufan fuska da jiki.
•Tuffa da zuma : A markada ko a jajjaga tuffa sannan sai a sanya zuma cokali biyu, sannan a kwaba da kyau. Sai a wanke fuska da sabulu kafin a shafa kwabin da aka yi. Sai a wanke bayan mintuna 30. Yawan amfani da wannan hadin, na sanya hasken fata.
• Ayaba da Tuffa: Ayaba na dauke da sinadarin gyaran fata da kuma na bitamin A da B da kuma C. Yin amfani da ita a fata mai gautsi na gyara fata. A kwaba ayaba bayan an bareta, sai a hadata da markadaddiyar tuffa sai a kwaba da dama kafin a shafa a fuska. Za a iya sanyawa da zuma ko kindirmo kadan a wannan hadin. A shafa a fuska na tsawon mintuna 30 kafin a wanke.
• Lemun tsami da tuffa da kindirmo: Wannan hadin na sanya sulbin fuska . markada tuffa sannan a matsa ruwan lemun tsami da kindirmo, sannan a kwaba. A shafa a fuska da wuya. Sai a wanke bayan mintuna 20. Wannan hadin na sanya laushi da sulbin fata da kuma dada wa fata haske.