Kwalliyar bikin Sallah ga mata

Ga yadda za a caba kwalliya da Sallah

Kwalliyar bikin Sallah ga mata

Wata amarya yayin biki (tsohuwar ajiya)

Assalamu alaikum ’yan uwana mata. Kasancewar an fara bukukuwan Babbar Sallah ya sa na yi wannan rubutu domin taimaka wa wadanda za su caba kwalliya da Sallar.

Saboda yadda masu sana’ar kwalliyar fuska suke cika kudi, yana da kyau mata su koyi yadda za su yi kwalliya da kansu, ba tare da sun kashe ko sisi ba, kuma yadda ko da bayan Sallar za su iya yin irin wannan kwalliya domin burge mazansu a kullum.

Ya kamata fitar da za a yi a bikin Sallah ta fi ta koyaushe kyau.

Kayan kwalliyar da ake bukata:

  • Gazal launin baki da mai ruwan kasa
  • ‘Eye shadow’
  • Hoda
  • ‘Mascara’
  • Jan jambaki ( shi ne ake yayi yanzu)
  • Fandesho (foundation)
  • Hodar ‘Blush’
  • Ma’askar gira (tweezers) ka’idoji
  • Kafin a fara komai, za a wanke fuska da sabulu mara karfi.
  • A dauko ma’askar gira (tweezer) ki sa a saman girar ki yi tsari mai kyau.
  • Sai a jira fuskar ta bushe. Bayan fuskar ta bushe, sai a shafa mai kadan a fuskar musamman in fatar mai gausti ce. In ko mai laushi ce, to ba sai kin shafa mai ba.
  • A shafa hodar fandesho mai launin fata. Sannan a bar ta kamar minti uku. Sai a samu hoda mai kama da launin fatar a shafa a fuska har wuya Kwalliyar bikin Sallah da kunnuwa. Saboda kada launin fuskarki ya bambanta da na wuya.
  • A samu gazal musamman ma launin ruwan kasa (dark brown) sai a zana a girar da aka aske.
  • “Eye shadow” launin kayan da za ki sa sai a shafa kamar launi biyu a kan fatar idon.
  • Kwalli: A shafa a ido sannan maskara (mascara) launin shudi (blue) ko baki a gashin ido, ana taje shi.
  • Hodar ‘blush’: A shafa ita ma daidai da launin fatar fuska.
  • Jambaki: A shafa a lebba. Bayan an yi hakan, sai a sake samun gazal mai launin kasa a bi lebban bakin da shi. Bayan an gama wadannan abubuwa, za a ga fuskar ta canza sosai.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos