Kwamadan ’yan sintiri ya hallaka a tagwayen hare-haren Boko Haram

Wasu tagwayen hare-haren kunar bakin wake da aka kai a garin Potiskum da ke Jihar Yobe sun yi sanadiyyar hallaka rayukan mutum takwasa ciki har da ’yan kunar bakin waken biyu da kuma wani kwamandan ’yan sintiri. Tagwayen hare-haren dai wasu matasa biyu ne suka kai su a wurare daban-daban, kamar yadda wani ganau da […]

Kwamadan ’yan sintiri ya hallaka a tagwayen hare-haren Boko Haram
Kwamadan ’yan sintiri ya hallaka a tagwayen hare-haren Boko Haram

Wasu tagwayen hare-haren kunar bakin wake da aka kai a garin Potiskum da ke Jihar Yobe sun yi sanadiyyar hallaka rayukan mutum takwasa ciki har da ’yan kunar bakin waken biyu da kuma wani kwamandan ’yan sintiri.

Tagwayen hare-haren dai wasu matasa biyu ne suka kai su a wurare daban-daban, kamar yadda wani ganau da ya nemi a boye sunansa ya shaida wa Aminiya.
Ya ce dan kunar bakin wake na farko ya yi yunkurin shiga cikin wani taron matasa ne
a Unguwar dorawar Mashaya da misalin karfe 1:30 na rana sai mutane suka gano kudirinsa, sai wani matashi ya ruga ya rungume shi, bam din da ke jikinsa ya tashi da su.
Ya kara da cewa fashewar bam ke da wuya sai suka sake jin fashewar wani bam din a Arewa da su, inda suka garzaya suka ga wani dan kunar bakin wake ne ya tada bam a ofishin ’yan banga da ke gab da gidan mai na Rimi a hanyar Nangere.
Ya ce a wannan harin bam ne dan kunar bakin waken ya hallaka Kwamandan kungiyar ’Yan sintiri mai suna Ado Kwamanda da wasu mambobinsa hudu da wata yarinya mai sayar da abinci da shi kansa dan kunar bakin waken.
Duk kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Mista Toyin ya ci tura, amma wata majiya ta ce jami’an kungiyar agaji ta Red Cross sun kwashe wadanda suka mutu da masu rauni zuwa asibiti.
A wani labarin wasu ’yan bindiga da ake zargin’yan Boko Haram ne sun kai hari a garin Babbangida hedikwatar karamar Hukumar Tarmuwa da ke Jihar Yobe, inda da dama daga cikin maharan suka rasa rayukansu a gumurzun da suka yi da jami’an tsaro na JTF da ’yan sintiri, inda wasu ’yan banga biyu suka mutu a gumurzun.
Wani mazaunin garin Malam Abdullahi Tarmuwa ya shaida wa Aminiya cewa, tunda La’asar a ranar Asabar suka ji ’yan Boko Haram sun fafata da jami’an tsaro a kauyen Sasawa da ke gabas da Babbangida, kuma inda a safiyar Lahadi kuma suka fara jin kararrakin bindigogi da karar fashewar abubuwa daga gabas da garin.
Wani dan banga da ke cikin jami’an tsaron da suka yi artabu da ’yan bindigar ya ce lokacin da suka samu rahoton harin sun garzaya wurin, amma kafin su isa sun yi barnarsu sun gudu shi ne suka bi su suka cimma wasu a kauyen Kariyari suka fafata suka kashe da damansu, inda su ma suka rasa mutum biyu.
Ya ce ’yan bindigar sun je ne cikin motoci kirar Toyota Hilud 13 da babura masu yawa, kuma suna zuwa suka wuce gidajen burodi suka kwashe, kuma suka fasa shaguna suka kwashi kayan abinci sannan suka kone ofishin Babban Jami’in ’Yan sandan yankin da wani bbangare na fadar Mai Jajere da wasu shaguna.
Shugaban karamar hukumar Alhaji Isma’ila Mai Adamu ya tabbatar da hakan ya ce amma al’amura sun fara dawowa kamar yadda suke a garin.