Kwalliyar gazal da maskara

Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa da ku a cikin wannan filin na kwalliya. Tare da fatan ana gwada irin abubuwan da muke kawo muku a kowane mako don samun fata mai kyau da sheki da kuma sulbi. A yau na kawo muku wani sabon salon amfani da gazal da maskara domin inganta kwalliyar fuska. […]

Kwalliyar gazal da maskara

Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa da ku a cikin wannan filin na kwalliya. Tare da fatan ana gwada irin abubuwan da muke kawo muku a kowane mako don samun fata mai kyau da sheki da kuma sulbi. A yau na kawo muku wani sabon salon amfani da gazal da maskara domin inganta kwalliyar fuska. Ga kadan daga cikin  yadda ya dace a yi amfani da maskara da gazal.

• Akwai gazal na zamani wanda yake kamar ruwa. Ana shafa irin wannan gazal ne a kan layin ido, ba a ciki ba kamar yadda Larabawa suke sanya gazal. 

• Gazal mai kama da fensir shi ne wanda za a iya sanyawa cikin ido. Kuma ana iya amfani da shi wajen cika gurbin gira.

• Za a iya samo launuka da dama wajen cika gurbin gira. Amfani da launin gazal wanda ya yi kusa da fata na matukar inganta kwalliyar mace .

• Ita maskara kuma, za a  iya sanya ta wajen taje gashin idon. Ita ma tana da launuka da dama, za a iya amfani da shudi wajen kawata fuska. Tana sanya gashin ido yin kyau kuma tana taje gashin ido. Turawa na da gashin ido kamar an sanya musu maskara. Amma za a iya sanya maskara domin kara tsayin gashin gira.

•Maskara na taimakawa wajen taje gashin gira tare da ba gashin wani irin tsari wanda daga an kalli mutum an san an caba ado da kwalliya.

•Ana iya sanya wani launi daban a kan lebba kafin a shafa jambaki domin kawata kwalliyar baki da kuma kara kyawun kwalliya.