Kwalliyar ‘mai da tsohuwa yarinya’
Mace duk tsufanta, ba ta son a ce da ita ta tsufa. Kullum tana so a rika ganinta kamar yarinya ko ’yanmata. Ko da biki za ta, sai a ga tana kokarin ta ga ta fi matasan wajen ado da takalmi ko riga da kuma kwalliya. Don haka ne, a yau, na kawo muku yadda […]
Mace duk tsufanta, ba ta son a ce da ita ta tsufa. Kullum tana so a rika ganinta kamar yarinya ko ’yanmata. Ko da biki za ta, sai a ga tana kokarin ta ga ta fi matasan wajen ado da takalmi ko riga da kuma kwalliya. Don haka ne, a yau, na kawo muku yadda za a magance irin wadannan matsalolin.
Kwalliyar ido
Babban kuskuren da mata suke yi idan sun zo yin kwalliyar idanunsu shi ne, a maimakon su sanya kwalli ko gazal kawai, sai su hada bakin kwallin a fatar saman idanu. Idan mace ta dan manyanta, bai kamata ta rika irin wannan kwalliyar ba. Sai dai ta zabi daya. Ko ta sanya gazal a ido, ta bar saman idon ko kuma ta shafa ‘eye shadow’ a fatar ido ta bar idon ba kwalli. Yin duka biyunsu na sanya ta yi kama da dododo.
Gyaran fatar fuska da jiki
Idan shekaru sun ja, lallai ne a kula da fatar jiki fiye da kwalliyar da za a yi a fuska. Sirrin yin hakan shi ne, ana son fitar mace ya zama kamar ba ta yi kwalliya ba. Don haka, ya kamata a shafa hodar fandesho daidai da kalar fatar fuska don boye tattarewar fuska da kuma tsufa. Idan akwai kuraje a fatar jiki ko fuska, za a iya amfani da man ‘concealer’ a hada da hodar fandesho don boye wadannan tabbai ko kurarrajin fata. Kada a manta, a rika amfani da kalar da ta dace da fata wajen sanya hodar fandesho.
Baki
Ba lallai ba ne a nemi kala mai haske sosai wajen sanya jan baki. Ko da ja ne, za a iya sanya jan da bai cika haske ba. Ko kuma man baki kadai ya wadatar. Idan aka gwada wadannan kwalliyar, lallai za a ga canji, tsohuwa ta zamo yarinya.
Yanayin kayayyakin shafa daban-daban: