Kwalliyar Amare
Mata da dama da zarar an sanya ranar bikinsu, mafi yawancinsu za su fara shiga da fita ne domin neman yadda za su gyara jikinsu kafin wannan babbar ranar.Ga hanya mafi sauki yadda amarya za ta gyara jikinta ,ba sai ta daga hankalinta ba •Idan gari ya waye a debo garin alkama a kwaba da […]
Mata da dama da zarar an sanya ranar bikinsu, mafi yawancinsu za su fara shiga da fita ne domin neman yadda za su gyara jikinsu kafin wannan babbar ranar.Ga hanya mafi sauki yadda amarya za ta gyara jikinta ,ba sai ta daga hankalinta ba
•Idan gari ya waye a debo garin alkama a kwaba da ruwa mai tsafta sosai sannan a shafa a fuska da wuya. Bayan ya bushe a wanke da ruwan dumi sannan sai a goge fuskar.
•Da daddare kuma a rika hada zuma da ruwan glycerin a shafa a fuska bayan ‘yan mintuna kadan sai a goge da tawul mai laushi.
•Kamar sau daya a sati, a rika kwaba zuma da amfuna sai a shafa a fuska da wuya. A jira kamar tsawon awa daya sannan a wanke da madara mai sanyi.
•Domin sanya fuska haske, a yanka gurji sai a rika shafawa a fuska.
•Idan ana son samun hannu mai laushi, a zuba rabin kofin ruwan glycerin da ruwan rose sannan sai a shafa a tafin hannu a duk lokacin da aka yi amfani da ruwa.
•Idan fatar hannu ta kasance mai yawan fashewa ce, sai a jika gishiri a ruwa a sanya hannun a ciki.
•Domin rabuwa da amosanin kai, a sami ganyen shayi a jika sai a shafa a fatar kai.
•Idan ana so a rika kamshi a kullum, a sami kwalbar turare, a zuba ganyen filawar rose a zuba ruwan glycerin sannan a rufe kwalbar kamar tsawon sati uku sannan a rika shafawa a jiki.