Kwallo 4 a bana: Shin PSG ta yi asarar dauko Messi?
Zuwa yanzu dai Messi ya lashe kofuna 36 a kungiyoyi.
A wani abun mamaki, an fitar da jerin sunan gwarazan ’yan wasan Gasar Ligue 1 ta Faransa amma babu sunan Lionel Messi da Neymar.
Wadanda aka lissafa a matsayin gwarazan ’yan wasan su ne Kylian Mbappe na PSG, wanda shi ne yake kan gaba a jefa kwallaye a raga a gasar da kwallo 24; sai dan wasan Rennes, Matin Terrier; sai dan wasan Monaco, Wissam Ben Yedder; da Dmitiri Payet na Marseile; da kuma Lucas Paqueta na kungiyar Lyon.
Sai dai wannan lamari na rashin ganin Messi a jerin zaratan ’yan wasan bai zo da mamaki ba, ganin har zuwa hada wannan rahoto kwallo hudu kacal ya jefa a raga a kakar bana a wasa 23 da ya buga a Gasar Ligue 1 ta Faransa.
A watan jiya ne kungiyar PSG ta lashe Gasar Ligue 1 din ta Faransa karo na goma – sau 8 a cikin shekara 10 da suka gabata kadai.
A farkon kakar bana ne Messi ya koma PSG da taka leda inda ya sanya hannu a kwantiragin shekara biyu bayan kwashe sama da shekara 20 a kungiyar Barcelona.
A Barcelona ya lashe Gasar Laliga 10, sannan ya lashe Gwarzon Dan Wasan Gasar sau tara.
Haka kuma ya lashe Gwarzon Dan Wasan Duniya sau bakwai, inda ye kere kowa a duniya, sai Cristiano Ronaldo da ke biye masa da guda biyar.
A Gasar Zakarun Turai kuma, dan wasan ya zura kwallo biyar ne a wasa bakwai da ya buga kafin kungiyar Manchester City ta lallasa su a wasan farko na zagaye na biyu.
Messi a PSG a bana
Lionel Messi ya zura kwallo hudu ne kacal a Gasar Ligue 1, ya zura kwallo biyar a Gasar Zakarun Turai, jimilla kwallo tara ke nan.
Sai dai ya taimaka an zura kwallo 13 a kakar ta bana, sannan ya samar da damarmaki guda 58, inda ya zama dan wasa na hudu wajen samar da damarmaki a gasar, sannan na biyu wajen taimakawa a zura kwallaye.
Messi a da
A duniyar kwallon kafa, za a dade ana maganar kwarewar Messi musamman duba da zamaninsa a Barcelona.
Ya fara taka leda ne sama da shekara 20 da suka gabata a Barcelona, inda ya fara wasa a watan Oktoba na shekarar 2004 a wasan Barcelona da kungiyar Espanyol a Gasar Laliga.
A kakar ce ya fara lashe Laliga ta kakar 2004-05 karkashin kocin da ya fito da shi, Frank Rijkaard.
A shekarar 2005-06 ce ya lashe Gasar Zakarun Turai inda Barcelona ta doke Arsenal a wasan karshe.
Zuwa yanzu dai Messi ya lashe kofuna 36 a kungiyoyi.
A kungiyar Barcelona, ya buga wasa 520, inda a cikinsu ya zura kwallo 474.
Sai da ya dauki kusan shekara goma, duk kaka sai ya zura akalla kwallo 20 a kakar wasanni daya.
Me ya kawo matsalar?
Tun zuwansa a farkon kakar bana duniyar kwallo ta dauki zafi, inda aka yi tunanin kasancewar akwai Neymar da Mbappe, ga shi kuma PSG din ta dauko Sergio Ramos da sauransu, sai aka yi zaton sauran kungiyoyin duniya sun shiga uku ba ma a Faransa ba.
Sai dai tun a lokacin wasu masu nazarin wasanni sun yi hangen cewa ba Messi kungiyar ke bukata ba, kasancewar ba cin kwallo ba ne matsalarsu.
Zuwan Messi, Mbappe ya so ya daga, amma Shugaban PSG din ya ki amincewa, inda ya ce ya amince Mbappe din ya karasa lokacinsa, sannan ya tafi a kyauta.
Tunanin shugaban shi ne idan aka samu Mbappe da Messi da Neymar din, za su ci duk abin da yake bukata, musamman Gasar Zakarun Turai.
Wasu kuma musamman magoya bayan Messi din sun rika cewa ba a taba samun kwararrun ’yan wasa a kungiya daya ba a tare kamar su, don haka babu kungiyar da za ta iya doke ta cikin sauki.
Sai dai wasu sun ce an yi lokacin da Barcelona ta samu Messi da Neymar da Suarez kuma an doke su, sannan an yi zamanin Cristiano Ronaldo da Benzema da Bale amma su ma aka rika lalla su.
Amma zuwa yanzu, ana iya cewa hadakar ta Madrid da Barcelona ya fi samar da sakamako mai kyau.
Shin PSG ta yi asara?
Bakin Raga tana gani cewa a bangaren samar da kudin shiga, kungiyar PSG tana kashe €300m wajen biyan albashin ’yan wasanta, inda Messi ke kan gaba da €41m a shekara, sai Neymar da ke biye da €36.8m, sai kuma Mbappe mai daukar €25m.
Kungiyar ta kashe makudan kudaden nan ne domin lashe Gasar Zakarun Turai, duk da cewa sun yi murnar lashe Gasar Ligue 1 din, amma kuma hakan bai samu ba.
Ko a da sun lashe gasar Faransa da yawa ba tare da zaratan ’yan wasan ba, duk da cewa a kakar bara, kungiyar Lille ta yi musu ba-zata wajen lashe gasar.
Ko gobe za ta fi yau?
Ganin wannan sakamako da aka samu, da yadda Messin ya sha wahala, akwai rahotanni da ke nuna yana so ya nannade tabarmarsa ya bar PSG, inda ake tunanin kungiyar Inter Miami ta Amurka, wadda mallakar tsohon dan wasa Bekham ce da Barcelona da ke son yi masa kome.
Sai dai ana tunanin yana so ya zauna ya karasa kwantiraginsa da tunanin ko zai iya ba marada kunya a kakar badi.