Kwallon Kwando: Kobe Bryant ya yi murabus

Shahararren dan kwallon Kwando na Amurka na kungiyar LA Lakers, Kobe Bryant ya yi murabus bayan ya kwashe shekaru ashirin yana bajinta. A wasansa na karshe ya ci kwallaye 60 a kan kungiyar kwallon Kwando ta Utah Jazz inda aka tashi 101-96. Ya fara wasan kwarraru ne yana da shekaru 17 a shekarar 1996. Ya zama […]

Kwallon Kwando: Kobe Bryant ya yi murabus
Kwallon Kwando: Kobe Bryant ya yi murabus

Shahararren dan kwallon Kwando na Amurka na kungiyar LA Lakers, Kobe Bryant ya yi murabus bayan ya kwashe shekaru ashirin yana bajinta. A wasansa na karshe ya ci kwallaye 60 a kan kungiyar kwallon Kwando ta Utah Jazz inda aka tashi 101-96.
 Ya fara wasan kwarraru ne yana da shekaru 17 a shekarar 1996. Ya zama dan wasa mafi shahara watau MbP a tsakanin shekarar 2007 zuwa 2008. Sannan dan wasan ne ya jagoranci kungiyarsa wajen lashe kofuna a gasar kwallon kwando a shekarun 2000 da 2001 da 2002 da 2009 da kuma a 2010.  Sannan yana cikin wadanda suka lashe wa Amurka lambobin zinare a gasar Olamfik da ta gudana a shekarar 2008 da kuma 2012.
 An sayar da tikitin wasansa na karshe ne a kan Dala dubu 27 da500 wanda ya yi daidai da Naira dubu 800  maimakon Dala dubu 1 ko Dala dubu 2 da aka saba sayarwa.
 Kobe Braynt a jawabinsa na ban kwana ya ce: “Na gode wa jama’a da abokaina da takwarorina da iyalaina kan goyon bayan da suka ba ni”.
 Tsohon kyaftin din kungiyar kwallon kwando ta Najeriya Mista Scambo Morrison ya ce “Ya yaba masa matuka don ya cimma burinsa a wasan kwallon kwando.  Sannan ya yaba da murabus din da ya yi don ya ba na baya dama su ma su nuna tasu bajintar a wasan kwallon kwando.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa